← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 47

Sashe 21

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda garin Allah ya waye Ammah ke faman neman number zahra abin yaci tura, a yau dai hakurinta ya Gaza Dan tun Daren jiya da zilai ta Kira Ammah tana fada Mata yanda fasalin gidan da suke yake da kuma kudin da tace an Basu dubu ashirin da safe da yamma ma an kawo musu wasu kudin dubu dari-dari ita da iya Rahane ga turamen atamfofi guda hudu hudu da lace bibiyu, Kuma ta fada Mata tunda su zahrar suka fice Bata Kara ganin giccinsu ba ga wayar ta ma a rufe.
Akalar Kiran Ammah ta canza ta shiga lalubo Number Abdul Hakeem.
Ringing din farko ya dauka yana Fadi "barka da Asuba Ammah, an tashi lfy?.
"Alhamdulillahi, idan ka tashi ka shigo Ina son ganinka" ta fada cikin damuwa.
"To in Sha Allah, gani nan shigowa"..
Ta kashe wayar, ta ajiye a gefe tana fadin "kazo ka nemomin wannan yaron ya fada min waye shi Ina Kuma ya Kai min 'yata ko waya ya Hana muyi da ita inji meye dalilni Daya hana ta amfani da wayar, tunda Naga Abban ba wani Abu zeyi ba, ga wannan kinibabbiyar matar tasa da koma sai taji Masa kwakwaf".
Tsaki tayi tana Jin duk Zuciyar ta ba dadi ko kadan, tana Nan zaune Abdul Hakeem din ya shigo sanye da jallabiya coffee colour a jikinsa ya gaishe da Ammah ya nemi guri ya zauna Yana fadin "lafiya kuwa Ammah?".
"Da sauki, Nemo min mijin Zahra a wayarka naji dalilinsa na yanke ma'amalarta Dani tunda suka bar garin Nan ban Kara Jin duriyarta ba".
Shiru Abdul Hakeem din yayi kafin yace "ba haka za'ayi ba, Zan kirasa na saka handsfree sai kiji yanda zamuyi dashi idan munji da alamun rashin gaskiya sai a San abunda ya Kamata tunda ba'asan dalilinsa. Ba na hanata amfani da wayar, ke uwace kiyi hakuri babu abinda ze Samar Miki 'ya da izinin Allah, in Sha Allah sai kinyi alfahari da Auren Nan Muhmud mutumin kirki ne bashi da wata alama ta rashin gaskiya, kinsan ya fada min shi Dan Sokoto ne,.har unguwar su da iyayensa duk ya fada min lokacin da zeyi tafiyar nan, yace saboda halin Rai Koda be dawo ba na nemi Sameer ko sabon mai gadin Daya kawo a can gidansu na hayin banki, ko Binya na gidan Baba malam duk mutanensa ne. Bari na kirasa Dan hankalinki ya kwanta".
Ya Fara dialing din number sa.
Sun Gama break fast din kenan wayarsa ta dauki slow music daga kitchen inda ya barota tsam ya tashi ya nufi kitchen din kafin yaje Kiran ya yanke, sunan Abdul Hakeem ya gani, kafin ya Kira wani Kiran ya shigo.
Saida ya zauna daf da ita ya daga kiran.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu babban yayan mu, barka da Asuba".
Ya fada Yana murmushi.
"Wa'alaika Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu barkamu kadai, ya iyalin?" Dariya abin ya bashi "Gasu Nan muna ta basu hakuri kasan Mata sai a hankali".
Ya fada Yana Dan Jan tsunin hancinta, Batasan dawa yake wayar ba.
"Wai meya samu wayarta ne Bata shiga kwata-kwata duk hankakii Ammah fa ya tashi, Jin kwana biyu shiru ba suyi magana ba idan tana kusa ka Bata suyi magana Dan hankalinta ya kwanta".
"Ya salam Dan Allah ka bawa Amman mu hakuri laifi tayi min na karbe wayar, amma Zan Bata ita yau in Sha Allah, ai Zan shigo garin gobe ko jibi".
Tunda ta fashinci da Ya Abdul Hakeem yake wayar taji hankalinta gaba Daya yayi gida Jin cewa zeje Azaren bada ita ba sai taji duk ta shiga tashin hankali da gaske gida take son komawa, ta dauka da Wasa yake Mata lokacin da yace ze dauko Mata Rukayya idan zasuje Azare.
Wayar ya Mika Mata ya Mike ya fice daga parlourn gaba Daya.
Sallama tayiwa ya Abdul Hakeem din sannan ta gaishe shi.
Sannan ya dora da fadin "ga Ammah nason magana dake".
"Dan Allah Ya Abdul Hakeem ka Bata hakuri wallahi saboda bansan abinda Zan fada Mata ba na kashe wayar Allah ba yaji nayi ba, kaina ne yayi zafi gurin fa buduwarsa ta turoni Asibiti ita Kuma ta shiga wulakantani, Dan Allah ka rokarmin shi ya maidoni gida wallahi na gaji Ni tsoro nakeji bakaga irin gidajen da yake kawoni ba kamar baza'a mutu ba fa". Ta ida fada tana kuka.
Duk abunda ke wakana Ammah na zaune tayi tagumi tana Jin wani sanyi da tausayinta a Zuciyar ta, amman koba komai ta samu nutsuwa taji lafiyar ta sauran Kuma tasan shegantake ce kawai.
Wayar Abdul Hakeem ya mikawa Ammah ya tashi ya fice shima gara ya Basu guri su tattauna.
"Wai kukan Kuma na menene haka? ai kowa ya gyara ya sani kowa ya Bata ya sani, kiji tsoron Allah ki rike sirrin mijinki kinsan baqi kinsan fari keba karamar yarinya bace,saboda me Zaki tafi wani guri har ki nemi kwana bada izinin mijinki ba, haka kawai kin tashi hankakin jama'ar da suka daukeki da mutumci kin kyauta kenan? To wallahi kada na sake Jin wani Abu makamancin haka daga gareki ki nutsu ki rike aurenki kada na Kara Jin kin ambaci ya dawo dake nan, kinsan dai ba'a nan zaku dawwama ba ina cewa ya fada Miki garinsu wata Rana dole ze koma gida sai kice bazaki bishi ba? Akul na karajin magana makamanciyar wannan daga bakinki".
Tunda Ammah ta Fara magana Zahra ke shashsheka a hankali.
"Kiyi hakuri wallahi na daina bazan Kara ba, wallahi bansan laifin da nayi Masa ba ya dauke min wayar da passport dina har da kudi da ATM duka".
Salati Ammah ta dauka tana fadin "Ni Asma'u yanzu harda passport dinki Kika dauka dole ya kwashe wato guduwa kuka shirya zakiyi kibar kasar ko?"
Cikin gigita Zahra ta fashe Mata da kuka sosai tana Fadi "wallahi ba guduwa zanyi ba Daman suna cikin jakar fa".
Ji tayi an zare wayar daga hannunta Batasan lokacin daya taso ta shige jikinsa ba tana fadin "Dan Allah ka fadawa Ammah abinda take zargina dashi ba haka bane".
Ai Jin wannan furucin na Zahra yasa Ammah yanke Kiran cikin gaggawa.
Jin alamun yanke Kiran yasa shi Kara sakata a jikinsa baya son kukanta ko misqalazarratin.
[2/7, 11:32 PM] +234 906 821 6318: 💞
* AUREN HUCE HAUSHI *

Maman Fateemah

Page 63.

............ cikin sa'a zahra ta Sami magajin a wayar, tsokanar ta ya fara.
"Dan Allah ka tsaya ka isheni da magana, kanaji Wai sahura ce zata tambaye ka Ina na koma kada ka fada Mata kace Mata bana garin kawai".

"An Gama yallabiya, kinsan bazata Fara ma tunkarata da wannan maganar ba, ba sakar Mata fuska nakeyi ba tunda na gane ita munafuka ce"
Tsaki zahra tayi.
"Can ta matse musu duk munafurcin mutum sai dai ya koma Kansa babu abinda ze sameni sai abinda Allah ya hukunta min, Wai sako to sakon me? har wani abun arziki Mama zata taso mutum ya kawo min wadda ko kallon arziki baya hadani da ita saboda tsabar kin jinina da tayi".
"Share kawai bakin ciki ne taga Allah yayi halitta a Nan take hasaada saboda nata 'ya'yan Kamar ka yanka ka boye wukar, Ni bansan wace kaddara ta Kai Abba Aurenta ba, duk matan jihar Nan Saida ya tsallake ya dauko ta Dan ma Allah yasa Basu da yawa da ansha kwantai".
Ya fada Yana wata dariyar rainin wayo.
Zahra ce ta katse shi tana fadin.
"Amma wallahi baka da kirki magaji 'yan uwanka nefa kake fada musu haka".
"Kema dai ai kinsan gaskiya na fada duba fa ki gani, kawai dai abar kaza cikin gashinta".
"Allah ya shiryeka wataran sai ka fada a gabanta, ta sauke maka ajja".
Tana Gama fada Masa ta yanke Kiran tasan sai su Kai minti goma shi ba gajiya zeyi ba.

Zahra Bata koma gurin Aunty zilan ba a Nan daki ta zauna, karatun Qur'an tayi sosai Dan Saida tayi surori da yawa, sannan ta shafa Addu'a ta tashi.

*
Sahura ce ta shiga dakin Mama Jiki ba kwari, ganin ta shigo yasa Mama tashi zaune tana fadin.
"Meya faru Kika dawo? na dauka yanzu kinje can din?"

"Eh naje Amma gidan babu alamun da mutane a cikinsa gaskiya. Dan idan ba idona ne bega dai dai ba babu wata alama data nuna giccin mutane ma a nan kusa a cikinsa, sai na Kirawo zilai nace ta fada min suna Ina ne, sai cewa tayi Wai ita Bata San sunan unguwar da suke ba tunda ba fitowa tayi ba tunda ta shiga gidan, Dan tsabar munafurci".
Ta fada tana aje kunshin kayan da za'a Kaiwa zahra.
Wata shariya Mama ta lafta tana fadin.
"Har yaushe raini irin wannan ya shiga tsakanina da zilai? Har ta Isa ta nuna min wuyanta ya Isa yanka, wallahi idan tayi Wasa saina yi mata sanadin barin aikin kwata-kwata, ai dama matsiyaci be iya cin arziki ba".
Hakuri sahurar ta ringa ringa bawa Mama ganin Nan da Nan ta ture sai masifa takeyi bakinta har kumfa yake fitarwa saboda bala'in da take kwasa .
Ita dai sahura sai abin ya daure Mata Kai, to menene najin zafi haka, dan zanyi maka Alkhairi anje ba'a sameka ba, ba sai nabar abuna ba ko na bawa wani tunda Inda nayi niyya ba rabonsu bane.

Cikin bacin Rai tace kije ko magaji ne ya rakaki Mana Zaki zo kiyi tsaye Kamar baki da wayo da dabara Dan Allah wuce a gurin".
Kayan ta dauka ta nufi kofa tana fadin.
"Bari naje na gani ko Yana nan din".
Ta wuce ta fita.
Zugum Mama tayi tana nazarin yanda abubuwa suketa lalace Mata, Wai yarinyar Nan me take takama da shine? duk abinda za'ayi da sunanta sai ya lalace,ko da tsiya-tsiya yau sai sakon Nan ya shiga gidanta duk Inda ta koma ma saina lalubo shi Dan wallahi bazanga bakin cikin da ze hanani barci ba.
Chapter 21 · 0% Book details