← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 47

Sashe 46

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

...........
Maganar data sauka a kunnen Ammah kenan, wani kallo Ammar ta yiwa Abdul Hakeem na ina tunaninka yake da lissafinka yake.
"Me naji kana fada tayi bako Kuma kamar yaya?".
Dawo yayi daga fitar da yayi niyya.
"Ammah bafa wani bane da ban Sameer ne abokin mijinta Ina ganin sako ne ze Bata fa, ya za'ayi nazo kiranta idan bansan waye ba tubda da aurenta shima ganin na hannun Daman mijinta ne Kuma ga bayanin da Kika yi min nasan da abinda ya kawo shi girinta".
"Ah to yanzu naji magana, turo min magaji ya bude Masa falon baki.
"Haba basai na turosa ba bani kawai na bude masa".
Gurin dinning Ammah ta nufa ta dauko Masa keys din ta bashi ya fice, Alawiyya Ammah tasa ta Zuba abinci da drinks ta Kai Masa.
Sai da Zahrar ta bashi a kalla minti talatin tasa dai zuwa lokacin ya Gama komai sannan ta leqa ta fadawa Ammah zataje gurinsa.
Lokacin da tayi sallama ta shiga Sameer Yana tsaye da waya a kunne Yana fadin.
"Dan Allah ka koyi hakuri Mana haba kamar a kanka aka Fara Aure duk ka tashi hankalina nace maka Ina Cikin gidan abincin tarba aka kawo min kafin ita madam din ta fito.....yauwa gata Nan ta fito".
Ya fada Yana mikowa Zahra wayar wadda ke fadin.
"Barka da sauka oga Sameer".
"Yauwa sannu amarya, ungo mijinki ya hanani sakat Saida ya tasoni daga aikin daya sakani a garin nan Wai nazo na gani da abinda yake damunki".
Dan murmusawa tayi.
"Ni lafiya ta kalau kawai dai baya son ka huta ne, Ina baby na?".
"Baby sun dauki hanyar sokoto acan zaku hadu, harda su Rukayya da mommy da mutuniyar ki ai Rukayya na fada Mata tayi tsallen albarka tace tafiya ta tashi".
Ya fada yana nufar kofa.
Wayar ta duba Yana Kan layin Yana jinsu.
"Karawa tayi a kunne tana fadin.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
A zuciyarsa ya amsa sallamar Amma a zahiri sai yace Mata
"Haba precious kunyi min adalci kenan? me yasa Zaki yarda a maida Mana hannun agogo baya, Wai Dan kada mutane suyi surutu sai a dauke min ke? Nifa nayi zaton koma menene a iya sokoto Nan ze tsayaKema na kiraki Dan na samu relief sai kik'i daga wayar sai ace min wai kuka kikeyi wato so kike na nuna musu raunina a kanki ko?
Shiru tayi ita ta rasa mema zata ce Masa Umarnin mahaifiyarsa zata tsallake, da kunnanta fa taji Yana fadar Ammi ze bawa zabi ta zabar Masa Mata, to Kuma tace ta tashi tabi yan uwanta su tafi to musu zatayi Mata tace bazata ba ko Yaya?shi me yasa ya Bata zabin tayi abinda ya dace, ita Bata kullace shi ba sai ita zega laifin ta taho wato shi yayi biyayya ita kuma ta nuna ba haka ba ace kwadayin dukiyar su take yi kenan,duk da itama a Cikin wadatar ta tashi gaba da baya Amma ai ba kowa ne ya san hakan ba.
"Kinyi shiru precious".
"Me kake son na fada bayan biyayya na yiwa Ammi cewa fa tayi na tashi mu tafi kawai lokacin banma San inda zamu ba Saida mukazo Kano Naga mun dauki hanyar Azare na gane Ina zamu,ai Ina ganin kawai mu hakura mu yiwa Iyayen mu biyayya kaga Nima biyayyar nayi lokacin da aka bani Kai bansan Koda waye aka daura min aure ba,Amma na hakura nayi biyyyar iyaye kaima kayi biyyyar idan Ammi bani bace zabinta muyi hakuri haka Allah ya nufa zaman takaitaccene kabi abinda takeso bazaka tabe ba in Sha Allah".
Cikin tashin hankali ya Fara magana.
"Me kike fada haka preciousss? Kina son heart attack ya sameni? Waya fada Miki Ammi Bata Sonki? Soyayyar tasa ta raboki da gidanta badan Bata sonki ba Kinga yanda ta kasa zaune ta kasa tsaye duk fa kunyar Dan fari Ammi ta aje a gefe hidimarta takeyi babu Kama hannun yaro, Ina gama da sakon data bawa Sameer ya kawo Miki, na Ammah Ina Jin sai gobe za'a taho dashi, ki shirya dake za'a taho min fa a Mika min kayana daga cikin daki Nima naji abinda 'yan uwan sukeji na gaji da gararamba gara na tsuguna Nima na Fara hada nawa family din, in sha Allah da biyu Zaki Fara min ko 'yar gidana".
Runtse idanu tayi ita fa idan yana ambatar irin wadannan kalaman na haihuwa tuno yanda sabgar take kafin samun abun haihuwar shine damuwar ta da gasken gaske tana hasaso ranar da alama Kuma an dauki hanyar zuwanta.
"Dan Allah ya mahmud ka Bari ba kyau fa irin wannan maganar"
"Kam bala'in waye yayan naki Allah ki iya bakinki babu hadin Zuma da guna,ki nemi yayanki tun dare be Miki ba,Ni ki barni a your love dinki kawai ko kin manta meu amor dinki ne...? Pls Dan fada min irin tanadin da aka yiwa meu amor a wannan special day din?".
"Wayyo.... Dan Allah ka rufa min asiri.. ni wallahi wannan zancen yafi karfina pls Kan bariiii..?
Ta fada da sigar data yamutsa Masa jam'iyya nan da nan ya nemi nutsuwarsa ya rasa.
"Ya salam! Previousss Anya Zan iya hakurin kwana uku nan gaskiya tahowa zanyi na daukeki mu wuce Dubai inda a tanadar Miki Dan amarcinki alkawarin nayi azumi uku kawai bazan iya ba"
Ya fada Yana Mata wani irin numfashi a kunne, da sauri ta cire wayar daga kunnenta tana fadin "nashiga Tara me kuma nayi Masa?
Da sauri ta mayar da wayar tana Masa magiyar ya rufa Mata asiri kada ya jawowa mahaifiyarsa abun fada Cikin kishiyoyi.
Ba Karamin Kai ruwa Rana akayi ba kafin ya hakura, da gaske tuburewa yayi shi baya son bidi'a ansan tun yaushe suke tare da za'a wani tarki bikin babu gaira babu dalili, tana samu ya Dan sauka tayi Masa sallama tace Ammah tana kiranta anyi Baki,yasan neman guduwa takeyi kawai Bai barta ba saida ya jaddada Mata ze Kira da dare.
Lokacin data fito Sameer baya kusa tasan suna tare da ya Abdul Hakeem part dinsu ta nufa Ya imam ta gani ta tambaye shi ko su Ya Abdul Hakeem suna nan? Tabbacin hakan ya Bata Kira shi a wayar ta tace tana jiran oga Sameer.
Ba jimawa suka fito ya Mika Masa wayarsa, tana fadin .
"Gashi nagode".
Karba yayi yana fadin..
"Bari na dauko Miki sakon Ammi Wanda ta bayar a kawo Miki"..
Wata Leda Yar madaidaiciya ya Miko Mata Yana fadin.
"Gashi Aunty Aishat tace zakuyi waya".
"Ok Nagode, bazaka shiga ku gaisa da Ammah ba?"
Yar dariya yayi.
"Na nawa kuma? Na shiga mun gaisa".
Dan murmushi tayi ta nufi Cikin gida.
Ba zato tayi arba da Aunty Hasana da gudu ta shige jikinta tana fadin.
"Aunty kin manta Dani wallahi, laifin me nayi Dan Allah".
"Kuji mun yarinya ! Sai Kuma nayi ta kiranki a waya har mijinki ya Raina ni ya daina Jin 'yar kunyar tawa da yakeji ai yawan damun kani ko d'a da Kira a waya bini-bini Yana kawo raini da rashin ganin kima a tsakani gara a ringa daukar lokaci yanda duk lokacin daka Kira ya Zama ana marmarinka ku rabu ana kewarka da Jin ba'a gaji da Hira da Kai ba".
"Wannan maganar taki bisa hanya take, haka ake son Babba yaja girmansa".
Hajiya kaltume ta fada.
"Ah to Mamma fada Mata dai so take girma ya Fadi a gurin kanin nawa yanzu kuwa Aunty sama Aunty kasa duk bayan kwana biyu saiya kirani ya gaisheni".
"Aunty Ina zuwa".
Zahra ta fad'a tana nufar bedroom din data yiwa kanta masauki, Bata Jima ba ta fito da abinda Ammi ta Bata ta mikawa Aunty Hasana tana fadin.
"Gasu Nan na manta dasu Ammi ce ta bani jiya da zamu taho".
Bata zauna ba daki ta jiya tana rike da hannun Autar Aunty.
Aunty Hasana ce ta cire rapping sheet din na madaidaicin, white gold din ne yayi musu maraba, da sauri Hajiya kaltume ta matso tana fadin.
"Masha Allah girma sai Dan girma wani kayan sai amale wane jaki,lallai babban goro sai magogin karfe, irin wannan kyautar girma haka, 'yan biting bude sauran muga abinda ke ciki".
Wata ubansun Alkyabba ce baka da ratsin zare golden sai turarika masu azabar kamshi a ciki.
Jim maganar Hajiya kaltume yasa Ammah fitowa daga daki taga menene ake dagawa murya haka?
Sarkar Hajiyar ta mikawa Ammah.
"Duba kiga Karamar arziki irin wannan daga uwar mahmud, Ashe dasu tazo gidan ta aje ta shiga tata sabgar, inga fa sarkar Nan ta tasamma wajen fifty millions wallahi Dan kwanaki mun siyar da wata Bata Kai wannan ba wurin forty seven milion aka sayar".
Ammah rasa abin fada tayi saboda abin ya Bata mamaki to su wane irin dukiya garesu mutanen nan?.
Nan suka zauna suna ta maida yanda akayi har kusan la'asar duk abinda ya kamata sunyi yi an bada aikin kayan garar da za'a Kaiwa Zahra Dana Iyayen mijin duk wata al'ada da ake a sokoton Ammah ta tambaya an fada mata, da yammaci suna zaune Abba ya shigo Yana fadin.
"Asma'u ku tanadi abun tarbar Baki gobe in sha Allah bakin sokoto na Nan tafe yanzu ba dadewa Kanin Alhaji Muhammad ya kirani yake fada min zasuzo naso na hanasu duba da nisan dake tsakanin Bauchi da sokoto Amma ya nuna min a'a idan ma yafi haka zasuzo godiya ce zasu zo tunda ba aure za'a sake daurawa ba inaga ko maza ne ko kuma Mata da maza ne ban sani ba dai sai ayi dai abinda ya kamata nace Abdul Hakeem suje da magaji a debo zabi sai a Kara Dana gidan idan yaso sai a kawo sabo Naman na gida.
"To Allah ya kaimu, ya Kuma maganar furniture's din da za'a tafi dasu daga nan?".
Sai goben insha Allah za'a had a da kayan da kikace za'a kawo daga Bauchi Sai a tafi dasu gaba daya ai inaga hakan yayi ko?"
Chapter 46 · 0% Book details