Sashe 17
Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
______ Duk budirin da take Yana jinta tana ta faman jijjiga shi Sai da yaga da gaske hankalinta ya tashi sannan ya dago kansa Yana kallonta da hargitsatstsun idanunsa, wata ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta kauda idanunta da gasken gaske wani irin nauyinsa takeji, matsowa jikijnta yayi a hankali ya sakata a jikinsa Yana fitar da numfashi a jikin wuyanta, wata irin kasala ta kara saukar mata gashi ba halin kwacewa ya kanainayeta ta ko ina.
Cikin kunnenta yayi maganar da wani yanayi Mai wuyar fassarawa. "bani maganin na Sha".
Da sauri ta Mika masa 'yar kwalbar, jikinta ta janye da sauri ta dauko robar ruwan data Dan gangara wurin karshen gadon.
Kwara biyu ya Ciro maganin ya karbi ruwan ya watsa maganin a bakinsa yabi da ruwan, Saida ya shanye shi tas sannan ta karbi robar.
Zanewa yayi ya kwanta rigingine, hannunsa Yana dafe da goshinsa Dan ji yayi kansa Yana wani irin Sara masa, ganin haka yasa zahra janyo blanket din ta rufe jikinta dan itama har lokacin jikinta Dan karkarwa yake mata daga ciki.
Sun jima a haka kowa da abinda yake sakawa a tasa Zuciyar, Amma ita zahra Hamdala take ga Allah Daya tarfawa garinta nono, tab da yanzu ba wannan batun akeyi ba, tsikar jikinta ce ta tashi sharrrrrr.. jikinta ta kankame guri Daya tana ayyana wani Abu a cikin ranta, Jin motsin tashinsa tayi, dan waiwaya inda yake kwance tayi taga ya tashi ya nufi toilet Yana hada hanya.
Har ranta taji tausayinsa sai dai tafi tausayin kanta a kan halin da yake ciki.
Ya jima tsakiyar ruwan sanyi Yana dukan jikinsa,sai ajiyar Zuciya yake saki ba kakkautawa tamkar yaron Daya wuni kuka baiga uwarsa ba, Saida ya samu nutsuwa sosai sannan yayi wanka ya fito har lokacin tana kudundune a cikin blanket din.
*
Har gate din gidan Mai adaidaita sahun ya kawo Faruq yana fadin "Yallabai kayi muhalli Mai kyau Allah ya kawo abokiyar Zama ta gari Masha Allah".
Shi dai Faruq hankalinsa in yayi dubu to Yana Kan ya shiga yayi arba da Ya Mahmud dinsa badan yaso ba ya taho ya barosa, yaso kafarsa kafarsa su taho dan gani yake kamar guduwa zeyi ya rasa inda ya shiga, kudin da baisan adadinsu ba ya Ciro ya mikawa Mai Dan sahun yayi gaba. Yana Jin Mai Dan sahun na fadin " Yallabai kudin fa sunyi yawa ka duba kuwa?"
Bai waiwayo ba ya dago masa hannu Yana fadin "kaje ka Kara petrol da sauran". Yayi gaba abinsa, yana jiyo yanda yake kwararo Masa addu'a kamar ba gobe, da yake irin mutanen Nan ne masu kaifin harshe kamar jikan maroki.
Sau biyu Faruq yayi knocking din gate din,malam Musa ya leko ta kofofin dake jikin gate din, ganin shine yasa da sauri ya bude Faruq din ya shigo, sun yiwa juna farin sani tunda sun Sha zuwa da Mahmud suna kwana idan wani Abu ya kawo su kanon, sauda yawa anan gurin malam musan yake zama idan baya son fita ko Ina.
Cikin mutunta juna suka gaisa malam Musan yake fadar "Ashe tare kuke da yallaban Amma kunyi shigowar dare gaskiya, kaga motar can ma a kunne ya barta Naga kamar Matar tasa Bata Jin Dadi, dan da sauri suka wuce ciki ko motar Bai samu damar rufewa ba, nayi mamaki da naga yau yallabai da kansa ma yake tukin motar".
'yar dariya Faruq yayi, Bai tofa ko kalma Daya ba akan maganar tasa da yayi akan Ya Mahmud din, gurin da motar take Ya nufa Yana fadin.
"Ina zuwa Baba Musa Bari na gyara parking din".
Zuciyarsa fari tasss, Daya samu Mahmud a gidan ba kafa ya bashi ya gujewa haduwarsu ba kamar yanda ya yanke hulda da kowa, bai San Yana da irin wanna Zuciyar ba Saida aka samu matsalar, Amma Abu mafi daure Kai yanda Baba Musa yasan matarsa ce har yake fada Masa, ko a Ina ya samu labarin dasu Family dinsa Basu sani ba?.
Saida ya Kai motar parking lot sannan ya dawo gurin Baba Musa ya zauna suka Fara Hira, tunda mutuminsa ne sosai, sai da sukayi nisa a hirar sannan Faruq ya tambayi Baba Musan ko da sabuwar lambar Ya Mahmud a gurinsa shi ya baro wayarsa Mai sabuwar lambar a gida, tunda ya fada Masa ba tafiyar su Daya ba, shi biki yazo garin, shine ya shigo tunda ya fada masa Yana garin.
Ba musu ya Miko masa wayar yana fad'in.
"Duba ka gani Nima jiya jiya nan ya kirani da ita yake fada min za'a kawo kayan gyaran wancen sabon ginin da aka Gama".
Ya fada Yana nuna Masa inda su Mahmud din suka shiga.
Number ya saka a wayarsa ya maida Masa wayar Yana fadin "dauko min keys din wancan part din na shiga na kwanta na gaji sosai".
Dakinsa ya shiga ya fito Yana fadin gasu ka duba niba banbancewa nakeyi ba. Amsa yayi yayi masa sallama ya nufi part din Zuciyar sa fal da tambayoyin Daya Kamata ace ya yiwa Baba Musan Amma gudun bada wata kofa da za'a Sami wata kofar sanin wani abun yasa yaja bakinsa yayi shiru.
Har Mahmud ya shirya cikin pyjamas dinsa sky blue tana kudundune a cikin blanket din, duk Kai kawon da yake tana jinsa amma ko motsin kirki batayi ba, sai ya Gama komai ya nufi kofar ficewa daga dakin ya juyo kadan Yana Kare Mata kallo da gaske ita ce rauninsa yaga alama, a hankali ya koma cikin dakin yaje har inda tayi wurgi da hand bag dinta ya tsuguna ya dauka ya koma gefen gadon ya zauna ya bude jakar, wayarta ce da sauran tarkace irin na Mata sai ATM cards dinta da 'yar robar maganinta a ciki na wajen Hajiyar makwarari, ATM'S din ya dauke da wayar da sauran kudin data Ciro jiya a Hanyar Janbulo, harya mayar da jakar ya ajiye sai kuma yayi saurin Kara daukota kamar Wanda aka tsikara ya Kara budeta cikin wani zip na gefe ya bude takardu ya gani ya cirosu duka passport dinta ya gani da wasu magungunan da aka Bata na Asibiti sai takardun tests da akayi Mata na Azare Dana Nan kanon.
Passport din ya dauke ya hade da abubuwan daya dauka ya Mike ya fice daga dakin yana saka Mata alamar tambayoyi masu yawa.
Saida taji ya fice daga dakin da kusan minti goma sannan ta samu zarafin tashi zaune tana Dan turo Baki tana 'yan matanganunta a ciki Wanda ita kadai tasan me take fada.
Sai lokacin ta shiga bin jikinta da kallo ita fa duk ya dagula Mata Lissafi. Banda taimakon Allah da yanzu ba wannan batun akeyi ba, tsikar jikinta ce ta kara tashi yarrrr kankame jikinta tayi tana sauki wani malalacin numfashi, tare da furta "Narrow escape".
Ta Kai dubanta inda yayi Mata wurgi da kayan jikinta, ita har zuwa lokacin ta rasa meya tunzura shi haka daga ganin Musbahu ita ba ita takai kanta ba, ba ita tace ajeba ballentana yayi tunanin setup ne.
Itama wankan ta shiga yi tana zuwa ta duba jikinta cikin ikon Allah period din ya dauke Daman tun safe taga alamun hakan duk pad din data saka a yinin haka nan take cirewa, ta yanzu ma hakan ce ta kasance, tayi hamdala ga Allah tafi a qirga wato ba karamar kariya wannan pad din ta Bata ba.
Wankan tsarki tayi tare da wankan sabulu ta fito daure da towel, yanzu ta Zama 'yar gari gurin suturar sakawa, gurin kawai ta nufa ta Ciro Riga da wando sleeping dress masu rawa ta saka ta dauko hijabi ta shimfida sallaya ta tayar da sallar magariba da insha'i.