← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 47

Sashe 20

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ledojin ta shiga dubawa taga Dame Dame Nene a ciki, Wanda su Fateeha da mommy ta Bata ta cire ta aje a gefe sai Kuma Wanda ya sawo jiya ta cire na kitchen, kofar data gani a tufe taje tadan tura ga mamakinta a bude ta ganta shiga tayi kitchen ne modern sosai babu abinda babu a cikinsa tsayawa tayi tana nazarinsa kafin ta juya ta koma dauko Kayan.
Saida ta aje komai a muhallinsa sannan ta bude freezer data gani ta kwance, nama ne dasu kifa da kayan miya a Nike cikin manyan bikitin roba, kaji biyu ta Ciro da Zuba a roba ta tarasu a famfo saboda kankarar ta saki.
Filawa ta diba ta kwaba da yeast da barking powder ta rufe ta koma ta gyara Naman ta Dora a wuta.
Wani ruwan ta Dora daban ta dauko Madara ta bude ta diba Mai yawa ta dama Zuba akan ruwa data Dora ta Dan zame murfin sannan ta ciro hollandia custard ta fasa ta dibi yanda take ganin zata ishesu ta dama ta aje a gefe. Plates da cups da duk abinda tasan za'a bukata ta dauko ta wanke ta aje a muhallin Daya dace.
Filawar data kwaba ta dauko taga ya tashi ta ringa murzawa round sai ta Gama ta shafa Mai a frying pan ta rage wuta ta shiga gasawa tanayi tana juyawa.
Biyu ta raba Naman ta dattaka rabi tayi source Rabin Kuma tayi pepper soup dashi ta dama custard din ta dafa coffee Kuma.
Tun daga sama Mahmud ke jiyo wani irin kanshi girki yayi tunanin ko da wani sabon restaurant a Nan kusa dasu, Saida ya fito yana saukowa yaji kamshin ya cika gidan.
Shigar kananun Kaya yayi yayi masifar kyau, yau shigar da yayi ta fito da ainihin ko waye shi Dan ba karya kana kallonsa kasan matashi ne Mai cike da Jin Dadi da wadatar arziki Dan agogon dake hannunsa kadai na millions of naira ne, shigar da ya Jima da daina yinta Nan gida Nigeria rabon da ya fito haka tun kafin ya shiga rubibi.
Hannu Faruq ya shiga tafawa Yana fadin "perfect match, wallahi kun Dace Ashe haka Auntyn tawa take? Haba shi yasa baka sauraren masu yi maka rawar Kai, ya Mahmud Ashe da abinda ka taka shiyasa kayi shuru ka kyale kowa, Mai irin wannan matar mezeci da tarkace irinsu Safna, wallahi na Dade Banga ma'auratan da suka tafi da imanina kamar kai da Aunty na ba, Dan Allah ka tsaya min na auri kanwarta pls🙏".
Ikon Allah Mahmud ya tsaya yana kallo lokaci Daya faruq ya gigice masa wato yaga zahrar kenan tunda ya sauko yaji gidan ya hade da kamshin girki yasa itace a kitchen, ko ba komai yasan Allah yayi Mata baiwar iya abinci a Dan zaman da sukayi ya fashimci hakan.
Shi rasa abin cewa ma yayi a Kan kalaman Faruq, Dan uwansa ne na jini, amma ya gigice da ganin matarsa, tab lallai da matsala Babba.
Bai nuna Masa komai ba sai Dan murmushi da yayi Yana fadin. "Ai mata ta ita kadai ce Bata da Kani ko kanwa, nine wanta nine komai nata Sai dai ka duba ko a Ina ne Zan shige maka gaba in Sha Allah".
"Dan Allah nidai ka taimaka ko cikin family dinta ne ayi min wanna alfarmar ka shige min gaba".
Kyale shi yayi ya nufi kitchen din lokacin ta Gama hada komai ta juyawa kofar baya tana cire jan bayan kwakwa zatayi amfani da ita in anjima.
Kamshinsa ya Fara fada Mata ya shigo gurin a hankali ta juyo, Yana tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa ya zubawa bayanta Ido,yanda ta juyo din nan shi Kansa da take halalinasa Saida yaji wani yarrr a jikinsa Dan gani yayi gaba Daya ta canza Masa ga wani irin cikowa da kirjinta yayi sosai.
Lumshe Ido yayi Yana tunanin lallai dole addinin musuluci da yayi Hani ga mutum baligi ya shiga gurin macen daba muharramarsa gaskiya. Yana can Yana tunani ya tsinkayi muryarta tana fadin "Ina kwana" batare data Kara kallon inda yake ba.
Bai amsa ba ya danyi gyaran murya.
"Meye Kuma Ina kwana? Na fada Miki ki iya tarairaya ta wallahi, kada garin kallon ruwa kwado yayi Miki Qafa, kina da kishiya fa kinsan idan ta fiki iya lafazi da tarairayata can Zan tare a gurinta".
Warrr tayi masa da sexy eyes dinta tana Masa wani kallo.
"Yes ko Baki yarda ba? yanzu na Kira Miki ita ku gaisa".
Kai ta girgiza Masa alamar A'a.
"Come on, zo Nan ki fada min bakya son kishiyar?"
Ya bude Mata hannuwansa alamar ta shigo, kafada ta make ta aje kwakwar ta nufi famfon cikin sink ta Fara wanke hannunta.
Cikin takunsa na nazantaka ya shigo ciki directly gurinta ya nufa Yana fadin "Ni gani na shigo sai nazo ki bani hot one tunda ni ba'a son nawa".
Bai jira tace komai ba ya saka hannunsa ya rungumeta ta baya Yana shafa cikinta.
Shiru tayi Masa kamar ruwa ya cinyeta, Jin hannun nasa ya nufi wata jihar yasa tayi saurin rike Masa hannu tasan idan ya karasa akwai damuwa sosai.
"Pls Dan Allah ka Bari kaga da bako a gidan kada ya jiyo mu fa".
Ta fada tana kokarin kwace kanta.
"Ok saboda shi Zaki hanani na sake kenan? To Bari na sender shi inda yafi wayo".
Dayan hannun ya saka ya ciro wayarsa yayi dialing din number Faruq, Sam batayi zaton kiransa zeyi ba, Saida taji Yana fadar "Faruq kaje wancen part din ka qarasa aikin gani Nan zuwa".
Bai jira yaji abinda yake kokarin fada ba ya kashe wayar ya Dora a gefen cabinet din kitchen yana fadin "to saiki sake ki bani hakkina tunda sirikinki yabar gurin".
Juyota yayi ya hade bakinsu ya cire rolling din, yana shafar gashin da yaji gyara ga qamshin hair spray sai tashi yakeyi ya jima Yana yamutsata kafin ya janye Dan Kansa yana Maida numfashi.
Tsugunnawa yayi ya dauko Mata veil din ya rufa Mata a Kanta Yana fadin "dauko wasu flask din ki zubawa Faruq nasa ki saka a basket na Kai Masa can idan ya gama ya tattara ya tafi gurin bikin da yazo".
"Me yasa? ba yace min shi qaninka bane".
"Ok. Dan Yana qanena saina zauna dashi gida Daya Yana kalle min Mata ko? Ai ya tafi shine mafita Dan akanki zamu iya batawa da kowa to maganin Kar ayi kada a fara, Dan Allah ki ringa saka hijab idan munyi Bak'i ba kowa ne ze iya kawar da Kai a kanki ba Kinga kuwa yanda Faruq ya gigice min na Nemo masa sister dinki, na fada masa babu Amma ya kasa fahimta sai rokona yake na samo Masa mace ko cikin family dinku ne"
Ya fada a Dan zafafe.
Shiru tayi ta nufi abinda ya sakatayi Saida ta Zuba Masa komai ta saka basket din ta aje a gefe ta dauko Wanda ta zubawa Mai gadi ta aje a kusa Dana Faruq din.
Malam Musa ya Kira yace yazo kofar parlourn su hadu, dauka yayi ya fice daga kitchen din yabar zahra da dogon tunanin akan abinda yace Faruq din yayi.

___
Chapter 20 · 0% Book details