← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 47

Sashe 41

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.............karfe bakwai dai dai mahmud ya baro gidan Hajiya Inna, bayan yayi wanka,dole tasa yazo gidan tunda a gidan Ammi baya da kayan sakawa ya duba baiga komai ba be sani ba ko canza musu guri akayi ko bayarwa tayi abinda be bi ba'asi ba kenan yaga gara ya taho Nan ya shirya kawai, shigar kananun Kaya yayi ya fito Shar dashi, Bai koma gurin Hajiya Inna ba duk da albishir din da tayi Masa na sinasir da tasa ayi Masa da pepper soup din kafafuwan shanu.
Yaso ya shiga gurin Abbie Amma gurin Amminsa zaya har yanzu bakinsu Bai Saba ba jiya da zummar suyi kwanan zaune ya shigo sai kuma aka samu akasi ya bige da allurar barci.
Ta kofar baya ya shigo part din Ammin har ya Haye sama Bai hadu da kowa ba dakin da Zahra ta kwana ya bude ba kowa sai kamshinta Wanda har ya Fara kama dakin, komai tsab ba tamkar ba'a kwanta gadon ba, kofar ya janyo ya nufi dakin Ammi yasan a irin wannan time din Bata ciki turo kofar yayi da sallama shiru sai kamshi kawai ke tashi a dakin.
Wani sanyin dadi ya ratsa shi jinsa yake kamar an sauke Masa wani katon dutse daga kansa, a tsakiyar dakin ya tsaya Yana tuno wasu lokutan baya da shigo cikinsa tamkar mahaukaci Yana magiya Amma ko gezau Ammi Batayi ba Saima tsallakewa da tayi ta wuce ta barahi a durkushe, Amma yau gashi ya shigo cikinsa da walwala da Aminci ba bacin Rai ba tashin hankali.
Kwanciyarsa yayi a Kan sofa Yana fashi "Alhamdulillahi Ala kulli halin".
Yayi zaman kusan minti talatin kafin yaji alamun bude kofar a Hankali ya cira Kansa daga wayarsa da yake duba sakonnin whatapps, Ammi ce ta shigo tunda ta shigo master parlourn ta tasan ya shigo gurin Bata Kara tabbatarwa ba Saida ta hauro saman Dan kamshinsa na daban ne.
Tsayawa tayi a gurin tana Kare Masa kallo, Masha Allah gani tayi ya Zama Babba ya cika Ido kenan jiya ganin tsoro tayi masa gashi ya Kara yin wani fresh dashi da gani ya samu nutsuwa ba kadan ba.
Aje wayar yayi ya taso ya nufota inda take tsaya murmushi yaki barin Bakinta ta Kuma kasa dauke idanunta daga kansa.
Ba wata wata mahmud na zuwa ya shige jikinta Yana fadin.
"Ammina fushi kike Dani ko? Nasan zakiyi fishi dani, gani Nazo kiyi min duk hukuncin Daya Dace Dani in dai Zaki yafe min, Dan Allah kiyi hakuri Nima bansan me yake faruwa Dani ba, Sam bana kaunar ko sunan garin nan naji an fada bana Kuma son naji ko sunan Wanda na sani in dai Yana Cikin family wallahi".
Zamewa Yayi ya tsuguna ya rike kafafunta sai hawaye.
Dan duk'awa tayi ta kamo hannunsa ya taso jansa tayi kamar Karamin yaro har gefen katafaren gadonta ta zaunar dashi itama ta zauna.
"Waya fada Mata Ina fushi da Kai? Ko alama dama ma banyi fushi da Kai ba sai yanzu da Ubangiji ya amshi rokona ya share min hawayena, bakayi min komai ba ko kayi ma na yafe maka duniya da lahira, Allah yayi maka albarka ya baka kariya daga sharrin dukkan wani abunqi, yanzu Ashe kana Bauchi state kayi zamanka akayi ta nemanka a turai da kasashen larabawa?".
"Ammi Nima fa wayar gari kawai nayi na ganni a garin bansan ta Yaya naje ba, Saida Habib Wanda ya ganni a yashe a kasa karkashin bishiyar gamji ya fada min a halin daya ganni nayi mamakin to ta Ina nabi naje can? da kafata naje ko kaini akayi? duk ban sani ba, Ammi Ina jinfa na rasa hankalina na wasu kwanaki ko watanni, Ammi hatta magana fa daina yinta nayi sai dai Ido Ina Jin abinda ake fada Amma bana iya bude bakina na mayar mutanen Nan ba Karamin jihadi sukayi ba gurin ceto rayuwata, Idan malam dawo har Azare Zan kaiki ki yiwa Baba malam godiyar abinda sukayi min kudi dai bazasu iya biyansu ba sai dai Allah mutane ne su masu karamci". Nan ya zazzage mass
Mata duk irin rayuwar da yayi a Azaren har ya zauna a dakin waje na amajirai.
Baiyi zato ba yaji shashshekar Ammi.
"Subhanallahi ! Haba Ammi me yasa Zaki Bata hawayenki abin fa ya Riga ya wuce, Ina fada Miki ne kawai saboda ki Kara yi min addu'a saboda bamu San me goben zatayi ba".
Knocking din kofa akeyi mahmud ya bada izinin shigowa.
Aishat ce da suhailat suka shigo itace Mai bin batool.
Da murnarta ta Karaso sai Kuma tayi turus tana kallon Ammi dake share hawaye Aishat ma jikinta sanyi yayi.

"Meya sameta take share hawaye?
Aishat din ta jefawa mahmud din tambayar.
Ammin ce ta Bata amsa

"Ba komai Hussein ne yake fada min halin rayuwar Daya shiga tamkar marara gata harfa so akayi a haukata min d'a a banza wallahi Ina istigifari ga Ubangiji kafin na fada, dama wani Allah ya bawa dukiyar Nan bashi ba da yake da kananun shekaru irin haka, wallahi da nasan wannan condense milk din itace sila Dana yiwa jama'a unguwa rabonta an wuce gurin,to ba haka zanen kaddarar take ba sai hakuri".

Suhailat ce ta dan matso kusa da mahmud tana fadin.
"Sannu Ya Mahmud ya jikin naka?"
"Jiki da sauki suhailat ya karatun kin Gama ko?".
"A'a da saura sai next year in Sha Allah".
"Allah ya taimaka".
"Amin"
Suka fada gaba daya.
Aishat ce tacewa mahmud "kaje Abbie Yana nemanka a parlournsa na part din nan, Ammi kema yace a Kai masu abin break fast can kamar na mutun bakwai".
Mikewa yayi yana fadin "Bari naje Ammi".
"Jeki ki fara hada abinda za'a shigar part din Abbie din keda sauda da Batool Kice iya Halima ta Zuba pepper soup din kayan Cikin Nan a babban warmer sauran ta saka a fridge".
"To Ammi"
Waje suhailat din tayi da sauri.
Saida suhailat din ta fice shima ya nufi kofar Yana Daf da ficewa Aishat tace masa.
"Ka fada Mata wacece zahra a gurinka Naga alamar ba iya playing match din zakayi ba".
Tsaye yayi shi Bai fice ba shi kuma bai juyo ba, sai Kuma ya juyo ya dawo a Hankali ya zauna a gabanta ya sadda Kai da gaske wani irin nauyinta yakeji Wanda Bai taba tunanin zeji kwatankwacinsa ba a tare da ita, a Hankali kamar baya son yin magana ya furta.

"Ammi ga zahra Nan an bani aurenta a Azare, tun watannin baya nace saina kawo Miki ita idan ta kwanta Miki a matasyin suruka ki saka Mata albaka ki kaita dakinta da kanki idan Bata yiiki ba ki saka a mayarwa da iyayenta ita a Basu hakuri, duk hukuncin da Kika yanke na karba da hannu bibiyu".
Yana gama fada Bai jira yaji abinda zata fada ba ya tashi ya fice da sauri Dan ba Karamin kokari yayi ba gurin kinar bakin waken fada Mata ba.

"Eh to da dai hakan yafi a mayar musu da yarnyarsu tunda akwai alkawarin da nayiwa fulani, Ina ga sai dai suyi hakurin gaskiya"
Abinfa ya iya jiyowa kenan daga bakin Ammin tasa bai it's cewa komai ba ya fice.
Daga shi sai Wanda ya halicce shi suka San abinda yake ji a kasan Zuciyarsa.
Aishat zatayi magana Ammi ta daga Mata hannu dole ta kame bakinta daga abinda tayi niyyar fada.
"Kuje kiyi serving din ku kafin na fito, idan kun Gama ki hadawa yarinyar Nan kayanta Wanda kikece min tsaraba yasa akayi Mata nafi son tabar gidan Nan kafin wani tsegumin ya fito".
Sororo Aishat tayi tana duban Ammi wadda ta tashi ya shige toilet kirjinta na bugawa da sauri da sauri.
"Allahumma Ajirniy fiymusibati, wannan wane irin tashin hankali ne Kuma? Allah ka kawo sauki".
Fita itama Aishat din tayi jikinta a mugun sanyaye, bedroom dinta ta nufa ta yiwa Zahra magana suka fito tare, da kyar Aishat tayi ta maza ta danne zuciyarta sukaci abincin tare da su suhailat duk da basa cin abinci da wuri Amma dole tasa tunda Umarnin Ammi ne.

**
Chapter 41 · 0% Book details