← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 47

Sashe 22

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk iya kokarin sahura na taga magaji abun ya gagara wayar zilan ma an rufe ta, ko Kuma network yaki bada hadin Kai.
Wata dabara ta fadowa sahura, da sauri ta nufi gurin Bala driver tana fatan samun mafita a gurinsa saboda Bata fatan ta rasa abinda Mama ta kwadaita Mata zata Bata.
Yana aikin goge mota da alama fita zasuyi da Abba, sallama tayi Masa suka gaisa sannna tace Masa.
"Dan Allah malam Bala ko zaka taimaka ka kwatanta min gidan da yarinyar Nan zahra suka koma naji ance sun tashi daga Nan hayin banki,Kuma na nemi duka lambobinsu ban samu ba".
Ta fada tana fatan samun abinda take so.
Tunda ta fara Kora bayani malam Bala ya dakata da aikin da yakeyi Yana kallon ta Saida ta Kai aya sannan yace Mata.
"Haba sahura yaushe Zan dunga bin diddigin yarinyar da take gidan mijinta, ai wannan rashin lissafi nema ma wallahi ai da kunya ki fito neman gidan Zahra a Nan gurin mu alhalin ga uwarta can a cikin gida, to ke me zakiyi a can Wanda Baki son uwarta ta sani".
Cikin rashin yarda da Kai ta Fara fadin.
" A'a wallahi kasan wani abun alherin idan mutum zeyi baya son a gani sai dai shi yaron ya fadawa uwar tasa daga baya".
"To shiga ciki ki nemi bayani dole"
Ya juya yaci gaba da aikinsa ya bawa banza ajiyar ta, it's Kuma ta koma ciki da ledarta a hannu, mita yake shi kadai.
"Haba mutane sai halin tsiya, Nan gaba kadan wallahi wannan mijin nata ze shayar da mutane mamaki Dan naji Alhaji Yana wani furuci jiya bansan dai dawa yake waya ba Amma Ina ganin da bincken da yake yi akan yaron Nan Kuma jiya Wanda ya saka shi ya dawo Masa da amsa".

Shi kadai yaci Baga da Yan maganganunsa.
Duk iya dabara Mama tayi Amma babu wani cigaba dole ta nufi bangaren Ammah.
Cikin iya makirci Mama tayi knocking a kofar falon Ammah.
Autane ya taso ya bude mata kofar, parlourn yasha gyara sosai sai kamshi ke tashi da sallama ta shiga, duk sai ta Raina nata dakin Dan babu karya ko yanayin gyaran da banbanci.
"Mama Ina yini".
ba zato Mama taji muryar magaji yana gaisheta daga bayanta.
Da sauri ta juya tana fadin.
" A'a Magaji! Daman kana gidan Nan tun dazu nake nemanka na rasa, Dan Allah tashi ka taimaka ka raka sahura gidan Zahra akwai wasu Kaya Dana saka a kawo Mata Amma shiru basuzo ba sai yau da safe shine nake son a Kai Mata su banso ko Ammah ma ta sani ba, sai dai zahrar ta Bata labari, to anje ance Wai basa gidan".
Zama magajin ya gyara, Yana kallon Mama Ido cikin Ido.
"Wai Mama kina maganar zahra ne?".
"A'a to da maganar wa nake maka".
"To ai Bata garin nan tun jiya suka wuce Kano, kinsa mijin nata baya kasar suna tare da Baba malam a India, to yafi son ta zauna a ca gaskiya, kin San manya Basu fiye son zaman gefe ba gara gurin da yake da kyakykyawan tsaro"
Rasa abin fada tayi, ta rasa zancen wa zata Kama na magaji Kona zilai data ce Bata San unguwar da suke ba, kenan ba'a garin Nan ba kenan take nufi,ai da mamaki Daman Ace Wai zilai Bata San sunan unguwa a garin Nan ba, to Wai waye ma babban da taji magaji ya fada shi yaron ko Kuma waye?.
Tunda magaji ya Gama fada Mata abinda zahra ta fada masa ya koma yayi kwanciyarsa, yaci gaba da latsa wayarsa.
Fita tayi daga parlourn ta koma nata part din duk dabara takwance mata Kuma Bata taba zaton wankin hula ze kaita dare ba sai yanzu, tana fita Ammah na shigowa.
Magaji Ammah ta kalla tana fadin.
"Waye ya fita yanzu?"
Tashi zaune sosai magaji yayi haka Musaddiq ma matsowa yayi tana fadin.
"Ammah Wai Ya magaji yaje ya raka sahura gidan Adda Zahra".
Gyara Zama magaji yayi sosai Yana fuskantar Ammah.
Kinsan wani Abu Ammah Anya zahra Bata San wani abu ba game da maganar zuwan da sahura ba zatayi ba? saboda ina zaune Zahra ta kirani ta kada min warning akan kada na kuskura na kawo sahura inda take, tace min na fada mata Bata Nan sun koma Kano, to yanzu magamar ce ta kawo ta wai na dauki sahura na kaita gidan zahra zata kai Mata sako shine nace Mata ai sun koma Kano".

Jinjina Kai kawai Ammah tayi tace.
"Allah ya kyautata".
A binda ta iya fada Kenan tayi gaba abin ta, ita lamarin Mama har ya daina ma Bata mamaki tausayi take Bata hassada ai mugun ciwo ce.

*

Sai kusan Sha biyu na agogn kasar India Habib ya tashi, yayi mamakin yanda lokaci yayi gudu haka, da sauri ya nufi toilet Yana yiwa Kansa fadan me kenan yayi shida ya biyo marar lafiya Amma ya bige da dogon barci irin haka, "ko Yaya Baba malam din yake?" Ya yiwa Kansa da Kansa tambaya.
A gaggauce yayi wanka ya fito, Bai wani Bata lokaci ba ya shirya ya fito yana ayyana Allah yasa Mahmud ya dawo Dan jiya sun Dade suna dakon zuwansa Amma shiru dole suka hakura suka kwanta.
A parlour ya iske mahmud Yana ta faman aiki a cikin computer desktop wadda take girke a parlourn, daga gefe Kuma wasu indiyawa ne su biyu Yana musu magana da harahen indianci suna amsa masa, da alama Kamar Umarnin wani Abu yake basu, har Inda yake zaune Habib ya Karasa yayi Masa sallama ga mamakinsa sai yaji gaba Daya sun amsa masa, Shima Mahmud barin abinda yake yayi ya juyo Yana sakin murmushi ya mikawa mahmud hannu sukayi musabaha, sannan ya mikawa bakin mahmud suka gaisa, ganin Kamar Habib na dari-dari dashi dan Yana kula da yanda yake tsare shi da ido, sai idan yaga zasu hada Ido yayi saurin janye nashi, tashi muhmud yayi daga Kan computer ya riko hannun Habib Suma sauran biyun suka rufo musu baya.
"Bakon india, nasan ka gajine shi yasa na Hana Abubakar tashinka nace ya barka kayi barcin gajiya tunda ka gaji da yawa".
Ya fada suna Zama a kujera two seater,
"Bari kawai ni kaina nayi mamakin barcin da nayi, Ina Abubakar ne?".

"Sun fita da Mr Ajey kasuwa, inaga sun kusa dawowa ma yanzu, ga abinci nan kaci idan ka gama zaku fita dasu Mr Salman zasu rakaka kuje a Sami kayan sakawa tun dazu suke jiran ka fito ku tafi baka tashi ba, ga abincin can ka duba Wanda zaka iyaci sai ku wuce, nima Zan shiga naga doctors din dake kula da Baba malam yanzu suka nemi ganina tunda tun jiya suka shiga dashi dakin bincike na musamman sai gobe za'a fito dashi, kasan tsare-tsaren Asibitocin su da banbanci da namu na Nigeria"..
ATM mahmud ya mikowa Habib na bankiya juya Kuma yayiwa su Mr Salman maganar da Habib besan me aka fada ba, ya wuce ciki Yana fadin.
"Kada ka dauko kaya kadan Dan bamu San how long samu zauna a Nan ba sai yanda Hali yayi".
Shi dai Habib kasa cewa komai yayi Dan ya gama Shan ruwan mamaki ba kadan ba, Mahmud din da suke kwana su tashi tare ne wannan? ko a mafarki be taba kawo haka ba".

Cikin abinda be wuce minti latatin ba Mahmud ya fito cikin kananun Kaya yayi fresh dashi ya fice daga gidan, har lokacin su Abubakar Basu dawo ba, da kanshi yake driving din, da Dan hanzari yake tafiya saboda gaba Daya hankalinsa yayi Asibiti.
Lokacin Daya shiga direct office din consultant din ya nufa, be same shi a office ba Yana cikin ward inda yake duba patient dinsa, baifi zaman minti goma ba doctor din ya dawo da zugar wasu dalibai a bayansa Yana ganin mahmud ya gane shi, tunda yaji yana Jin yaransu yake Nan Nan dashi.
A cikin office din wasu hotuna ya dauko ya aje a Kan table dinsa yace mahmud da sauran daliban su matso.Dalla Dalla ya shiga Yi musu bayanin yanda ciwon yake da yanda yake yiwa mutum illah idan har ba'a Farga an kawo mutum Inda za'ayi Masa aikin gaggawa ba saboda yanda spinal cord din ta matse to komai ze iya faruwa za'a iya rasa kafa da amfanin kasan Jiki na har abada, Dan haka daga Nan zuwa Kwana uku za'ayi wannan aikin, Amma dole charges zasu karu tunda sun Kara gani karaya a kashin hakarkarinsa na hagu guda biyu sai kashin mukamikinsa Daya goce".
Take a Nan mahmud ya nemi a bashi bill na Karin charges din da aka samu, yaje ya biya komai ba damar ganin Baba malam haka dokar take,yana tafiya a Kan barandar Asibitin Yana sauri ya Karasa gurin Daya aje mota yaji daga bayansa ance.
"Waye nake gani Kamar Mahmud Dange".
Da sauri ya juya Yana mamakin waye wannan yayi Masa farin sani haka.

Faisal ya gani kanin Aunty Surayya matar uncle Mustaphan zasuyi sa'anni da mahmud din, cikin fara'a Mahmud ya Fara fadin.
"Faisal bungudu Long time, Daman talaka Yana ganinku?".
"Kaji ka da wani magana Kai ganin ku ai sai Mai sa'ar gaske, Nigeria kun Mata tawaye ma kwata-kwata yaushe ake ganinku, meya kawo ka Nan ne haka ko patient gareka".
"Eh wallahi wani Babana ne ya samu spinal cord injury muka kawo shi Nan, Kai Kuma meya kawoka?"

"Wallahi Alhajin mu ne ya samu accident tun kusan wata hudu da suka wuce, karaya ya samu a cinya, anyi gyara har sau uku abun yaki shine, wani doctor da muke gani a wani private orthopedic hospital a Sokoto yayi Mana hanya mukazo nan, kaga jiya uncle Mustapha ya bar Nan kasar tunda shine ya kawo mu sai da ya Gama Mana koma".

Jinjina Kai Mahmud yake kafin yace.
"Allah ya bashi lafiya, ga jikin girma ga lalura muje na ganshi na duba shi".
Tare suka juya Faisal din Yana fadin.
"Wallahi Rabon mu hadu ne nace Bari na koma masaukina nayi wanka na huta tunda ba wata damuwa a tare dashi sunce sai Nan da sati uku zasuyi Masa aiki sai sunyi treating din gurin da infection ya Kama sannan zasu sake Masa aiki"
Chapter 22 · 0% Book details