← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 47

Sashe 2

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankalin Zahra be kwanta ba so sai Saida ta ganta a cikin falon gidan su Sajida, Mai aikinsu ta bude Mata parlourn tana fadin "A'a marhabin maraba da Amarya sannu da zuwa".
Ta fada tana murmushi, tare suka shigo ciki.
"Yauwa Mama Hauwa sannu da gida, ya naji gidan naku Shiru ko su Mamar basa nan ne?"
"Wallahi sunje Rimin sumaila duba kanin Baffa bashi da lafiya,a nan ya kwanta a Asibitin Murtala to shine sukaje su Kara duba shi da jikin".
"Allah sarki ko kawu Musa?"
"Shine Ashe kin sanshi".
Eh nasan shi Mana, har a gidansa mun kwana lokacin da mukaje da sajida. Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne"..
"Allahumma Amin, Bari na bude Miki dakin mutuniyar ki shiga na kawo Miki abinci can, inaga sai dare zasu dawo tunda suka Kai har wannan lokacin".
Wanka ta shiga ta Dade a toilet din kafin ta fito tana tsane jikinta da towel, lotion ta shafa ta dauko Rigar material marar nauyi ta saka a cikin kayan sajida.
Jallop din kuskus aka kawo Mata wadda Tasha kayan lambu da pepper soup na kayan ciki da kunun aya Mai sanyi da ruwa.
Abincin taci ta koshi ta dora da kayan sanyi tayi hamdala ga Allah ta kishingida jinta take fresh idan Allah ya kaimu safiya ta karawa motarta Mai, ganinta a araha yasa ake garata kamar kwallo.AUREN HUCE HAUSHI.

MAMAN FATEEMAH

Page 42.

_______Abu kamar Wasa har kusan karfe taran dare ba zahra ba labarinta, iya Rahane mommy ta Kira tana tambayarta kosu Rukayya sun dawo? Dan bazata fada ba direct tace ana neman zahrar hakan dabara ce ta tambaya a fakaice.
Amsar data Bata ita ta Kara tadawa kowa hankali cewa tayi "Basu dawo ba tun fitar safe da sukayi ga zulai ma duk ta shiga damuwa tace tun yamma Ammarta ke Kiran wayar zilan tace wayar zahara'un Bata shiga".
"Yanzu ya za'ayi kenan?"
Rukayya ta tambaya.
"Ni damuwa ta Daya kada ta fada mugun hannu Dan ma dai ba lallai ansan matar waye ba Amma yau abin tsoro ce kiransa zanyi kawai na fada Masa halin da ake ciki ko yasan wasu 'yan uwansu a nan kanon, tunda barin Kashi a ciki baya maganin yunwa gara ya fada kawai asan Yanda za'ayi tun guri be kure ba.
Number dinsa yayi ta try Amma amsar Daya ce a rufe take.
Da kyar ya mayar dasu mommy gida har Rukayya a gidansu ta sauka, to ta koma tacewa baiwar Allah da sukazo tare zahrar ta Bata ko me?"
Duk wani lissafi ya gama suncewa Sameer, duk wannan Abu be tashi faruwa ba Saida sukazo gidan kakarsa, ita kanta Hajiyar makwararin tashi Dan kukanta tana mitar yarinyar Nan Bata kyauta Mata ba ta rasa a inda zatayi irin wannan shegantakar sai a gidanta.
Jiki ba kwari Sameer ya shiga gidansa, sau Daya Fateeha ta kalleshi ta dauke Kai ta cika fam da fushi tun safe Daya fice Bata Kara sakashi a idanunta ba, ta kirawo shi ya Kai sau biyar sai dai yace Mata gashi Nan Amma bezo ba sai yanzu wurin Sha dayan dare.
A kusa da ita ya zauna ta kauda Kai, hannu yasa ya dauki yaron a Kan cinyarta, yasa hannu Daya ya tallabota ta hada da babyn ya rungumesu, Jin ajiyar zuciyar da yake saukewa a jajjere yasa Fateeha ta gane da matsala.
"Wai menene?"
Ta fada cikin damuwa.
"Bari kawai wlh hankalina a tashe yake, tun bayan Azzahar Zahra ta fice daga gidan Hajiyar makwarari bamu San inda ta nufa ba, duk inda muke tunanin zataje munje Bata nan".
Itama mantawa tayi da fushin da takeyi dashi ta Fara sallallami "Yanzu Ina ta tafi? Kadafa wani Abu ya sameta kasan mutane yanzu gaskiyar su kadan ce".
Dafe kansa da yake Sara Masa yayi "Bana tunanin haka gaskiya da Kanta ta fita ta tafi kawai dai an Bata Mata Rai ne ban Kuma yi tunanin abin yayi Mata zafi haka ba da bazan barta a gidan Hajiyar ba, amfani tayi da masu kawo lefen mujahida ana can gurin karbar lefe ita Kuma ta fice daga gidan Dan akwai Wanda ya fada min Yanda ta fito nasan da niyya ta fice abunta".
Zuru Fateeha tayi tana sauraren mijinta.
"Ka Kira ka fada masa?"
Kai ya girgiza Yana fadin na kasa samunsa nafi one hour Ina nemansa ban same shi ba".

*** *** *** ***
Karfe Tara su Umman sajida suka shigo gidan lokacin Zahra na parlour suna hira da Mama Hauwa, turus Maman tayi ganin zahra ko rantsuwa tayi Babu kaffara, wannan ba zuwan arziki bane amma sai ta share tana fadin "wa nake gani haka?"
Dariya Zahra tayi tana fadin "Umman mu sannunku da hanya".
"Yauwa sannu,aike za'a yiwa sannu kin sha doguwar tafiya".
Shiru zahrar tayi batace komai ba, kannen Sajidar ne suka Fara gaisheta suna fadin "Aunty kin rigamu zuwa munata cewa idan Ya Abba ze Kai Miki sakonki da Baffan Rimi ya bada a Kai Miki zamu bishi sai gashi Kuma kinzo"
Karamar kanwarsu ta janyo tana fadin "ai zakuje ko mutuniyar tunda anyi min Alkawarin zuwan".
"Eh zamuzo Aunty zahra".
Nusaiba ta fada suna Zama kusa da zahrar, yayin da Maman su ta wuce bedroom dinta tana cike da tunani barkatai a zuciyar ta.
Tana shiga jakar hannunta ta zuge ta Ciro wayar ta, Ammah ta Kira Dan bazata Zama uwar banza ba da alama gudowa yarinyar Nan tayi.
Lokacin da Kiran ya shigowa Ammah tana duba wasu kaya da Hajiya kaltume ta Aiko Mata dasu ne.
Ganin Umman sajida ne yasa ta aje kayan ta dauki wayar tare da sallama.
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
"Hajiya ya gida ya wajen Amare? Ina ta son na Kira mu gaisa Allah Bai nufa ba sai yau, itama zahrar mun kwana biyu bamu gaisa ba".
"Wallahi kowa lafiya, Amare Kuma suna nan kusa daku Bata jin dadi ne mijin ya matsa suzo Nan Kano a dubata ni tun safe da muka gaisa da wayar zilai ban Kara samunta ba, na Kirawo zilan ma tace min har yanzu Basu dawo ba duk ta tada hankalin ta, nace ita da ba ita kadai ta fita ba tare suke da amininsa da kanwarsa, Kinga duk inda suke ai suna tare".
Shiru Maman tayi kenan hasashenta ya kusa Zama gaskiya Kenan.
"Hajiya ga zahrar a gidan nan,yanzu muka dawo daga Rimi Sai na tarar da ita Ina ganinta nasan ba lafiya ba Ashe garin sukazo ta kawo min ziyara".
Jim Ammah tayi tana jinjina lamarin.
"Anya kuwa ki dai saka Mata Ido zuwa safe kome ke nan sai ki fada min idan anzo daukarta to da sanin mijin tazo idan Kuma tace zata tafi ki hanata ki fada min na gode kwarai Allah yayi Mana jagora ya Raya Mana zuri'a".
"Allahumma Amin". Sukayi sallama.
Zuciyar Ammah sai bugawa takeyi a hankali ta furta "meke Nan Kuma? Ni Asma'u Allah ka taimaki 'yar marainiyar Allah, matsaloli daga an toshe wannan sai waccen ta bulle Allah yayi Mana maganin wannan matsaloli yanzu kuma ko menene damuwar datasa ta tsallake tabar inda suke gashi ta Kama wayar ta rufe Dan ma kada a San inda take,ai kuwa zamu gauraya bazan dauki shashanci ba".
Ta hada duk kayan ta zuba a ledar da aka kawosu ta fice daga dakin ta nufi dakin Abban Yara tunda ita keda girki.

Saida Umman sajida tayi wanka tayi sallah sannan ta fito har lokacin suna falon da yaran direct dining ta nufa taci abinci sannan ta dawo falon.
Gaisheta zahra ta Karayi tana tambayar ya Mai jikin,
Dasu Baffa.
Sun dauki lokaci suna hira kafin Ummar tace "Wai daga Ina kikazo ne daga can Azaren ne ko Kuma kinzo nan garin ne?"
Shiru zahrar tayi kafin tace "ganin likita nazo akan wannan ciwon marar da bakeyi duk wata".
"Ikon Allah kuma ke kadai Kika taho ganin likitan kamar marar gata".
"A'a bani kadai nazo ba tare da Aunty Zilai Mai aikin Ammah mukazo tana can a Nasarawa G.R.A".
"Ok, to mryasa baku taho tare ba Nan din".
Shiru tayi Bata ce komai ba, ganin da Yara yasa itama ummar tabar zancen.
Kafin kowa ya tashi Zahra ta tashi tana fadin "Umma Bari naje ba kwanta barci nakeji"
"To Allah ya tashemu lafiya.
Basu Dade ba Suma suka shige daki Daman duk sun gaji.

Lokacin da Ammah ta shiga dakin Abban samun Mama tayi kane -kane tana ta zuba zance da kudi a hannunta masu Dan yawa da gani a gurin Abban ta Karba, cikin alamun rashin gaskiya mamar ta Fara fadin. "Aina leka parlourn ki naji Shiru nayi zaton kina Nan wallahi Ashe Baki shigo ba"
Fuska ba annuri Ammah tace. "Eh ban shigo ba idan kin gama na dawo ta juya har Takai kofar ficewa Abban yayi gyaran murya Yana fadin "dawo ki zauna Ina Kuma Zaki ita ta tashi ta tafi tunda ta gama abinda ya kawo ta"
Jiki ba kwari Mama ta tashi tana fadin "ai Kam na Gama Allah ya tashemu lafiya nagode Allah ya Kara arziki".
Ta nufi inda Ammah ke tsaye tana fadin "mu kwana lafiya ki tayani yiwa Abban yara godiyar abin arzikin Daya bawa Najjahi na kudin registration".
"Masha Allah! An gode Allah ya bada sa'a".
Ta fada fuskar ta Babu walwala ko alama, da gaske ta kule Abun Yana so ya Zama rainin hankali tayi noticing dinta duk ranar girkinta sai ta dunga Karakaina a part din Abban Amma idan tasan wata ai Bata San wata ba.
Dawowa tayi ta zauna kusa dashi "meya Bata Miki Rai ne Kika juya Zaki bar dakin?"
"Ba komai".
Ta Bashi amsar in short.
Haka Nan yabar zancen badan ya gamsu da abinda ya fada ba.
"Neman izinika na shigo zanje Kano gobe in Sha Allah"..

Saida ya Kare Mata kallo tsab sannan yace. "me akeyi a kanon da zakije?"
Kai ta girgiza ba komai zanje barka ne na yaron nan Sameer ranar da yazo daukar su Zahra yake fadawa magaji anyi Masa haihuwa an samu takwaran mijin Zahra".
Chapter 2 · 0% Book details