Sashe 43
Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
.............
Cikin wani irin karsashi mahmud ya riko Aishat Yana fadin.
"Meye haka kikeyi? Kinfi Ammin sannin abinda ya Kamata tayi ne, Ni ne nace Mata idan zahra Bata kwanta Mata ba tayi abinda ya Kamata, ina cewa a gabanki komai ya faru? to meye kuma na daga hankali Allah yasa hakan yafi Alkhairin".
Ya juya ya fice daga part din gaba daya, mota ya shiga yabar gidan gaba daya, isolation yake bukata a yanzu Dan Kansa babu abunda yake sai Sara Masa besan me yasa Ammi tayi hakan ba amma jikinsa be bashi Wai an rabashi da precious bane har abada, akwai wata manufar yin hakan duba da zuwan gaggawa da yaga su mummy Badi'a da Hajja zuwaira matar kawu yusufu sunyi yasan da magana a kasa Kuma ga tafiarma a sirrance akayita ta kofar baya motarma Mai duhun glass ce,
Duk abinda mahmud ya fada Ammi taji shi sarai Amma tayi gaba dole ta nemarwa matarsa uwar 'ya'yansa Qima da mutumci bazata biyewa yarintarsu ba a haifi Dan da babu idanu.
Sama ta Haye tana lalubo number Aunty Surayya matar uncle Mustapha.
Daki Aishat ta koma ta dubo ko Afnan ta tashi tunda Abulkhairi Yana gurin Batool, Amma fa hankalinta yaki kwanciya so take taji daga bakin Ammi din dole su zauna.
Kwanciya tayi tana lalubo number sweet heart dinta dole su ta fada Masa halin da ake ciki saboda a gabanshi Komai ya faru akan yanda ya gigice daga yi masa fushin d'an lokaci to Ina ga anyi Mai dungurungun kuma, ai sai yanda Hali yayi tasan abinda ya fada kawai dauriya ce bawai har Zuciyarsa haka abin yake ba.
*******Tunda su zahra suka dauki hanya tayi shiru mummy Badi'a ke yiwa Zahra Hira da hannunka Mai sanda akan abubuwan da suka danganci zamantakewar aure da irin 'yan dabarun rike miji yaji ba wata sai Kai, ita dai zahra daga eh sai a'a take fada ko hanyar Bata lura da inda suke nufa,ita dai Hajja zuwaira barcinta take Sharawa tunda suka dauki hanyar dodar, tafiya Malam Habu yakeyi iya tafiya ga kuma lafiyayar mota, a Kano sukayi sallar azzuhur da la'asar suka dauki hanya zahra tayi mamakin yanda wannan bawan Allah yasan hanya haka gashi dai ya fara manyanta.
Karfe shida da rabi suka shigo Cikin garin Azaren katagum, dan rage tafiya Malam Habu yayi ya Dan juyo Yana fadin 'ranki shi dade Ina muka nufa gamu Allah ya kawo mu Azare".
Hanya ta ringa nuna Masa Yana bi har kofar gidan Abba.
"Masha Allah".
Mummy Badi'a ta fada a ranta ganin gidan da suka zo da gani Suma ba kashin yadawa bane da nasu rufin asirin daidai gwargwado dan ko makaho ya Shafa yasan da abun.
Horn biyu malam Habu yayi Baba sani ya leko ganin Bai sheda motar ba ya fito ya nufo su dai dai gurin window din driver ya leko gaisawa sukayi kafin Zahra tace Masa.
"Baba sani nice zahra ka bude Mana".
Da sauri ya juya Yana fadin "sannunku da zuwa ai bangane ba sai yanzu".
Suna sako Kai Cikin harabar gidan magaji na fitowa da sauri da alama wani uzirin ne ya taso masa ganin bakuwar mota Mata na fitowa yaja ya tsaya yaga su waye ganin Bai sheda su ya nufi hanyar ficewa yayi taku kadan yaji maganar Zahra daga bayansa tana fadin.
"Sulaimanu".
Da sauri ya juyo yana dariya.
"Kai Kice cere Bina ce ta shigo garin".
Mummy Badi'a bata san lokacin da dariya ta kubce Mata ba, tana kallon magaji Daya nufosu da sauri.
Gaishe dasu mummy Badi'ar yayi Yana fad'in.
"Sannunku da hanya Bismillah ku shigo, yayi gaba da sauri don ya isarwa da Ammah sako, haba Ashe da dalili shi dai yaga anata faman dafe-dafe Daya tambaya ba Wanda ya bashi amsa, Zahra na gaba su mummy Badi'a suna bayanta cikin gidan shiru ba kowa sai su zilai da sahura suna gyaran kitchen din waje daga nesa sahura ta hango su zahra zasu shige part din Ammah.
"Kai zilai Kinga kamar uwar dakinki sa wasu mata sun shiga part din Ammah".
Banza zilan tayi Mata tana ganin tsabar gulmace kawai irinta sahura wace zahrar kuma wadda bata kasar ma gaba daya, jin tayi banza da ita yasa ta hakura taci gaba da abinda takeyi.
Su zahra na shigowa Ammah da magaji suna fitowa daga kofar baya wadda aka Samar da ita saboda part din Abba.
Cikin farin ciki Wanda har ya bawa zahra mamaki, Ammah ta taresu tamkar tasan da zuwansu, Fadi take "sannunku da hanya kunsha doguwar tafiya nayi ta neman zahra dazu network ba kyau sai hakuri nayi".
Zahra taso ta shige jikin Ammah kamar yanda ta Saba Amman sai taji nauyin yin hakan a gaban bakin Ido sai dai dan kwantar da kanta tayi a jikin Ammah nan da nan taji wata karaya da tausayin Ammah ya kamata tunda ta Zama budurwa Ammah Bata huta da kwaramniyarta ba yanzu ma gashi ana murna anyi auren ga Kuma wata sabuwa ta bullo In "yan caca.
"Bismillah ku zauna Hajiya sannu sannunku fa"
Alawiyya ce ta shigo da katon tray dauke da abubuwan sanyi ta aje tana gaishe da bakin nasu.
Mummy Badi'a ce tacewa Ammah.
"Yauwa sannu Hajiya ya muka sameku".
"Lafiya kalau Alhamdulillahi"
Ammah ta gaishe da Hajja zuwaira.
Ruwa kawai suka Sha kafin a rakasu dakin da akayi musu masauki a Nan part din Ammah din Amma Yana daga can gefe daban ba'a fiye amfani dashi ba tunda da wadatar dakuna.
Magaji ma fita yayi da ruwa da kwalin exotic da Coke na gwangwani yaje ya budewa Baba Habu dakin Baki na waje lokacin Yana gurin Mai gadi suna Hira.
Kayan dake Cikin motar malam Habu ya Fara fitowa da magaji yana fadin.
"Dan Allah shigar musu da kayan nan".
Zahra dakin da take Zama ta shige tana mamakin yanda Ammah Bata nuna tsahin hankalinta ba duk da Batasan dalilin zuwansu ba ita da 'yan uwan Ammi.
Cikin Kan kanin lokaci magaji ya Gama shigo da kayan ya zube su a parlour ya shiga ya fadawa Ammah.