Sashe 36
Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
......... Tunda jirgin su zahra ya sauka a filin jirgin sultan saddiq Abubakar dake Sokoto gabanta ke faduwa,tasan a Nan ne komai fa ze iya tabbata ko ayi ko a fasa gata a Sokoto sai Kuma abinda Rabbi Izzati ya hukunta shi ne ze tabbata, Afnan ce a sabe a kafadarta tana takawa a hankali tamkar Bata son taka kasar Dan da gaske ta Gama yin giving up a cikin Lamarinsu da mahmud.
Aunty Aishat ce tsaye a Kan kayan da sukazo dasu Saida komai ya kammala sannan ta nufo inda Zahra suke ita da Afnan yayin da Abulkhairi yake biye da ita kafa ya kafa.
Kamar tare Aishat din suke da Sameer Dan tana karasowa shima Sameer Yana karasowa da waya a kunne da alama doguwar waya yakeyi, saida ya Gama sannan su zahra suka gaishe dashi har Aunty Aishat na fadin.
"Nayi fushi kaje har India amma ka kasa zuwa mu gaisa".
"Kiyi hakuri kinsan halin kayanki bashi da lokacina a lokacin Kuma infact ma dai bai barni na zauna ba".
"Ai shikenan Daman ku Ina kuke Zama guri Daya tamkar marasa gaskiya Baku da standard gurin Zama dole ku canza yanzu kun aje iyali suna da hakki a kanku baze yuwu ki ringa Abu babu lisafi ba Daman kasan tun farko Ammi Bata son wannan dabi'ar taku ko misqalazarratin Sai dai da yake Abbie ya tsaya muku ne yasa dole ta hakura".
"Wannan gaskiya ne Auntyn mu za'a gyara in Sha Allah ko Baki fada ba zakiga canji ke dai kisa Ido kawai zakice na fada Miki".
"Allah yasa hakan ta kasance".
"In Sha Allah".
Sameer ya fada yana Dan kallon zahra ta gefen Ido tana ta yiwa Afnan Wasa.
"Madam barka da sauka sokoto Allah yasa mun shigo kenan, yasa Albarka a cikin rayuwar da zakiyi a cikinta".
Dan murmushi tayi, yayin da Aunty Aishat ta amsa da. "Allahumma Amin, ni jikina ya Gama bani zahra Alkhairin mu ce".
Kayansu aka dunga jida ana kaiwa mota Sameer sai mita yake yiwa Aunty Aishat akan sun lodo Kaya bayan Wanda suka turo jiya sukazo yauma ga wasu.
Kunnen uwar shegu tayi masa sufa sunfi son daga su sai kayan jikinsu, tunda suka dauko hanya zahra ke kallon garin, yayi matukar burgeta ba kadan ba tayi santinsa duk da hankalinta ba a kwance yake ba Amma ba karya sokoto tayi Mata 💯% sai dai Bata San meze biyo bayan zuwan nata ba, wata zuciyar ta fada Mata.
"Khairan in Sha Allah"
Take ta Fara addu'ar sauka a sabon garin da kaje ba garinku ba, Dan harga Allah ta manta.
"RABBI ANZILNI MUNZILAN MUBARAKAN WA ANTA KHAIRUN MUNZILIN".
Ta fada a zuciyarta tana rokon ubangiji ya dafa Mata a cikin lamuranta gata ta shigo garin da babu uwa ba uba ba dangin iya babu na Baba sai wannan bawan Allahn shi kadai ta sani, kallon garin taci gaba dayi daga kasan Zuciyar ta Kuma abubuwa ne rututu gasu Nan.
Wani katafaren gida taga Sameer ya dosa tamkar fadar shugaban kasa, Zahra hankalinta ta tattaro ta nutsu taga Nan kuma Ina ne Sameer ya kawo su Yana tsayawa a kofar katafaren gate din Mai Kama Dana kofar gari saboda girmansa wasu masu uniform suka taso su uku suka Karaso gurinsu Sameer kafin su Karaso sameer ya sauke glasses dan bada da baya,suna sameer ne suka gaisa sannan suka gaisa da Aunty Aishat da suke zaune a baya.
Katafaren gata din aka bude musu suka shige, " masha Allah".
Abinda zahra ta fada kenan a zuciyarta, wasu gine-gine take ganowa kamar a cikin film, an kawa gefen titin da flowes masu kyau da fitilu compound din ba mutane sosai sai 'yan tsiraru masu banruwan flowers har kofar part din Ammi na baya sameer ya kaisu ita dai zahra ba baka sai kunne Dan ba karya gidan gida ne tamkar dauko ginin akayi aka Dora a gurin a zuciyarta take tunanin meya yi zafi da har Wanda yake rayuwa a nan ze tsallake ya bar shi yaje yana rayuwar kwanan shago, ita dai saida Aunty Aishat ta Dan tabata ta dawo hayyacinta.
"Mu shiga ciki?"
Fitowa tayi dauke da Afnan a kafadarta tabi bayan Aunty Aishar wadda me rike da hannun Abulkhairi, numbers Auntyn ta saka ta bude kofar Dan juyowa tayi kadan tana fadin "Bismillah".
A hankali zahra tabi bayan wasu parlours suka ringa ratsawa na garari sai da suka wuce parlour biyar sannan Aunty Aishar ta cewa zahra ta Dan jirata tana zuwa ta nufi upstairs tana rike da Abulkhairin.
A kan center carpet zahra ta zauna tana wasa da Afnan wadda duk tayi laushi ta gaji danma yarinya ce mai hakuri, dogon tunani zahra ta shiga bata taba tunanin maganganun Hajiyar makwarari gaskiya bane sai Yau wallahi duk a lokacin shirbtun tsufa ta dauki zancenta Ashe batama fada mata gaskiyar zancen ba.
A sama direct bedroom din Ammi Aunty Aisha ta nufa knocking tayi daga ciki taji Ammin na fadin "shigo mana batool kinsan bana son yawan damu da safe"
A hankali tura kofar ta shiga da sallama, ai Abulkhairi na ganin Ammi ya Zane hannusa daga na mamansa ya ruga ya rungume Ammi wadda tayi tsaye kawai tana duban Aishar Dan ba karamin mamaki ta bata ba."surprise ko Ammina?"
Ta fada tana shgewa jikin Ammin tana dariya.
"Kin kyauta kenan ki dauko jiki daga uwa duniya Amma bazaki fada ba ko Addu'a ayi muku sai dai ba ganku ba zato ba tsammani".
" Afuwan my Ammi nima bansan da tafiyar ba sai shekaran jiya waccan, kinsa dan gidanki baya jira".
"Ina kika ganshi ko kuma daman yana tare dake kika ki fada? Ina kuma Afnan din take?".
" suna master parlour da bakuwa mukazo fa".
"Bakuwa kuma?".
" Eh shigowa nayi na fada miki, to sannunku da hanya muje kasan a Samar muku abun break fast".
Suka nufo kasan takun takalmansu das das ya saka zahra dago kanta daga wasan da take yiwa Afnan tana bulbula dariya, caraf suka hada ido da Ammi nan da nan taji gabanta ya fadi, itama Ammi wani shock ta shiga babu ko tantama wannan fuskar take gani tare da Hussein dinta a mafarki yau gata a zahiri, tayi mafarkin yarinyar nan yafi sau shurin masaki me hakan ke nufi kenan.
Suna shigowa kamshin Ammin ya hade parlourn.
Zahra ba tayi tunanin haka zataga Ammin ba, babu Wanda zece ita ta haifi su Aunty Aisha sai dai ace yayarsu ce, 'yar gayu ce ta ajin karshe ga jindadin daya hana shekarunta nuna Kansu,a hankali take takowa idanunta na kan zahra wadda taji wata irin kunya ta rufeta, gurin da suke zaune Ammin ta karasa tana fadin.
"Sannunku da hanya, a kunya ce zahra ta bude bakinta tace.
" yauwa Ammy, ina kwana"..
"Lafiya kalau ya gajiyar hanya?".
Ta fada tana mika hannu zata dauki Afnan, makalewa tayi a jikin zahra alamar bazata zo ba.
Gaba Ammin tayi ta zauna tana fadin huta roro waken gizo yaqi 'ya'ya".
Aunty Aisha ce dubi Ammi tana fadin.
" Ammi ga zahra nan 'yar Amanar Hussein diyar mai gidansa ce bata da lafiya aka kaita India ganin likita shine yace na taho da ita Nigeria kafin yazo su 'yan jihar bauchi ne katagum local government sunanta Fateemah zahra".
Dan gyara zama Ammin tayi tana kara kallon zahrar from head to toe, haka nan taji wani Abu yana mata kai kawo a kasan zuciyarta.
"Sannu fateemah ya jikin naki?".
Kanta na kasa bata yarda ta dago ba ta amsa.
" Da sauki Sosai".
"Masha Allah, Hasana rakata sama dakin fake opposite da bedroom din ki bude Mata tayi wanka kafin a hada muku breakfast".
" To Ammi bari muje,ko kuma muje can gurina saita zauna tunda duk cikin part din nan ne".
Kaita girgiza "kaita sama inda sauran 'yan uwanta yara suka can gurinki ba zataji fadi ba nan kuwa gasu Batool nan kuma ba kince bata jin dadi ba sai saida babba a kusa maza kuje lokaci yana tafiya gara taci abinci ta kwanta ta huta tunda ba irin ujilarku ta iya ba".
A kunya ce zahra ta mike tana sabe da Afnan.
Saida suka bacewa ganin Ammi sannan ta dauke idonta daga kallon zahra.
" ya rabb kai kasan abinda ke boye da make nuna min yarinyar nan tare da Dana sauran sirrin kuma bani da masaniyarsa, ubangiji ka tsareni jin abinda ze zamar min tashin hankali".
Ya fada a cikin murya mai rauni.
Suna shiga dakin Aunty Aishat din tace "wow! Lallai matarmu you are special ai bansan haka Ammi ta hada wannan bedroom din ba, bari na sauka da wannan 'yar taki makale matar kawai"
Ta dauko ta tana kuka ta fice da ita, tana jin Zahra na magiyar ta dawo da ita tayi mata wanka Amma ta wuce kawai.
Lokacin da Aishat din ta sauko bata samu Ammi da Abulkhairi ba itama wata hanya ta nufa tana dan jijjiga Afnan.