← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 47

Sashe 26

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

MAMAN FATEEMAH.

Page 65

---------- Wayar hannun Hajiyar makwararin Rukayya ta karbe tana fadin.
"Dan Allah ki daina fadin wata maganar ba girman ki bane".
"To uwata saiki hanani na saita yarinya, ai gobe in Sha Allah Mahfuz ze dangana Dani Azare, yo duk abinda aka yiwa matar Mahmud ai bazamu iya biyansa abinda yayi Mana ba, Banda rashin lissafi irin naki Rakiya ke kome nace zanyiwa iyalin yaron Nan ai naki idone,kina zaune ya daukeni ya kaini wata uwa duniya aka gyara min ido da yanzu kina Nan kina min jagora ko bakya so kuwa. Tashi ki kimtsa ni ki rakani kurmi na Sami abinda bani dashi, muje agadasawa a Sami kilishi da dambun nama na tsaraba mu shiga madatai a samo gireba da su bakilawa to kinji"
Ta yunkura ta tashi Tana daukar sauran kununta, ita dai Rukayya bakinta mutuwa yayi da kalaman Hajiya, tunda ta furta tafiyar nan Allah ne kadai ze kawo abinda ze hanata zuwa Amma badai Dan mutum ba, tun su Sameer na secondary tasu tazo Daya da mahmud tun Batasan Allah ze daga shi haka ba.

A nutse Amatullah ke driving dinsu, taso ta wuce gida saboda ta gaji sosai Amma jin zahra na garin Kuma babu nisa da gidan yayar mamanta da take zaune a hannunta sai kawai tayi waya ta fada Mata zasuje unguwa.
Tunda suka shigo layin Amatu ke Kakabin gidan tana fadin.
"Kambala'i wannan Kuma waye yayi one in town din Nan? lallai Aunty Safiya unguwar taku ta masu ido da kwalli ce".
Murmushi tayi mata tana kokarin Kiran waya.
"Mun shigo ki turo a shiga damu".
Dan saurare tayi kafin tace.
"Ok muna jira".
Ta sauke wayar daga kunnenta.
"Kika ce menene?".
"Cewa nayi unguwar taku ta Zama ta masu Ido da kwalli".
"Bakiji ranar nan muna maganar layin Dan America ba? To ai gidan ne ake cewa gidan dan America".
Labarin yanda gidan ya Sami suna ta Bata.
Dai dai suna zuwa kofar katafaren gate din gidan.
"Dan tsaya a Nan mu jira muga ta Ina zata bullo Mai kaimu gidan".
Amma ita Safiyar ta hakikance matukar da gaske MAHMUD DANGEN ne da gaske mijin Zahra to babu ko tantamar wannan gidansa ne.
Saka aya a tunaninta da bude Karamar kofar gate din ya Zama lokaci Daya.
Zilai Mai aikin gidansu zahra Amatu ta gani ta fito, zaro Ido tayi tana kallon Aunty Safiya.
Gyada Mata Kai tayi kawai, sannan ta bude kofar ta fito.
Gaisawa sukayi da Aunty zilan, sannan tace Mata.
"Ko kune Bakin Uwar dakina Zahra".
"Eh mune".
Aunty zilan juyawa tayi da sauri ta koma ta fadawa zayyan zahra tayi Baki.
Jim yayi Yana kallonta kafin ya samu zarafin fadin.
"Yallabai fa ya kafa dokar kada nabar kowa ya shigo gidan nan, Amma Bari na fada Masa duk da nasan ba wadanda yake nufi bane.

Tana tsaye ya Kira Mahmud cikin sa'a ya sameshi, tun kafin ya fada masa wani Abu yace masa.
"I sw everything, just open the door".
Kawai ya katse Kiran Dan yana bibiyar gidan ne tun lokacin da yaga ta saka ayi wani girkin, Dan har a kitchen Saida aka saka CCTV.
Gate din zayyan ya bude musu suka shigo, parking lot Amatu ta aje motar suka fito zilai tayi musu jagaba.
Amatu sai raba Ido take Dan wallahi gidan ya tafi da imaninta ba kadan ba.
Suna shiga zahra tayo wani tsalle tana fadin
.
*Wayyo Allah oyoyo! oyoyo!! Sannu da zuwan ku Amatu, Aunty safiya nagode da Kika kawo min Amah wallahi Daman Ina nemanta.
Dan ja Baya Amatun rayi tana fadin.
"Ni ba gurinki nazo ba Aunty safiya na rako".
Hannunta zahra ta riko tana fadin.
"Haba my bestie kiyi hakuri Dan Allah na tuba kowane laifi nayj kada a tona"..
. dariya sukayi su duka, Ammatu dai 'yar kauye ta zama Dan Saida ta tada Kai taga yanda saman dakin yake kamar sararin samaniya Dan harda taurari da wata.
Dauko wancan kawo wannan zahra da Aunty suka shiga yi, sai murna zahra keyi na ganinsu, sunci sun Sha sannan suka Dora da hira har aka Kira sallar magariba hirar yaushe gamo akeyi, cikin hirar ne Zahra ke fadin "Wai da gaske kinsan Mahmud?"
Zama ta gyara tana fadin.
"Wallahi ba karya har gidansu na sani sai dai shi nasan be sanni ba". Daga Nan ta tsaya itama Zahra Bata zafafa ba taja bakinta tayi shiru.
Dakin kusa dana Aunty zilai zahra ta kaisu sukayi alwala, har Amatu zata Fara sallah ta tsaya ta dubi zahra.
"Ya Naga ke Baki tashi kinyo alwalar ba".
"To sa'i'dawa Ina ruwanki".
Gurin zahra Amatun dawo ta zauna a gefen gadon in da zahra ke zaune.
"Zahra Wai ya haka, ko dai planning kikeyi ne? Amma ace har yanzu babu wani labari, Ni da naganki kinyi wani sirrin kyau nayi zaton ko an Mana ajiya ne? Kuma kice Wai bakya sallah".
Dariya zahra tayi tana Fadin.
"Cikin lafiya? Ai ni ban isa haihuwa ba".
Wata malalaciyar dariya Amatullah tayi.
"Kice min 'yar yaye aka kawo masa, Wai Ina yallaban? Ko yana ciki kin Hana shi fita Dan Naga yanda Kika cika din Nan nasan baya Wasa gurin zagaya gonarsa tunda ga yabanya Nan tayi kyau da gani ana samun ban Ruwa akai akai".
Ta fada tana Kara wata dariyar.

"Wallahi Amah ki daina wannan dabi'ar Baki da magana saita wannan sabgar Kinga fita ta, Ni idona da sauran kunya a cikinsa Banda tsabar jaraba a gaban Aunty safiyar kike fadar irin wanna magana, Dan tsabar gulma da kinibibi kinyi alwala Amma Kika zauna Zaki Fara zancen da ze karya Miki ita, wallahi mijinki yaga ta Kansa irin ku ne maza suke guduwa daga gida saboda halinku".
Tana Gama fada ta Mike ta fice, wayar ta aje a Kan gadon.
Daukan wayar Amatullah tayi tana juyawa, ba karamin mamaki tayi ba da ganin wayar dake hannun Zahra.
"Wai ba zakiyi sallar ba kema Naga da alama ma kin Manta zakiyi sallar in dai lamarin gidan Nan ne bakiga kamai ba, I'm telling you in dai 'yan wannan family din ne, kinsan Allah duk wannan Wasa ne ko ita kanta Mai gayya Mai aikin Batasan wa take Aure ba, kin manta na fada Miki indai shine baze iya rayuwa da matarsa a wancen gidan ba?".
Kai Amatullah ta gyada alamar haka ne, Bata iya tofa wata maganar ba saboda shigowar zahra.
"Au bakiyi sallar ba kenan? Gaskiya kina Wasa da sallah".
"Kema dai Kya fada Mata, gashi na baro baby na Dan ma tana cin Abinci shi yasa Honey Bai takura min da Kira ba, suna cikin gari duka gidan Baba Dan lawan".
Tashi Amatullah tayi ta tayar da sallah.

Basu suka bar gidan ba sai bayan insha'i Shima Saida mijin Aunty safiyar ya Kira Dan bayan sunyi sallar babin karatu Aunty safiyar ta budewa zahrar Dan idan ta Fadi wani abun rufe Ido zahrar takeyi Amah na Mata tsinyar Wai muna furcine idan suka shige other room wata Kila ita ke Jan sitiyarin motar ai tasan ba'a banza ba tayi irin wannan cikowar tasan ta gane garin.
Sai a Nan Zahrar ke fada musu mahmud din ma baya kasar Yana India an Kai malaminsu Asibiti ya samu matsala a bayansa. Sun jajanta sosai, mayuka da turaruka Zahra ta basu, Aunty safiyar tayi mata Alkawarin kawo Mata wasu kayan Mata dasu tureren mara Mai fitar da oga daga hayyacinsa duk iya yanda ya Kai ga kame bakinsa, Amma Bata fada Mata hakan ba tasan halin kayanta sai taki amfani dashi.
Har gurin mota zahra da Aunty zilai suka rakosu, bayqn sun tafi ciki Zahra ta wuce wanka takeso Dan ki take kamar ya Bata Mata jiki.
Basu Dade suna Hira ba Zahra taga Aunty zilai tana hamma sai tace Mata taje ta kwanta kawai tasan har yanzu da sauran ramuwar barcin a idonta.

*********
Chapter 26 · 0% Book details