← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 47

Sashe 15

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

___ Rungume juna sukayi sosai, kuka ya saka Masa kamar karamin yaro da gani ba karamin missing dinsa yayi ba , Shima Mahmud Jin wani Abu yake yi a zuciyarsa badan namijin duniya bane da Babu abinda ze hana shi zubda hawayen shima, yayi kewar Faruq sosai saboda sunyi wata irin shaquwa dashi ta ban mamaki,duk da ba uwa daya ta haifesu ba Kuma kusan sa'anni ne Dan baifi wata hudu Mahmud ya bashi ba, Amma Yana bashi girma sosai,duk abinda yakeyi hankalinsa dari bisa dari Yana Kan musbahu Wanda yayi mutuwar tsaye shi Bai karasa gurin zahrar ba, shi kima bai dawo baya ba, me yake Shirin faruwa ne? wannan din meye dinta yasan dai tayi aure ance wani k'olo aka aura mata, to Ina auren kada dai gudowa tayi ta shigo yawon duniya?.
Ita ma zahrar ji tayi komai ya tsaya mata, har wata zufa taji tana tsatstsafo Mata a jikinta abun kamar a mafarki, gurin da su Mahmud suke ta kara kallo still suna yanda suke Saidai gaba Daya hankalinsa Yana gurinsu fuskarsa ba annuri ko misqala zarratin kamar dade duniya be taba dariya ba, sadda Kai zahra tayi dan ji tayi wani irin tsoronsa na shigarta tuna karonsu tayi wanda ya kusan cinye mata lebe, kasa tayi da kanta jiran taji ya zata kaya.
Bayansa ya Mahmud ya ringa Dan bubbugawa da tafin hannunsa Yana fadin.
"Haba Faruq meye na kuka da girmanka da komai Kai ba mace ba, ka nutsu ka share wannan hawayen, akwai mace fa a kusa damu tana kallonka, wallahi wata Rana sai tayi maka gorin ragon maza"
Ya fada Yana sakinsa da sauri yama duban masu rike da kayan daya saya a hannu "sorry na barku da Kaya kuyi hakuri Dan Allah mu karasa ku saka a mota"
Yayi gaba yana yiwa Mushahu wani shegen kallo, Faruq na rike dashi ram Kamar Yana gudun ya bace Masa.
Back seat Faruq ya bude suka zuba kayan,Faruq din ne ya curo kudin da baisan yawansu ba ya Mika musu sukayi godiya suka wuce bakin aikinsu.
Jikin motar Mahmud ya tsaya Yana facing din musbahu da fuskar shanu.
"Dan Allah Ya Mahmud kana Ina ne duk tsawon wannan lokacin? Kuma wacece wannan da kuke tare?"
Fuska Babu annuri Kona sisin kwabo ya Maida dubansa Kan Faruq din "Idan ka Gama abinda kazoyi ka sameni a Bawo road komai dare Ina jiranka". Ganin yanda mahmud ya daure fuska yasa yaja bakinsa yayi shiru be kara tambayarsa komai ba.
"Ok. Zan shigo yanzu ma in Sha Allah, Nima yau na shigo around four thirty, yanzu ma uncle mushahu na rako, dan yayar Mamee ne gashi nan,bari nayi masa magana ku gaisa be ganeka bane".
Da hanzari Mahmud ya daga masa hannu "pls Faruq no need". Ya fada yana dhugewa motar, abinda ya daurewa Faruq kai kenan, wai Ya Mahmud ne yake driving da kansa, sai yake ganin kamar an canza masa Ya Mahmud dinsa da wani.
Saida ya fice daga harabar gurin sannan Faruq ya karaso gurin Uncle dinsa yana fadar "Yanzu fa a hanya muke maganar Ya mahmud da kai ashe yana kusa damu wallahi ba wanda ya zaci yana kasar nan, abinda ya bani mamaki wannan Babyn da suke tare a sanina da Ya Mahmud baya harkar mata gaskiya, sai dai ban sani ba ko bacin rai ya saka shi yin hulda irin wannan dasu".
Faruq be ankare da shi kadai yake zubarsa ba sai da ya kai aya yaji Musbahu be tofa masa ko A ba sannan ya dan taba shi.
Firgigit yayi alamun yayi zurfi a cikin dogon tunani.
Dogon numfashi yaja yana yiwa Faruq duban tsanaki, kafin yace.
"Faruq waye wannan nake gani kamar Mahmud?".

"Shine mana baka ganeshi bane?".
Wani gumi yaji nan da nan ya rufe shi tabbas Shiya gani a cikin hotunan da Najib ya turo masa na daurin Auren zahra, ya dade yana hasaso inda yasan face din amma ya kasa tantancewa ke nan DANGE shine mijin da aka aurawa zahra a matsayin Almajirin Alaramma? take a nan yaji wata irin karaya ta mamaye masa zuciya yasan ya rasa zahra har abada, shi dinwa da ze iya ja da wannan dan tahaliki, ko manyan manajojinsa bai isa yayi takara dasu ba kafin ma a kai ga P.A dinsa.
Cikin nuna tsantsar karaya ya cewa Faruq.
"Ban gane shi ba sai bayan ya wuce, ina labarin dana baka dazu akan fasa aurena da akayi?" Kai Faruq ya gyada masa yana fadin "Na gane bana yarinar nan 'yar Azare ba?.
"Eh to ai wannan ta cikin motar itace yarinyar da nake fada maka kuma tabbas shine aka aura mata a matsayin Almajiri kolo, bari na nuna maka hotunan daurin auren, dan wani yaro nasa ya turo min hotunan na dade ina tunanin inda nasan fuskar Amma ban taba ko hasashen shine ba, tunda nasan meze kawo shi Azare harda zaman Almajiranci".
"What!!! Almajiranci kuma?
"Yes of course, bari na nuna maka pictures din ka gani". Ya fada da kyarin gwiwa duk da karfin hali kawai yakeyi hankalinsa idan yayi dubu a tashe take.
Ya ciro wayarsa daga cikin aljihun wando ya shiga gallary ya nemo hotunan, cikin sauri da zaquwa Faruq ya karbi wayar, da Sameer ya fara cin karo a hoton yana kusa da Ya Mahmud sai kuma wadanda be sansu ba, a hankali ya ringa duba hotunan tabbas Ya Mahmud ne tunda ga P.A dinsa nan wato duk tunanin da akeyi yana turai ashe yana Bauchi state saboda tsabar iya bada kafa.
Dago da kai yayi yana kallon Uncle din nasa da mamaki fal fuskarsa.
"Na gani tabbasa wlh shine, to amma ta yaya hakan ta faru? nayi mamakin auren daka fada min yayi, bafa wanda yasan inda yake ya yanke hulda da kowa fa, yanzu na gama fada maka irin badaqalar da aka sha a family din wanda yasa ya tsallake yayi tafiyarsa, uncle sorry bari na bishi hankalina baze kwanta gani nake kamar dabara yayi min ya gudu".
Kai kawai Musbahu ya iya jinjina masa, yayi hanyar ficewa da sauri, yana fita Allah ya kawo adaidaita ba kowa ya tare ya shiga saida suka fara tafiya ya fada masa Hausawa Bawo road.
Chapter 15 · 0% Book details