← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 47

Sashe 37

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kafin minti arba'in an hadawa su Aishat breakfast mai rai da lafiya, zahra tana fitowa daga wanka tayi tsaye a gaban mirror tana kallon kanta yanda tayi wani irin kyau na ban mamaki wato Inda ake gyaran jiki anayi dan tamkar anyi mata wankan inji,lotion din data gani ta Shafa tunda nata da take shafawa yana can cikin kayansu ba'a shigo dasu ba saida ta gama shafawa tayi turus Ashe bata da kayan sakawa kuma gashi towel din jikinta ma karami ne kusan Rabin cinyoyinta duk a waje suke, gefen gado ta koma ta zauna ita dai bazata iya mayar da kayan data cire ba, dan kwanciya tayi a jikin pillow dan tunda tayi wanka wata irin kasala ta saukar mata ba, tayi minti biyu ba barci yayi awon gaba da ita.
Jin shirun zahrar yayi yawa yasa Ammi tacewa Aishat ta bita ta kirata ko nauyin saukowa takeji tunda taga yarinyar akwaita da kunya.
Sau biyu tana knocking Amma shiru, kamar ba mutum a dakin a hankali ta murda handle din ta tura kofar ganinta tayi tana barci,komawa tayi a hankali dan bazata so ta gashi taga ta ganta a haka ba, haba dole bros ya rikice musu Ashe shi yasan sirrin kayansa Ashe a fuska wasa ne, tasan Allah ne yayi mass tukuicin kazafin da akayi masa ya bashi irin wannan yarinyar.
Sai data fara gangarowa ta tuna Ashe bata da kayan sakawa a tare da ita.
"Ya salam! Wallahi shaf ta manta tunda su basa dauko kayan sakawa suna dasu a nan.

******

Saida Mahmud yayi barcinsa mai isarsa ya tashi, sau uku Hajiya Inna tana zuwa ta buga masa daki tana jinsa a rufe, wanka yayi ya fito cikin yadin filtex mai laushi fari tas, a parlour ya samu Hajiyar da Aminiyarta Innoni suna hira, kusa da Hajiya Innar ya zauna yana gaishe da innonin, kama haba tayi.
" kai kuma yaushe ka dawo garin namu?".
Tabe baki Inna tayi "kin gashi nan saida malamai suka gama karbar nasu rabon ya mula ya Mile ya dauko jiki sinkin fakiti ya dawo, yazo kuma ya zaune min yaki ko leka kofar gidan nan, kofa gidan iyayen yaki zuwa ni naga ta kaina kasan da irin wannan ranar amma ka tsallake kayi naka guri sai yanzu zaka zo kana daddofar na kaika gidan".
Wata dariyar da bai shirya ba ta kubce masa.
" Amma wallahi matar nan kin gama dani ni zaki cewa ina kamun kafa fake ki kaini gida,ni kadai na fito ni kadai zan koma kuma kinyi da dan halak idan na fice sai kin shekara baki sakani a idanunki ba".
Ya mike ya nufi kofa, nan da nan Hajiya inna ta rude.
"Idan ka bawa Annabi daraja ka dawo wallahi wasa nake maka ga abincinka can kazo kaci".
Ya tsaya Amma bai juyo ba.
"A aje min idan na dawo zanci lokacin magariba ya karato masallaci zani".
Yana gama fada ya bude kofa ya fice.
" miskili kawai idan ba haka nayi masa ba ko gidan baze leka yau ba duk kuwa yanda yake da kawa zucin uwa".
"Ai mutumin naki sai ke".
Saida ya gaisa da masu gadi sannan ya shiga motar da yazo a ciki ya nufi unguwarsu tunda babu nisa daga unguwar su Hajiyar, yana shiga ana kokarin tayar da sallah da sauri ya shiga cikin masallacin gidan nasu tunda da alwalarsa.
Sahun bayan su Abbie dinsa yayi sallah da aka idar masu fita suka fita shi daman a dabi'arsu yawanci basa fita sai sunyi insha'i zirillahi yaci gaba dayi Abbie din bai juyo ba shima bai matsa ba sai Babban yayansu Ibrahim da yake daga jikin ginin masallacin ta kudu yake mamakin yaushe Mahmud din ya dawo kuma uncle saminu ya dawo dazu yace Mahmud ya gudu daga India, uncle mustapha ya bazu nemansa to ga Mahmud kuma a sokoto ga uncle mustapha ya sauka a abuja ze biyo jirgin karfe bakwai na dare zuwa sokoto to me kenan hakan ke nufi? Shifa daman ya dade yana zargin uncle saminu da wasu abubuwa marasa kyau a tsakaninsu.
Ana idar da insha'i Mahmud ya tashi ya fice kafin Abbie din su ya tashi, hannu kawai ya dagawa securities din ya wucesu suna faman murna dan sunsan kakarsu ta yanke saka mai yiwa dawa ruwa bare gashi a karkara,koda bayanan sakonsa yana iskesu to bare gashi ya dawo.
Ya dan jima a parking lot na gurin Ammi yana Karewa harabar gidan kallo ko ina haske ne tar ga wata iska mai dadi da take busowa cikin motar tare da kamshin furanni mabanbanta, abubuwan da suka faru suka dunga dawo masa daki-daki lumshe idanu yayi baiyi aune ba yaji ruwan hawaye suna bin kumatunsa abinda baiyi ba kenan duk badaqalar da aka sha a gidan nan a lokacin, kansa ya kifa jikin sitiyarin motar baiji alamun tafiya ko wani Abu sai dai jin hannun mutum yayi a bayansa bai dago ba, bubbuga kafadarsa yaji an fara kafin ya tsinkayi muryar Abbie dinsa yana fadin.
"Haba! namiji baya kuka tunda ka iya jure kwaramniyar baya baka nuna rauni ba yanzu lokacin fuskantar gaba ne taso mu shiga ciki kada kannanka suga kana kuka, su raina min kai".
Da Saudi ya dago jin furucin da bai zata ba daga bakin Abbie idan yayi la'akari da lokacin da guguwar abun ta tashi tsine masa ne kawai baiyi ba Amma yayi masa wata irin tujara ta Ala tsine uwar mai karya.
Jikinsa ya fada yana fadin.
" wallahi Abbie ban aikata ba! Ban taba zina ba, ka bani Qur'ani zan rantse da Wanda ya halicceni idan na taba zina a rayuwata Allah yayi min abinda yaso na azaba, ka yarda dani ka fadawa Ammi banyi ba sharri ne akayi min na fada Amma Baku yarda ba...kum..."
Sai jikinsa ya langabe ya saki.
Da sauri Ya Ibrahim dake tsaye a gefe Wanda shima hawayen yakeyi ya zaburo yana fadin .
"Suma yayi Abbie bari na samo ruwa"
Ya tafi da gudu ya haura steps din part din Ammi, suna zaune ya bude kofar afujajun baiko kalli su Ammi ba da saura yaran yayi kitchen da gudu ya dauko ruwan sanyi da sauri Ammi da Aishat da Batool suka rufa masa baya Ammi na tambayarsa menene? Bai ko juyo ba yayi gaba,suma gurin daya nufa suka nufa turus sukayi ganin Abbie a tsaye rungume da mutum Ya Ibrahim yana bulbula masa ruwan sanyi.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da shashsheka abinya yake fada yaci gaba da fada.
Ka fadawa Ammi ni ba nazinaci bane ban aikata ba".
"Pls kayi shiru mana ta sani ka kwantar da hankalinka bama zarginka kaga Amminka tana jinka fa".
Da sauri ya juyo sai kuma jiri ya kwashe shi ze zubar Ya Ibrahim yayi saurin rike shi suna faman jera masa sannu, juyawa Ammi tayi idanunta fal hawayen tausayin dan nata kenan duk tsawon lokacin nan yana fama da wannan damuwar wadda sai yau ya fasata gashi zata janyo masa matsala a lafiyarsa.
" Allah ka biwa yaron nan haqqinsa".
"Allahumma Amin".
Taji su Batool sun fada sai lokacin tasan a fili tayi addu'ar.
Su zahra na tsaye tana dauke da Afnan tun shigowar Wanda ya dauki ruwa ya fita su Ammy suka bishi taji gabanta yayi wata irin faduwa, ta mike tsaye ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai kuma taga an shigo da Mahmud din a rirrike yana layi kamar Wanda ya bugu da kayan maye.
Ai bata San yanda akayi ba ta dira a gabansa jikinta yana wata irin tsuma cikin rufewar idanu da manta a ina ma take ne ta fara fadar
" Na shiga uku meya sameka meu amor...? Me akayi maka fada min dan Allah..."
Hannu Aunty Aishat da Dora a bakinta data bude tana fadin.
" kai? Wonderful...! the game is over".
[23/02, 11:59 am] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI *

AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateemah.

Page 76.

.............. Aunty Aishat ce tayi sauri tazo gurin zahrar saboda kowa a gurin wutarsa daukewa tayi barema Abbie da Ya Ibrahim da Basu da masaniyar da wata bakuwar fuska a gidan, itama zahrar sai data fada ta dawo Cikin hayyacinta, wata irin kunya ce ta rufeta taji kamar kasa ta tsage ta shige Dan kunya, me tayi kenan shike Nan tayi abun kunyar da zata Dade Bata hada Ido da Amm bai wallahi.
Kan kujerar dake kusa dasu su aje Mahmud Wanda tun dirowar Zahra gabansa yaji wata irin Rahama ta saukar Masa a zuciyarsa badan a gaban iyayensa bane saiya Bata hot kisses na nuna godiyar nauyin data sauke Masa Cikin kankanin lokaci ta isar da sakon Daya Dade Yana tunanin ta Ina ze bullo musu Sai gashi in some minutes tayi musu aikin.
Chapter 37 · 0% Book details