← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 47

Sashe 32

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

........... Cikin kankanin lokaci mahmud yaji ya Dan samu nutsuwar Daya rasa, yarinya karama ta saka shi sakin layi a gaban mutane, ita dai Aishat sai jijjiga Afnan takeyi wadda har lokacin take 'yar mita, tashi Mahmud yayi da nufin barin gurin, Ya Abbas ne ya riko Masa hannu Yana girgiza masa Kai.
"Dawo magana zamuyi ta fashimta, baiyi gaddama ba.
"Kana ji yanzu ka Bata sarari ta huta ta Kuma Huce daga fushin da tayi da kai, idan so Samu ne ka koma gidanka ka kame kanka, kada ka Bari ta Kara ganinka Nan kusa har sai an Kai wani limit da zata nemeka ruwa a jallo ta rasa yanda ko kun hadu babu saura fishi sai dokin ganinka dole ba Zama very strong a fannin soyayya Kaine namiji kada ka yarda ta gane itace rauninka, sannan dole ka koyi takatsantsan kasan inda na dosa idan ba haka ba za"ayi amfani da wannan damar a cutar maka da ita Koda ta furucin Baki ne".
Shiru mahmud yayi Yana saurarensa wato shi kansa zaman takewar auren sai an shirya mata, Dan rausayar da Kai yayai yana fad'in.
"Anyway shike nan,Amma da so nake ta yarda muje asibiti su dubata tukunna sai na wuce din".
Wani kallon me yake damunka Ya Abbas yayi Masa.
"For God sake! Ashe bazaka Zama Mai karfin ba kenan? Tunda nace ka kame kanka ai sai kayi yanda nace ko, tashi mu fita ja rakani na dubo patient din namu ma ida discussion din a hanya tunda Naga alama ka rifta da yawa".
Ya fada Yana Masa dariya, sumar kansa ya shafa shima Yana murmushi.
Bayan fitarsu Aishar Goya Afnan tayi so take tayi barci, Bata Kara bi takan Zahra ba ta shige kitchen ta Dora ruwa ta dauko kaza ta Fara gyarawa ta Dora a wuta ta debo fresh fruits ta wanke ta Fara hada fruits salad ta saka a fridge tayi lemon kankana da Madara pepper chicken tayi da chicken rice sai coslow data hada ta dafa ruwan tea Mai hadin spices masu Dadi na dafa tea kafin magariba ta Gama komai, Babban tray ta hadawa zahra kayan bude Baki ta aje a gefe sannan ta ringa fita da nasu zuwa dinning tana jerawa Saida ta Gama komai ta dauki na zahra lokacin har duhun magariba yayi, knocking Daya tayi Zahra ta bude Mata ta matsa gefe tana fad'in.
"Sannu Aunty da aiki Aunty".
Ta fada tana karbar kayan Amma taki yarda su hada Ido.
"Zanje nayi sallah idan na Gama zamu zauna dake Ina so mu tattauna wasu abubuwa".
Aishat ta fada tana juyawa.
"To Aunty zanzo basai kin dawo ba".
Dan dakatawa tayi da tafiya ta waiwayo.
"Kiyi zamanki ai Amare 'yan lalashi ne, ni zanzo on behalf of my beloved brother".
Ta fada tana dariya, itama zahra murmusawa tayi.

******Daga gida direct Asibiti su Mahmud suka nufa, sun samu Habib da Abubakar, Ya Abbas yayi mamakin ganin Abubakar a gurin sosai Amma baice komai ba kenan da wadanda mahmud yayi hijirar dasu.
Lokacin Baba malam Yana zaune suna Hira, har gabansa su mahmud suka karasa suka gaishe shi da Kara suba shi, sannan su Habib suka gaishe dasu mahmud, Ya Abbas ne ya kalli Abubakar Yana fadar.
"Wato har Kai gurin kufe Mana gaskiya ko? Kana ji ana ta Fadi tashin nemansa kayi fumfurus kana kallon kowa daga karshe ma akace ka canza gurin aikine".
Sadda Kai yayi yana Dan sosa gefen wuyansa, gyaran murya Baba malam yayi Dan duk da bayanin matsayin Ya Abbas da mahmud yake basa baisa ya dauke hankalinsa daga maganar da Abbas din fada ba.
Jin gyaran muryar Malam yasa suka juyo gaba Daya suna kallonsa.
"Ayi Masa Afuwa shima Mai bin umarni ne,sai yanda akayi dashi kada aga laifinsa amanar kenan da baya da Amana baze yarda dashi irin haka ba. Allah yayi albarka ya kiyaye gaba, ai karfin addu'a ne yasa komai ya Zama tarihi naji dadin ganinka sosai Malam Abbas Dan Allah kayi min aikin Dana kasa ka maida min Dana gida tare da iyalinsa ka bawa mahaifinku hakurin karambanin da mukayi musu wallahi nagarta muka duba ba komai ba tunda Bamu San gaibu ba, in Sha Allah idan lafiya ta Samu Ina Nan zuwa sokoton da kaina".
Waje su Habib suka fice, ya Zama daga Malam din sai su Ya Abbas.
"Babu komai Malam Allah ya baka lafiya, muke da godiya ya fada min duk dawainiya da kayi dashi tunda kuka tsince shi har kawo yanzu ai kaima ubane ka Isa kayi yanda kaga dama dashi, Allah ya Kara lafiya da sutura yasa kaffara akeyi in Sha Allah amanarka Zan idata, ai mu bamu da Bakin godiya sai dai ubangiji ne ze biyaka".
Sun Jima suna tattaunawa anan Malam yake farawa Abbas yanda kayiwa mahmud makaru abinda Bai taba fada Masa ba sai yanzu yakeji, har wasu hawayen gefen Ido Mahmud yaji sun taro Ashe haka akaso a kassara Masa rayuwa Allah yayi Masa gada da Rahama ya kawo Habib ya gashi a gurin da yake a yashe a kasa.
Anan sukayi magariba sukayi insha'i sannan sukayiwa Baba malam sallama, mahmud ne yace suje su duba jikin Alhajin su Aunty surayyar uncle Mustaphan Shima Yana nan.
Shima sun samu 'ya'yansa maza biyu sunzo duba jikin nasa, sun gaisa tare da jajanta musu, shima Alhajin jikin da sauki sosai Dan har Yana takawa shima da karfe.
Gida suka koma mahmud yayi dinner tare dasu, haka Nan yayi ta maza bai nemi zahra ba Suma babu Wanda yayi maganar ta har suka gama, Mahmud Bai wani zauna ya shiga dakin da ya mayar nasa tun ba yanzu ba ya dauko laptop din da wayoyinsa ya fito.
"Ka Bari na saukeka Nima Ina son fita ne".
Ya Abbas ya fada.
"No, ka barshi kawai nayi waya da Mr salahuddeen Yana kusa da isowa, kawai dai Alfarma za'ayi min twins zasu shiga Nigeria a tsakanin kwanakin nan harna Fara musu processing na visa harda yaran duka".
"Ba damuwa Nima Ina son suje Nigeria din to saboda makarantar Abulkhairi ne, Amma yanzu dole suje tunda ta Kama amma naji kana fadar kana nemar musu visa Kai kana Nan kenan?".
Kai ya girgiza Yana fadar "A'a akwai dalilin raba tafiyar ne jikina Yana bani wani Abu da bansan ko menene ba".
"To Allah ya rufa asiri, Zan fadawa sweetie ka wuce tana can gurin 'yar daru ita da dare take tata rigimar amma da Rana lafiya kalau za'a wuni da ita".
Dan murmushi Mahmud yayi Yana ayyana Wai babyn su ce da zahra suna tarairayarta.
Yana fitowa harabar gidan motar sayyid tana shigowa, dai dai gurin Mahmud ya tsaya ya kashe motar ya fito da sauri ya rungime Mahmud Yana fad'in .

"Ina ka shiga a duniyar nan ka barmu da tashin hankali? Munyi nema har mun godewa Allah kasan Umma cewa tayi a saka nemanka a jaridu da mujallu da kafafen sada zumunta na zamani,Su uncle Mustaphan ne suka Hana sukace abun ze zama tonon sillil Wanda Bai sani bama ze sani".
Dan zare shi daga jikinsa mahmud din yayi Yana fad'in .
"Ai gashi Nan dawo sayyid ya karatu ace ka koma PhD ko?"
"Wallahi kuwa".
"To Masha Allah. Allah ya taimaka, Nima Zan wuce ne matar abokina na kawowa Aishat su zauna a Nan asibiti sukazo zataga likita".
Ya mika Masa hannu yayi gaba, sayyid Yana da kirki amma fa gurin lamarin Mata sai a hankali, ko baya Zina ta zahiri akwai 'yan tabe -tabe.
Yana fita ya turawa Aishat text message a waya.
Amma fa karfin Hali kawai yakeyi Sam zuciyarsa Bata nutsu ya tafi yabar zahra da wannan Karen farautar a gidan ba, amma dole ya kauda Kansa yayi kawaici da Kara kada Ya Abbas yaga Bai dauki maganarsa ba.
Koda ya koma su Habib suna gida Suma sun baro asibitin, coffee ya bukac Mr Ajey ya kawo Masa ta wuce ciki Saida yayi wanka ya bude laptop dinsa Yana aiki Yana sipping din coffeen, ya Kai kusan biyun dare Yana Abu Daya Saida ya tabbatar da komai ya dai daita sannan ya kwanta zuciyarsa da gangar jikinsa suna mararinta, filo ya rungime a haka barci yayi awon gaba dashi.
Bayan sun sallar Asuba barci mahmud ya koma knocking din da ake a kofar bedroom dinsa ya tashe shi daga barcin da yake Mai Dadi Wanda ya saka shi nishadi.
Umarnin budewa ya bada Yana daga Cikin blanket dinsa.
Mr sunny ne Mai yin share share da goge goge.
Chapter 32 · 0% Book details