← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 47

Sashe 33

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

" Good morning Sir"
Ya fada Cikin ladabi daga Bakin kofa sannan ya Dora da fadin.
"Akwai Baki daga Nigeria".
Wani smile yayi Yana tashi zaune yasan za'a Rina sai yanzu ya gane hikimar ya Abbas na cewa ya dawo nan shi kansa baze so zahra taga dabin da za'ayi ba".
"Kaje ayi musu duk abinda ya kamata, Mr Ajey ya Basu abinci kafin na fito".
Toilet ya shige yayi suk abinda zeyi sannan ya fito Yana tsane sumar kansa da Karamin towel a nutse ya Gama shirinsa ya fito a Mahmud dinsa, ya riko wayoyinsa hannu ya nufo main parlour.
Da uncle Mustaphan ya Fara yin tozali kafin ya sauke idanunsa a Kan uncle saminu, nan da nan ya hade girar sama data kasa tamkar yaki ya rigshi kofar gari.
A ciki ya gaishe su duk da shafi ce ta shafi uncle Mustapha sai yayi musu kudin goro, neman guri yayi ya zauna Bai Kara cewa komai ba, uncle saminu ne yazo iya wuya Dan ba haka yayi zaton zega Mahmud ba l,Dan an Bashi assurance na ya Gama lalacewa,dan a yanda a kayi Masa aikin rigar sawa ma sai tafi karfinsa, bare wani arzikinsa sai dai komai ya lalace masa, sai ya Zama abinda zeci ma saiya fi karfinsa, sai Kuma yaga sabanin haka Dan yanda yake da kyawun gani a yanzu ko kafin faruwar matsalar da suka Zama asasin fatuwarta Bai Kai haka kyaun gani ba.
A zuciye ya taso yana fad'in.
"Kai din banza har yaushe kayi arzikin da zamu tako har inda kake ka wulakantamu eyeh? Ka maida mu 'yan iska Wanda Basu San ciwon Kansu ba ko a Nan ma halin akuyancin kake tabawa shi yasa ka makale kana gyallin goshi?'
Uncle Mustapha ne ya taso da sauri yana fadin.
"Meye haka kakeyi saminu? Daman abinda ka shirya kayi kenan? Amma kaji kunya wallahi Dan zumunka? ko abinda kuka kitsa kaida munafukarka kuka lankaya Masa sharrin da gaske Yana yinsa ai ka rufa Masa asiri ba kazo kana wannan shirmen ba Wanda Allah ya daga ya daga shi sai dai mahassada suyi kuka, dai dai gwargwado meka nema ka rasa da yawa ta taka suke nema Basu samu ba wace irin sutura ce Ubangiji baiyi Mana ba Amma ka tsaya kana yiwa dan Dan uwanka hassada saboda Allah ya daukaka shi a cikin family din kace ya auri 'yarka yace baya so to nuna kin jini na me Kuma wani ya taba auren matar daba tasa ba ka ragewa kanka wannan walahar Dan babu inda zata kaika sai fagen Dana sani, Ashe 'yar burumburum kayi min ka nuna komai ya wuce muzo mu tafi dashi gida".
Sadda Kai saminu yayi baiyi zatom Mustapha zeyi masa haka ba Dan Saida ya shirya ya taho da zummar duk abinda yayi babu Mai iya tanka Masa.
Maganar Mahmud uncle Mustapha ya tsinkayo daga bayansa.
"Ka daina Bata Bakinka uncle Wanda yayi nisa baya Jin kira,ni Mahmud ta zamar Masa kadan garen bakin tulu ya barni na Bata ruwa a karni a Kar tulu, babu abinda ya Isa yayi min tinda bashi ne ya halicceni ba Kare ya canza min kaddarata kuma har abada Bazan taba auren wannan karyar 'yar tasa ba, yaje yayi bincken wacece ita kafin ya samu bakin fadawa mutane maganar suna Zina aje asibitin tugar barau ka nemi solomon kaji sau nawa ya zubarwa da 'yar taka ciki? Ko an fada maka bamu San haka ba Dan anyi shiru an kyaleta ba' a fasa maganar a family ba idan kace karya ne yanzu na nuna maka hujjata Mai karfi, kaci gaba da abinda kake kada ka fasa Dan Allah mu Zuba sharri dai Dan aike ne kada ka rufe kofa ze dawo Komai Daren dadewa, uncle Mustapha kayi hakuri wallahil azim Bazan bika ba yanda na fito ni kadai haka Zan koma indai da wannan mutumin zamu tafi Saida na mutu ban koma ba, bani da wani Hadi dashi Wanda ze shige min gaba a dukkan lamurana.
Uncle Mustapha baiyi yunkurin Hana shi ba saboda yasan irin bakin Cikin da yaron ya kunsa a wancan lokacin.
Juyawa mahmud yayi ze fice daga parlourn, uncle Mustapha ya riko hannunsa.
"Ina zaka tafi?".
Idunu jajur ya kalli uncle din, yana girgiza masa Kai, wallahi bazan zauna dashi ba idan ka matsa min za'ayi Dana sani, yanzu babu abinda ze hanani nayi abinda banyi a wancan lokacin ba, uncle kana da daraja da qima a idanuna to ka fada masa ya fita faga sabgata idan Yana so ya tsira da Dan sauran mutumcin Daya yage Mana to ya kiyaye shiga duk abinda ya shafeni, mu hadu a Sokoto two thirty flight dina ze tashi duk abin bukata a kwai shi a nan, idan ka shiga asibiti Faisal ze rakaka gurin malamina ka duba shi anyi Masa aikin spinal cord ne"..
Ya kada ya fice abinsa.
"Yanzu irin wannan Ina ranar ta ka zubarwa da kanka qima da girma saboda sakawa Rai hassada a banza, shima ya juya ya fice daga gurin zuciyarsa babu Dadi Dan ko kadan baiga laifin yaron ba an Bata Masa fiye da kima. ya bar uncle saminu ya kasa ko kwakwjwaran motsi.
[19/02, 11:46 pm] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI*

AISHAT ISAH MUSAH.
(Maman Fateemah)

Bismillahir Rahamanir Rahim.

P. 73

........... Tunda Zahra ta farka daga barci taji Sam Bata Jin Dadi jikinta ita ba Mai zazzabi ba duk jijinta ciwo yake Mata, ta Kuma kasa fita Dan Bata son su hadu da Dan gidanta kada ya Kara Bata kunya Dan taga alama tasa tayi kaura daga idanunsa sai ya iya yi Mata abinda yafi hugging ma ga Kuma uwa uba tana Jin bala'in nauyi Ya Abbas tunda ko banza yayan mijinta ne ya wani kwakumeta ko kunya babu, agogon waya ta duba karfe Tara saura kwata na agogon kasar, tattaunawrsu da Aunty Aisha ta ringa dawo Mata tiryan-tiryan. Tasha mamakin halin da aka saka mahmud Ciki yaga masifa da tashin hankali ace kowa yayi maka naqi, kuma dadin dadawa kowa ya kasa fashimtarsa, ta yarda kamar yanda Aunty Aishat din ta fada abun an Dade ana shirya shi Saida aka Sha Kan kowa sannan aka fasa maganar, kuma tayi wani irin tasiri Banda taimakon Allah da wani labarin akeyi ba wannan ba.
Yunkurawa tayi ta tashi sai taji tana bukatar kasancewa kusa dashi ta lallashe shi, abin tausayi be kuma abunda ya fada gaskiya ne, sai yanzu ta gane gundarin me maganarsa take nufi duk da na gari dole yabi iyayensa, kawai shedan ne ya tunzura ta ta hau dokin zuciya Mai mmakon ta Zuba Ido taga yanda abun ze kasance sai ta kasa ta hau fushin fari, ai dole ma hakan ce zata kasance tunda Yana da magabatansa, idan sun amince da auren da akayi Masa laba'asa idan Basu amince ba shikenan.
Tana zuwa wannan gab'ar taji wata irin faduwar gaba, kada fa iyayensa Suki yarda da ita a matsayin mararsa.
"No!!!. In Sha Allah mutu ka raba takalmin kaza.".
Ta sauko daga gadon gara ta fita ko tayi arba dashi tayi yanda tayi ta Shawo Kan kayanta.
Wanka ta shiga shaf-shaf ta fito ta shirya ta saka rigar cotton lace marar nauyi tana baza kamshinta, bata daura dankwalin lace din ba karamin gyale ta Dan rufe gashinta dashi ta sako plat shoes ta fito zata shiga kitchen tayi musu abin break fast kada ta Zama cima zaune sai dai ayi a Bata.
Parlourn ba kowa shiru sai karar a/c kakeji kawai sai Kuma sansanyan kamshin turarukan daki tunda gidansu akazo, kitchen ta nufa Kai tsaye saboda tana da yakinin masu gidan Basu tashi ba, da sauri tayo baya ganin mutum tsaye Cikin kitchen din daga shi sai boxer short da singlet, shima Jin motsi daga bayansa ga wani scent Mai shegen Dadi ya bakunci hancinsa yasa shi juyowa babu shiri.
"Ya subhanallahi!".
Ya fada lokacin daya Dora idanunsa Kan fuskar Zahra, da wani mahaukacin sauri ta juya fit ta fice daga Cikin kitchen din, shima sayyid da sauri ya aje cup din Daya dauko ze Zuba coffee din daya dafa.
Ko duriyarta sayyid Bai gani ba sai dai kamshin da tabar Masa.
Zahra na shiga daki ta Danna Masa key tana maida numfashi.
"Waye wannan Kuma da yake da irin wannan freedom din a cikin gidan matar aure irin haka? Gaskiya wannan rayuwar da sake, dole meu amor yazo su bar shi ai da matsala sosai gidan musulmi Kuma matar gidan Matashiyar mace Mai jini a jika, shaidan ake gudu gaskiya.
Wayarta ta dauka tana neman Aunty Hassana su gaisa.

______

Mahmud yana fita kofar baya ya koma ya shiga bedroom dinsa ya dauko abokiyar tafiyarsa jakar laptop ya shiga mota sai tashin motar uncle Mustapha yaji Dan ya fita har waje baiga mahmud din ba Bai Kuma kawo Yana Cikin gidan ba.
Da sallama ya shiga dakina da aka kwantar da Baba Malam din Yana zaune shi kadai Yana lazimi ga kayan break fast Nan an kawo Masa Bai Kai ga cinsa ba.
Sallamar Baba malam ya amsa Yana fadin.
"Sannu da zuwa mahmudu, Amma yau kayi sakko, ya Naga ran naka babu Dadi lafiya dai ko?"
Chapter 33 · 0% Book details