← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 47

Sashe 39

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin abinda Abbie ya fada yasa Aunty Aishar da Batool suka nufi parlourn da Zahra ke zaune Basu tarar da ita a gurin ba sama suka nufa Batool nata kakabin abin tana faman magiyar Auntyn ta fada Mata ita ce ta hada Ya mahmud da Aunty Zahrar? Amsar Daya ce dai take fada Mata yanda ta ganta itama haka ta ganta.
Knocking biyu sukayi Zahra tace su shigo a kan sofa suka sameta ta Zuba tagumi tana aikin tunani Afnan ta karba daga kafadar Auntyn wadda tayi barci kwantar da ita Zahra tayi.
"Kuma saiki gudo Baku gaisa da Abbie ba".
Sadda Kai tayi dan ji tayi Auntyn ma kunyar hada Ido takeyi da ita.
"Zamu gaisa ne ai yanzu bazan iya zuwa ba wallahi kunya nakeji, ji nake kamar nayi tsuntsuwa na gudu".
"Kaji Aunty meye abun kunyar a ciki keda ba rungumarsa kiyayi ba "Dan kin nuna damuwa a Kan halin da yake ciki ai Kara kankarowa kanki mutunci kikayi su iyayensa, ai Dadi sukaji ko Basu fada ba irin wannan rudewa da antayo soyyaya a gabansu sun San idan aka shiga other room Kuma sai yanda Hali yayi kenan,gaskiya a gurinki zanyi degree harda masters ma akan soyyaya Naga alamar kina Dora Ya mahmud a network".
Riqe Baki Aunty Aishat tayi tana kallon Batool.
"Yaushe Kika lalace haka? Wallahi Zan sami Ammi ayi gaggawar saka Miki Rana kece Mai fadar irin wannan maganganun a gaban idanuna gara a yiwa tubkar hanci kinyi service din a gidan mijinki".
"Kai Aunty Mena fada Ina ce kece ya kamata ki zaunar dani kiyi min Karatun yanda Zan Kama mijin nawa, Amma bakiyi ba sai kuma Kice Zaki hadani da Ammi Wai ayi bikin ko service banyi ba salon laulayin ciki ya hanani yinsa cikin dadin rai".
"Allah ya shiryeki wannan yarinyar da Baki samu miji ba wallahi cewa zanyi Ammi ta fadawa Abbie ya badaki sadaka Naga alamar idan Kika Kara watanni za'a iya samun matsala gaskiya".

Dr Hashim Bai Bata lokaci ba yazo bedroom din dake kasa wanda mahmud din ya mayar dakinsa suka shiga Dr ya duba shi, ya auna B.p normal yace ya rage saka damuwa a zuciyarsa saboda kada ta shafi lafiyarsa a irin wannan shekarun, tea yasa Ammi ta hado Masa ya Sha yayi Masa Allura ya bashi magunguna Yasha sannan ya tafi.
Ba'afi minti biyar dayi Masa allurar ba ya Fara hamma zuwa minti goma yayi barci.
Karfin A/C Abbie ya rage masa sannan suka fice daga dakin.
Suna fitowa Ammi taja ta tsaya tana duban General.
"Kaga abinda naketa fada maka ko? Game da mafarkin wannan yarinyar wallahi itace zahiri ake nuna mini a Cikin mafarkina suna tare dashi".
Hannunta ya kamo suka zauna.
"Ki kwantar da hankalinki lallai Allah ya nuna Miki wani sirrine da yaso ki fara gani kafin zahiri yazo Miki, tun ranar talata Mustapha ya turo min hirarsa da malamin Daya ya rike Miki yaro lokacin da baya Cikin hayyacinsa da yanda Sukayi ta fadi tashi akan nemar Masa magani da yanda ya fada anyi Masa asirin barin garin na har abada da yanda akayi auka bashi wannan yarinyar yanzu haka dai in takaice Miki labari matatmrsa ce ta sunnan wadda marikinta yayi Mata AUREN HUCE HAUSHI, saboda itama anata samun matsaloli ne a dukkan lokacin da auernta ya tashi, shine markinta Kuma Aminin malamin ya yaba da hankalinsa ya bashi aurenta ba tare da la'akari da irin matsayinsa na bako kuma Almajiri ya bashi ita, babu irin surutun da ba'ayi Masa ba ya toshe kunnensa ana ta fadar Dan ba 'yarsa bace ya Bata marar gata. To shi malamin ne ya gamu da jarabawar matsalar Spinal cord injury shi mahmud din ya fita dashi India lokacin dashi malamin yake kokarin dawo dashi gida sai kuma ya gamu da wannan lalurar yace a bamu hakuri sunyi kuskuren yi Masa Aure Amma mu dauka haka kaddarar take a rubuce gurin Ubangiji shiya kawo aka samu matsalar da tasa mahmud ya tsallake yabar gida har hakan ta faru da ba'a samu wannan matsalar ba da ta Ina zeje Azare ya zauna har a bashi auren yarinyar? Kinga Koda matarsa ce sai dai su hadu ta wata fuskar badai wannan ba tunda Allah ya hukunta matarsa ce".
Jinjina Kai kawai Ammi keyi Tana Kara girmamawa girman Allah s.w.a idan yayi wani abun sai dai bawa ya kalla da Ido kawai.
"Na fashimta bazan ja da hukuncin Allah ba, duk yanda yayi da bawa shine daidai naji Dadi da Allah yasa Dan uwanka yazo da maganar nan bashi Hussein ya fada ba da kuma abinda ita yarinyar tayi yanzu a gaban Dan uwansa Dan haka saika tarasu kasa Mustaphan ya kunna musu suji da kunnensu bazan dauki abinda na dauka a baya ba, Kuma sabon biki za'ayi kamar yanda ake yiwa kowa a gidan Nan maganin tsegumi Dan haka da safe Zan Kira Ya I Ishaq ya bani aron Aunty Badi'a zata rakata har Azare ta yiwa mamanta bayanin sabon biki za'ayi kosu can Basu sake ba su hada jama'arsu za'a zo a dauketa kamar ko wace Amarya da dangin mijinta suke zuwa su daukota, zatafi kima da daraja a Cikin family fiye da a wayi gari ace wai yazo da Mata ai wani ma abin magana ze Zama ko Yaya kake gani? kasan tunanin mace da namji ba Daya bane".
"A maganarki babu gyara hakan yayi Amma idan har hakan za'ayi no need a ce sai kowa ya San gaskiyar maganar kawai Mustaphan yace an daura aure ne yanzu bikin za'ayi kawai Daman suna Shirin dawo dashi gida ubangidan nasa ya samu matsala Yana asibiti a India inda aka kawo labarin ganin mahmud din Ashe jiyya sukeyi a can".
"Hakan yayi Allah ya Kara sutura"
"Allahumma Amin" Abbie ya fada, muje ki bani wani Abu marar nauyi naci tunda Naga Alamar murna ta hanamu yin dinner a gidan nan, ki kawo min can part dina".
"Kaiiii Yallabai ayi min afuwa yau Daya dai Ina da bakuwa ai nayi entertaining dinta".
"Babu wannan kizo Ina jiranki ki bar musu Nan din kinsan dai zasu iya abinda zesa ki kusa nutsewa a kasa Dan kunya kuma ma ke Ina ruwanki dasu ba tare Kika gansu ba kinsa auren nasu ya dauki watannin da yinsa?".
Dan murmushi Ammin tayi.
"Ni fa Banga alamar yarinyar nan an mayar da ita mace ba gaskiya budurwa ce".
"Kamar yaya, yarinya da mijinta ki ringa fadar haka?"
Shiru tayi masa ita dai taga abinda ta gani tun ganinta da tayi dazu kafin ta sauki daga steps ta kiduri duba abinda Hajjo ta fada Mata da yake nuna yarinya budurwa ce ko tana ma'amala da maza, da niyya taje da niyyar daukar Afnan Saida ta gani sannan taji ta Samu nutsuwa.
Lokacin da Ammi ta haura saman shiru da alamar sun kwanta,Saida ta Gama duk abinda zatayi ta rufo kofarta kamar zata shiga gurin zahrar saita juya ta nufi downstairs kawai tasan idan ta shiga kinya zata Bata gara ta Bari abun ya Dan bi jiki tunnna, downstairs ta nufa tana ayyana sai ta Dan yamutsa musu lissafi ko Yaya ya ne Dan su Kara sanin darajarta itafa tana kishin mace ganin an bashi yarinyar Nan a sama saiy
Zahra ta Dade tana tunanin makomar aurenta baran barama dai tariga tayi sai Kuma yanda ta yuwu Wai Dan daudu a lahira.
"Koyaya jikin nasa?"
Ta fada a zuciyarta, ta Jima tana sakawa da kwancewa, gashi duk yanda taso ta Kira Aunty Hasana abun ya faskara haka Ammah duk network yaki bada hadin kai. Sai wurin Daya saura tayi barci, can a Cikin barcinta taji Kamar ana tabata, kwanciyarta ta gyara ba tare data bude Ido ba sai tajita a jikin mutum da wata irin zabura ta yunkura zata Mike taji an mayar da ita Baki ta bude zata zabga ihu taji carab ya hade bakinsu sai lokaci taji kanshin turarensa a hancinta, wata ajiyar zuciya ta sauke, tayi lif a jikinsa da gaske sunyi missing din juna Saida yayi Mai isarsa sannan ya dan saurara Mata ya yanye bakinsa suna maida numfashi.
"Previous kin azabtar Dani whyyy... Me nayi Miki Kika haramta min ganinki kwata-kwata? Fada min kinsan halin Dana shiga kuwa? Kikasa na kasa controlling kaina a gaban elder brother dina kin kyauta min kenan?".
Ita dai mukus tayi to me zata fada masa tace labewa tayi taji shirarsu da Aunty Aishat ko tace Masa me shirun shi yafi Alkhairi. Juyin duniyar Nan taki magana dole ya kyaleta ya koma wata shirar da ban.
"Wai dazu da rungumeni zakiyi a gaban su Ammi?".
Saka kanta tayi a kirjinsa Cikin kunya tana gigiza Masa Kai.
"Kin dauka Zan tafi na barkine ko? To muna Nan sai kin haifo Mana fine babies masu Kama dake".
Ya fada Yana Kai hannu akan cikinta Yana Dan shafawa.
"Ka Bari Dan Allah Ammi fa tana Nan ka tashi ka tafi Dan Allah kada wani ya ganka ka shigo yayi zaton wani Abu fa".
"Kwantar da hankalinki ai kin Gama Mana aikin Dana kasa yinsa a Cikin kankanin lokaci meya rage kuma? sai mu tattara mu tafi inda mukafi wayo Nima nasan nayi aure na huta da ragaita mu fuskanci rayuwa kuma, badan nayi alkawarin kawowa Ammi ke a yarinyarki ba Aida yanzu muna Shirin tarbar babyn mu ko ba haka ba?"

Wannan furucin nasa shi ya ankarar da ita akwai fa sauran Rina a kaba, Nan da Nan wani tsoro ya kamata Nan ne fa karshen maganar, a Nan ne me afkuwa fa zata afku,tunda gata a sokoto har dakin mahaifiyarsa saura da me ya rage kuma?.
Chapter 39 · 0% Book details