Sashe 45
Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
"Wallahi kuwa yallabai nayi lallashin nayi lallashin taki ta saurareni".
"Pls Bata wayar".
Duk abinda suke zahra na jinsu ita fa wani Haushinsa takeji su baro wannan garin nasu Mai shegen nisa tun Dan hantsi Amma ya kasa kiranta sai da ya mula ya mule da tsohon Daren Nan ze wani kama kiranta tayi masa me.
Kin karbar wayar tayi ai ba bakuwa bace Aunty zilan da zataji nauyi ta dauka ko Dan kunyarta.
"Ta tashi ta fita yallabai Sai hakuri kasan da yarinta a Cikin Lamarin ta".
"Ok shikenan"
Wayar ya dangwarar a Kan bed side yana lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya.
"Haba uwar dakina yallabai baici irin wannan hukuncin ba, kiyi hakuri kome yayi Miki ki daga wayar kiji meye ze fada miki".
Autane ya leko Yana fad'in.
Aunty zilai kizo inji Ammah tana bedroom dinta".
Ya juya ya fice daga dakin.
**
S.K.T
Saida kowa ya Gama iya nasa iya yin gurin ganin lefen Amma dai mutum ko shine hasidin Iza hasada Bai Isa ya mushe kayan Nan ba, Saima korafin sunyi yawa yarinya Kamar wata diyar sarki, ba dai Wanda ya tanka tsakanin Aishat da Aunty Surayya, ba'a daukesu daga parlourn ba sai da Abbie ya shigo shida uncle Mustapha sukaga kayan Aishat taso ta bude musu uncle ya Hana Yana fadin.
"Haba Hasana sai kace Mata zamu zauna muna bude kayan sakawa muna kallo, Allah ya Sanya Albarka ya hada kawunansu ya kare fitina".
"Allahumma Amin"
Suka fada gaba daya, Aunty Surayya bata bar gidan ba Saida suka Gama duk abinda ya kamata suyi na shirye-shiyen Baki Dan Ammi taci alwashin sai ansan danta yayi Aure.
Saida Aunty Surayya ta taya su Aishat shiga da kayan wani daki kusa da Wanda Mahmud ya kwana a ciki, Amma Dan Karamin kit din da sarkokin gold ke ciki dakin Ammi aka kaisu.
Washe gari aka tashi da rabon IV na dinner da yini abinda ya girgiza duk wata yarinya data kwana ta wuni a family din dake kokarin cusa kansu gurin mahmud Kota halin Yaya ne.
****
Su Aunty Badi'a basu samu gaisawa da Abbansu Zahra ba sai da safe, yaji dadin abinda Ammin tayi sosai yayi godiya.
Bayan sun dawo sunyi break fast ne Ammah tazo musu da bayanin Abba ya sallami drivern tun dare sukayi sallama ana yin sallar Asuba ya dauki hanya yace Bauchi za'a kaiku kubi flight zuwa sokoton.
Godiya suka yiwa Ammah kamar wasu kayan duniya aka Basu, sai da zasu tafi Mama ta shigo shima Abba ne ya turota su gaisa da bakin Ammah, Amma batayi niyya ba duk da sahura ta kaimata tsegumin bakin ita abinda ya dameta shine a gabanta Lamarin salma wadda da kyar aka Zubar da Cikin tamkar bazata rayu ba Dan ta Suma yafi sau goma da kyar aka samu ta farfado, jini kuwa an Kara Mata shi yafi Leda bakwai Dan Zuba yake tamkar lalataccen famfo.
Ammah ce tayiwa su Aunty Badi'a bayanin wacece mama a gidan da kuma Matsayin su na iyayen mijin zahra.
Har dakin da zahrar take Aunty Badi'ar taje ta samu zahrar tana karatun Alqur'ani mai girma.
Tana Kai aya zahra ta rufe Qur'an din.
Shigowa tayi tana kallon Zahra wadda ta saka rigar wani material da Aunty Fateeha ta bawa tele ya dinka Mata sai tayi wani mahaukacin kyau, gefen gadon Mummy badai'a ta zauna ta nuna mata kusa da ita, Bata zauna kusa da ita ba saita zauna a Kan carpet din dake kusa da kafarta.
"Zamu tafi diyata me Zaki bamu mu kaiwa Dana kafin ki isko shi?".
Sadda Kai zahra tayi,duk kunya ta rufeta.
"Kina jina".
Kai zahrar ta gyada Mata alamar eh.
"Ki kwantar da hankalinki kada ki jewa yarona da rama, babu abinda ze rabaku in Sha Allah,mun kawo ki ne Dan Kara nema miki mutumci a idanun 'yan uwan mijinki idan aka wayi gari kawai suka ganki bazakiyi daraja da kima ba a idanunsu sai ayi muku wata fassara ta daban kinji, ki yiwa Amminku biyayya yana sonki sosai wallahi tun kafin ta ganki Allah ya nuna Mata ke a Cikin mafarkanta sau babu adadi tare da mahmud Kuma a zahiri ma Kuma ke dince dai ba wata ba, zata turo matanenta suzo har Cikin gidan Nan su daukeki su danka ki Amana a hannunta gadan dangin mahaifinsa da nata dangin, kuma duk jarabawar da tayi Miki a zaman kwana Daya daikayi da ita ba'a samu matsala ba haka muma a namu bangaren babu kuskuren da aka samu Sai ma abinda babu shi da muka samu Karin haske a cikinsa,Dan haka ki fadawa kawayenki na kusa zasu rakaki dakinki na dindidin duk sauran Wasa ne ai ya fada min yanda kukayi ta gantali kamar mararsa mafadi,Dan Allah kiyi Masa biyayya ki kula dashi jariri ne a gurin soyayya ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba kece mace ta farko Daya taba so a tarihin rayuwarsa da bakinsa ya fada min wannan yace min ya fara sonki tun Yana dan shekarar farko a university lokacin ya Dan Fara business Sameer Yana raka shi, Bai dai bude min maganar ba to kinji dai da sonki ya rayu Dan haka ki Zama jaruma a dukkan al'amuransa kinji diyata".
Kai ta gyada Mata alamar to.
Bayan tafiyar bakin ne Ammah ta dawo Cikin a parlour Ammah ta Sami zahra tana fada Mata yanda ta yaba da halin surukarta ba kadan ba.
Ba jimawa Hajiya Kaltum ta shigo suka kule da Ammah bed room din.
Zahra ma Bata koma ciki ba zamanta tayi a parlourn ita kadai tana kallon girkin larabawa.
Wurin Sha biyu da rabi Ya Abdul Hakeem ya shigo Yana fadin.
Ina Zahrar tazo tayi bako".
*AUREN HUCE HAUSHI*
AISHAT ISAH MUSAH
(Maman Fateemah)
09061432330
Or
08055362975
Page 79.