← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 47

Sashe 5

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Tun bayan fitar Rukayya zahra ta dosana gefen ta zauna ta zabga uban tagumi, da sauri tashi ta fito ta dauko handbag dinta ta biyo Hanyar da suka shigo kofar fitar ta murda tajita bam ko motsi batayi, tayi tayi taji kamar tana taba dutse, hakuri tayi ta juya sai lokacin tsoron ya rufeta da gudu ta shige dakin tana turo kofar, dube-duben makulli kofar ta Farayi ita dai bataga gurin wani key ba har zata hakura taga wasu numbers a jikin wani Abu kamar switch din kunna wuta numbers din ta Danna Yanda suke a jere taba taba ta karshe taji want Dan sound daga jikin kofar handle din ta Kama zata bude taji ta rufe gam, sai lokacin ta Dan samu peace of mind, ta nufi gadon ta aje jakar a gefe ta nufi toilet dole saita sake gyara jikinta. Tana Shiga ta cire rogar material din sajida data sako ta taho da ita ruwan zafi ta hada tayi wanka ta fito da towel a jikinta sanin ba wasu kayan sakawa a Nan yasa ta Haye gadon daga ita sai towel ta rage hasken dakin ta janyo lallausan bargo ta rufe jikinta sai fuskar kawai ta Bari a hankali ta Fara Addu'oin kwanciya barci, kafin ta Gama barcin yayi awon gaba da ita.

Karfe Daya da rabi daidai jirgin Max air ya sauka da duban jama'a daga kasahe daban daban na duniya, cikinsu harda Muhmud Muhammad Dange, a hankali yake tako stairs din jirgin sanye yake da kananun Kaya Ash T- shirt da black jeans a jikinsa sai jakar laptop dinsa a kafadarsa.
Yana karasa saukowa wani matashi fari marar jiki ya nufe shi Yana fadin "barka da sauka yallabai, ga key din motar Nan a hannunta oga yace na kaika gida, sai Balarabe ya bimu da wata motar sai mu dawo tare dashi".
Hannu ya mikawa Mai bayanin Yana fadin "bani key din kawai kace masa na gode kwarai da kulawasa, zanyi driving da kaina".
Mika masa Yana fadin "Allah ya tashemu lafiya kayi min godiya sosai ya Ciro kudin America ya mika Masa sannan ya bar gurin.
Lokacin Daya fito daga airport din Daya da minti ashirin da bakwai, tuki yake cikin nutsuwa sau biyu kawai ma'aikata suka tsayar dashi, har yazo gate din gidan ba Wanda ya Kara tsayar dashi, sau Daya yayi Horn Mai gadin ya falfalo da gudu yana leken waye a Nan baisan motar ba Dan haka ya koma ya dauko abinda ze Bashi kariya.
Kafin ya bude ya fito, Mahmud ya fito ya harde hannusa a kirjinsa ai Mai gadin Yana ganinsa yayi sauri ya koma da gudu Yana Fadin "barka da sauka fari Mai farar Aniya Allah ya Kare gabanka da bayanka baya Mai goya marayu"
Dan murmusawar Mahmud yayi Yana fadin "wani Abu sai Malam Musa shi Babu ruwansa da dare". Ya fada Yana kunna Kai harabar gidan wadda take kamar rana, mutane hudu ne suka bullo daga mabambantan gurare. Parking lot suka nufa sun San Mai gidan ne tunda suka jiyo hargagin Malam Musa. Shima da gudu ya karaso gurinsa Yana cigaba da Yi Masa kirari.
Sun gaisa sosai dasu har kusan minti biyar sannan yayi musu sallama Saida safe ya nufi babban part din, Murtala ne yayi sauri ya sameshi "yallabai Ina ganin madam din kamar tana can sabon gurin can Dan Nan Naga Sameer ya ajesu dazu ita da Rukayya kanwarsa, can ya nufa Yana mamakin me yasa Sameer ya kaita can alhalin yace a barta a tsohon part din.

AUREN HUCE HAUSHI.

MAMAN FATEEMAH.

Page 44
Chapter 5 · 0% Book details