← Book details Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 35

Sashe 35

Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sai dare sannan Sani ya farfado, yaso a sallameshi likita yace gsky baza'a sallameahiba akwai sauran gwaje-gwaje da akeson yimashi, khairat da zuby Kuma tun ranar aka sallamesu,

Khairat tawuce gida cikin tsananin tashin hankali, Wai yanzu itace d'auke da cutar 'kanjamau, Amma Zuby tacika babbar muguwa azzaluma.

Zuby Kuma Zama tayi da niyyar jiyyar Sani, sai dai tunda yaji sakamakon da likita yafad'i na Yanada 'kanjamau yasa yaji wani mugun tsanar zuby muddin Yana ganinta gabanshi zai iya rabata da numfashinta saboda haka korata yayi yace taje gida kawai bayason ganinta.

Hankali tashe zuby tafita daga asibitin cikin tsananin rud'ewa batako kallon gabanta tahau titi tana tafiya kamar wata Zararra by mistake kuwa wata mota tayi ciki da ita, Nan take tace ga garinku Nan.

Allah sarki Zuby anrigamu gidan gaskiya, sai muce Allah ya kyauta namu zuwan.

Mmn khady ce 🤼‍♀
🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 45

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

*Kuyi hakuri kunjini shiru kwana biyu hakan yasamu saboda wata Yar 'karamar matsala, bayan haka Kuma zanyi amfani da wannan damar wurin kawo 'karshen wannan labari, Amma kuyi hakuri zan takaita 'karshen labarin saboda wasu 'yan dalilai*

Bayan kwana biyu Sani kwance Kan gadon asibiti Alhmdlh yasamu sauki sosai,

Likitane yashigo d'akin hannunsa d'auke da wasu takardu,bayan sun gaisa da Sani yayimashi ya jiki Sani ya amsa "jiki Alhmdlh Babu abunda ke damuna"

Gyara zaman glass d'in fusakarshi yayi yace "sakamakon gwaje-gwajen damukayi, bayani ganowa damukayi kana d'auke da cutar 'kanjamau, sakamako na biyu Kuma ya nuna bazaka iya 'kara hauhuwa ba sakamakon buguwa dakuma tsananin razana dakayi"

"Me....." Me kake fad'i haka likita, kana nufin yanzu nida Haihuwa har abada"?

"Kwarai kuwa haka sakamakon ya nuna" likitan yafad'a tareda mi'kama Sani takardun sakamakon yafice daga d'akin.

Hankali tashe Sani yabar asibitin 'kafarsa ko takalmi Babu, tafiya yake batareda yasan inda yake saka 'kafarsaba, ikon Allah ne kawai yajaishi gidan Zuby, Yana zuwa ya tarar da mutane dankam 'kofar gidan 'yan zaman makoki, kafin ya isa wurin yaji wani dattijo na fad'in "Allah sarki zubaida anrigamu gidan gaskiya Allah jikanta da rahama" da wannan magan-ganun Sani ya tabbatarba kanshi da mutuwar zuby.

Juyawa yayi yabar wurin batareda yashiga gidanba kokuma yayima wani magana, Babu Kuma Wanda yalura dashi a wurin dukda dama bakowabane ya sanshi.

Shagonsu yanufa wurin Basiru dan yanzu Babu abunda yafi bu'kata sai kud'i, zuwa zaiyi ya 'karbi kud'insa ya tattara yanashi yanashi yaje wurin khairat ya amshi sauran farincikin daya ragemashi a rayuwa wato Khalid yawuce 'kauyensu.

Khairat tana zaune d'akinta cikin kwana biyu duk tabi ta lalace tayi ba'ki, hankalinta yagama tashi,

Ga maganin HIV din data karba asibiti amma batada kwanciyar hankalin dazatasha, dan tunda tadawo daga asibi da maganin da sakamakon gwajin da'akayimata duka tahad'a ta ajiye Kan kujera a falo Tama manta inda ta ajiyesu.

Khalid Yana d'akin Fauziyya wurin su Hanif suna wasa wani Zazzafan zazzabi ya rufeshi har Yana firgita, haniface takira Fauziyya tagwadamata Khalid d'in hankali tashe ta d'aukeshi takaishi d'akin khairat tagayamata bayada lpy, amsarshi kawai khairat tayi ta kwantar dashi dan batada nutsuwar dazata bashi wata kulawa.

Bayan azahar Salim yadawo gida kamar yanda yasaba,

Fauziyya ta gayamashi Khalid fa bayada lafiya Kuma tund'azu nakaishi wurin mamarshi Amma banga tafito takaishi asibiti ba"

'dakin khairat d'in Salim yanufa Dan ganin jikin Khalid d'in.

Yana shiga idonshi ya sauka kan ledar maganin khairat dake kan kujera, har zai wuce saikuma yadawo Yana bud'awa yafara duba magungunan danshi baitaba ganin irinsuba, tunani yafarayi wannan maganin Kuma na miye haka 'kara dubawa yayi ya d'auko takarda Mai d'auke da sunan khairat dakuma sakamakon gwajin HIV tana d'auke dashi.

Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un yafara maimaitawa, da sauri khairat tafito falo Jin yanda Salim ke rafka salati, ganin ledar maganinta gabanshi hannunshi Kuma d'auke da takardar gwajin yasa ta razana tayi hanyar waje.

Da hanzari Salim ya damkota ya wankemata fuska da lafiyayyan mari yace "khairat gayamin gidan ubanwa Kika kwaso wannan cutar?"

Zubewa khairat tayi gabanshi tana kuka, shima Zama yayi kan kujera jikinshi sai 6ari yake.

Wayarshi yafiddo yakira mamarshi yace tazo gida ba lafiya, sannan yakira Hajiya Habi mamar khairat itama yagayamata yanda yagayama mamarshi.

Ba dad'ewa suduka sun halarci taron, Fauziyya mamaki take Wai miye ke faruwa haka taga mamar Salim da mamar khairat sunzo, kodai jikin Khalid ne yayi tsanani, saboda haka itama sashen khairat tanufa Dan taji ko miye.

Ko minti goma dashigowa Fauziyya batayiba Sani yashigo gidan Babu ko sallama yayi wani wurjiga wurjiga kafa ba takalmi, kamar wani Mai tabin hankali.

Yana shigowa kallo yadawo kanshi, shima kallo yabi duka mutanen dake falon sannan yace nagodema Allah Dana iske wannan taron, saboda haka zanyi amafani da wannan damar ingayamaki irin mugun abunda muka d'auki shekara da shekaru muna aikatawa nida khairat.

Nan Sani ya zayyane masu kaf labarinshi tun kafin zuwan khairat gidan har zuwanta har Kuma zuwa lokacinda ake yanzu dayazo amsar d'anshi.

Arazane mamar Salim tace 'kanjamau" innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un Salim Babu dai abunda yashiga tsakaninka da ita"

Murmushi takaici Salim yayi yace "Ina kyautata zaton haka"

Mama tace "maza ka rubuta mata takardar saki yanzu kabata sutafi can su karata tsiyarsu"

Bama saina rubutaba khairat kije na sakeki saki ukku, Kuma kije keda Allah.

Kaikuma Sani kaci amanata kaci amanar matata inshaAllah sai kaga sakamako tun aduniya.

Mamar khairat kuka kawai take sai hakuri takeba mamar Salim.

Mama tace Babu wani hakurin dazanyi ki kwashi gayyar tsiyarki kubarmin gidan d'ana.

Sani Kuma kallon khairat yayi yace kafin kitafi inaso kibani d'ana.

Sai lokacin khairat tatuna da halinda tabar Khalid ciki, da sauri tashiga d'akin.

Wata irin razannaniyar 'kara tasaki domin ganin Khalid datayi Babu Alamar rai tare dashi.

Allah yaraba gardama kenan, Khalid yarigamu gidan gaskiya bayada rabon ganin takaicin rayuwa.

Da sauri Haj Habi tanufi d'akin khairat ta iske tanata fizge kayan jikinta tana wata irin dariya, da alama dai ta haukace.

Sani Kuma Nan aka gayamashi Khalid yamutu, innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un yafad'a baijira wani bayaniba yabar gidan.

Kai tsaye sahgon su yanufa Yana zuwa kuwa ya hango dan-dazon mutane anata zuba ruwa shagon yagama 'konewa 'kurmus.

Yana ganin haka bai Ida karasawa shagonba yayi baya yahau titi Yana tafiya tsakiyar titin, wata katuwar mota tazo tabi ta kanshi, Nan take ya margaya, wannan shine karshen masu cin Amana.

*ALHMDLH ANAN NAKAWO 'KARSHEN WANNAN LITTAFIN, SAIKUMA ALLAH YASAKE HADAMU WANI LOKACIN MAMAN KHADY KEMA MASOYA FATAN ALKHAIRI*
Chapter 35 · 0% Book details