Sashe 30
Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aiko Yana Kira ringing d'aya khairat tad'aga dama jira take.
"Hello Sani Ina kashiga inata faman kiranka tun d'azu"
"Inafa zanshiga inanan Ina fama da jikina har yanzu bai gama warwarewa ba"
"To ingayamaka akwai labari, kazo gidanan yanzu kagani da idonka"
"Mezan gani? Kawai kigayamin anan dan nanda kwana bakwai bazanzo gidankiba kidai gayamin kawai"
"Kara kazo d'in dai tunda nace kazo, gani yakore ji"
"To shikenan ganinan zuwa, amma wlh idan Naga bawani serious abu bane yasa kika kirani wlh sai rayuka sun 6aci"
"Eh naji kadaizo d'in kagani"
Suna gama wayar Sani ya canja Kaya wurin 'karfe tara da minti goma ya iso gidan, lokacin Salim yariga yatafi wurin aiki.
Sallama yayi, khairat ce ta amsa tayi saurin fitowa daga d'aki.
Wani kallo tayimashi tareda yimashi nuni da d'akin Fauziyya.
Kallon d'akin Sani yayi gabanshi yafad'i cikin murya 'kasa-'kasa yace badai tadawoba"
Murmushi khairat tayi tace "dukta dawowa mai sau'kine sai kaganata zakaga babban abun mamaki"
Fauziyya daga d'aki tanajiyo lokacinda Sani yashigo, fitowa takeso tayi su gaisa, sai dai tana mi'kewa 'kafarta tari'ke takai minti biyar tsaye awurin kafin tasamu tafito.
Sunajin alamun tafiya suduka suka maida kallonsu wurin.
Ganin Fauziyya da 'katon ciki yasa Sani yin Hocking, dan kasa motsi yayi, duka tunaninshi da kome nashi yayi sumar wucin gadi.
Muryar Fauziyya ce tadawo dashi dai-dai "Mal Sani kananan kenan?"
"Eh wlh inanan aunty, yafad'a yana 'ka'karo murmushi kamar Wanda akayima dole.
"Aunty yaushe kikadawo ne?"
"Tunjiya nadawo ai, dayake dare ne"
"Kai Amma nayi matukar farinciki, Allah tsare gaba"
"Ameen Sani nagode, ya maganar wanke-wanke kuma?"
"Kai aunty yaushe rabona da wanke-wanke, idan Kinga nazo gidannan yanzu zuwa nayi kawai mu gaisa"
"Ah Sani kacemin kazama babban yaro, kadaina wanke-wanke, to Allah ya taimaka" tana gama fad'in haka tawuce d'akinta tabarsu.
Kallon Sani khairat tayi tace "kaje kawai zamuyi magana"
Haka Sani yaja 'kafarshi yafita daga gidan Yana layi da tangadi kamar Wanda yashawu, saboda tsabar 6acin rai, Wai yanzu Fauziyya ce da wannan 'katon cikin, to yanzu ta'ina zaya bulloma wannan Al'amarin, haka ya isa gida ya zauna tunani kala-kala cunkushe a kwalwarshi.
Washe gari tun 'karfe takwas na safe Fauziyya da Salim suka fito cikin shiri, zai sauketa asibiti tasake bucking domin zuwa awo, daga Nan zaiwuce wurin aiki.
D'akin khairat yashiga yabata kudin cefane sannan yagayamata zai sauke Fauziyya asibiti.
Nan yake tambayarta "waike yaushe zaki Fara zuwa awo, naga baki ta6ayin maganar Fara zuwa awo ba"
Yamutsa fuska tayi tace "nifa banason zuwa awo, nifa asibiti idanba doleba bason zuwanshi nakeba, ko haihuwar idan Allah yakawomani da sau'ki nafiso inyita d'akina bawanda yaji bawanda yagani, sai dai aganni da babyna kawai"
"Amma Kinsan zuwa awo Yanada matukar muhimmaci gamai ciki, tananne ake gane idan akwai wata matsala Kuma ashawo kanta tun kafin lokacin haihuwa, ana gane ingancin lafiyar jaririn dake cikine ta hanyar zuwa awo, sannan Kuma ana koyama mata yanda zasu raini yaransu bayan sun haihu da yanda zasu kula da lafiyarsu"
"Hmmm zanyi tunani idan naji zan iya zanje, idan kuma bazan iyaba gaskiya bazan wahalar dakaina ba"
Fauziyya tana tsaye tsakar gida tana jiran salim ganin yanda yadad'e d'akin khairat Kuma tana jiyo maganarsu sama-sama yasa taji wani irin kishi, jitake kamar taje ta fiddo Salim daga d'akin, ganin fitowarshi yasa tad'an saki fuskarta dan bataso ya fahimci halinda take ciki.
"Muje ko" yafad'a yayi gaba tabi bayanshi,
Asibitin dai dasuke zuwa nan Salim yakaita, dan suduka Nan sukeda file, kudi yabata yace idan tagama tahau napep takoma gida.
Khairat tana ganin fitar Salim da Fauziyya takira Sani tace tanason ganinshi yanzu,
Gayamata yayi sundanyi wata 'yar tafiya Amma Nanda awa d'aya darabi zai iso,
Zaman jiranshi kawai take tanayi tana kallon agogo lokaci zuwa lokaci, tamatsu yazo suyi magana kafin Fauziyya tadawo gidan.
Yana isowa yawuce d'akin khairat din Kai tsaye, falo suka zauna suka Fara tattauna matsalar su.
Lokacin Fauziyya itama tadawo gidan dan batawani dad'eba a asibitin tagama abunda take.
Tanata sallama taji shuru, sai surutu take jiyowa sama-sama daga d'akin khairat, Jin an ambaci sunanta yasata son jin maganar da akeyi.
Matsawa tayi kusa da window d'in d'akin ta la6e.
Muryar khairat taji tana cewa "ai yanzu cikinta yayi girma maganin zubarda ciki bazai iya yimashi komeba, hanya d'ayace zamubi mukashe abunda ke cikinta shine muhad'a baki da likitan asibitin datake awo, idan taje awo yayimata Allurar dazatasa tahaihu cikin 'kan-kanin lokacin, kaga tunda lokacin haihuwar beyiba koma miye acikin zaizo ba Rai"
"Anya wannan hanyar mai 6illewa ce, bakigani za'a iya samun matsala, idan Kuma likitan ya'ki amincewa fa?"
"Hmm Sani kenan, badai kud'i ke magana ba, zanbashi kud'i masu yawa nasan zai amince da bu'kata ta"
Dafe 'kirji Fauziyya tayi, innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, kawai take mai-maitawa a zuciyarta,
Sauri tayi tafita daga gidan, ta dai-daita nutsuwarta sannan tadawo tasake kwad'a sallama da 'karfi kamar dama yanzu tadawo,
da sauri khairat tafito tana Yan kame-kame "ah kindawo kenan, wlh Nima inanan narasa d'an aike shine nabugama sani waya yazo ya taimaka yayomin cefane"
"Allah sarki" Fauziyya tafad'a tashige d'akinta.
Koda tashiga jikinta duk yayi sanyi, tunani take "Wai abunda taji da gaske ne kokuwa mafarki take, Wai yau khairat da Sani *ALMAJIRIN GIDANA* ake 'ko'akarin had'a kai acutar dani akashe abunda ke cikina, ya subhanallah, menayimaku haka me yayi zafi, ya Allah ka kareni ka tsareni daga sharrin masu sharri.
Ranar haka tawuni sukuku, Salim nadawoawa take har d'akinsa, kallonta yayi yace "Maman twowins andawo ko?"
Harararshi tayi tace "waima twowins nifa d'aya zan haifa, Kai bakasan wahalar haihuwarba shiyasa kakemin fatan twowins"
"Aike naga kinsan wahalarta tunda wannan itace ta bakwai"
Dariya tayi tace "ai dai zanyi d'in Kuma zanji"
Kamota yayi ya zaunarda ita kusadashi yace "zo gayamin ya akayi aaibitin?"
"Ba'ayi komeba Babu ma'aikata Inga zankoma general hospital kawai sai inri'ka awona acan"
"Kinaga babu wata matsala"
"Ba matsala yanda wannan asibitin zasu kula dani suma can haka zasuyimin, kawai dai atayamu addu'a Allah saukemu lafiya, nida amarya bansan waye zaifara Haihuwa ba"
"Ke Zaki Fara bakiga cikinkiba yayi ukkun nata girma"
Dariya sukayi suduka, Fauziyya tace "Allah girman cinnan na damuna" tayi maganar cikin muryar shagwaba.
Kwai-kwayon muryarta Salim yayi yace "Allah girman cikinnan na burgeni nikuma"
Rufe fuskarta tayi da hannu tace "banaso Allah"
Dariya yasamata.
Haka sukacigaba da fira cikin farinciki, harta manta da kudirin khairat da Sani akanta.
_______________________
Satin Fauziyya d'aya da dawowa Salim yasa tashirya yakaita gidan Mamarshi, mamakine ya kamata ganinta datayi da ciki, ba kunya kuma tafara Ina takasa Ina taka aza da ita.
Harda cewa "mahakurci mawadaci, kaga ikon Allah ashe zansamu jikoki har biyu kusan lokaci guda, keda khairat Allah sa ku sauka lafiya, gaskiya naji dad'in wannan abu"
Fauziyya dai murmushi kawai take tana mamakin rashin kunya irinna mamar Salim.
Ranar gidan tawuni sai bayan la'asar Salim yazo ya d'auketa har bakin 'kofa mama tayimasu rakiya tace "ki gaidamin khairat d'in idan nasamu lokaci zanzo har gida in'kara dubaku"
*Bayan watanni hud'u*
Cikin khairat Dana Fauziyya duka yashiga wata tara, khairat cikinta beyi wani girmaba, dan idan ka kalleshi zaka d'auka bai wuce wata shidda zuwa bakwai ba.
yayinda cikin Fauziyya yayi wani mugun girma, zama da kyar tashi da kyar, gawani irin kumburi da 'kafafunta sukayi suntum.
Khairat da Sani dai sunyi iya 'ko'karinsu na ganin sun zubarda cikin Fauziyya Amma abun ya faskara dan Zakaran da Allah yanufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi.
Kulawa sosai Salim yakebasu suduka, Fauziyya Kuma saboda halinda take ciki wata 'kanwar mamar Salim ce tadawo gidan dazama wacce suke Kira Inna Rabi dan tari'ka kula da ita d'akinma Fauziyyar take kwana, Inna rabi macece mai kirki da sanin darajar d'an Adam, ko kad'an halinsu ba d'ayabane dana mamar Salim.
Tana matukar son Fauziyya ganin yanda take girmamata Kuma takemata ladabi.
khairat Kuma bataji dad'in zaman Inna Rabi a gidanba dan gani take kamar antakurata anhanata sakewa, Kuma ga Inna Rabin kamar zatayi sa idon tsiya acewar khairat din.
Sani Kuma dole tasa yahakura ya'kale khairat dan tanunamashi duk wani jin dad'i dole suha'kura dashi har Allah ya sauketa lafiya.
Bahaka Sani yasoba amma ba yanda zeyi dole yahakura ya shafama khairat lalfiya.
Amma sai dai yakasa daurewa dan khairat tariga tasaba mashi bazai iya kwana bakwai batareda ya kusancetaba, saboda haka kullum cikin matsananciyar sha'awa yake.
Zuby ce tafad'o mashi arai wacce tuni takemashi tallar kanta yanacewa akai kasuwa,
Batareda bata lokaciba yaje gidan Zuby yagayamata ya amince da bukatar ta, dama abunda take nema Nan sukacigaba da badalarsu.
Mmn khady ce 👍🏻
🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 41
Bayan wani lokaci, misalin karfe 6 na yamma khairat tana zaune tana yanke farce, taji cikinta yad'an murd'a ahankali, gabantane yayi mummunan fad'uwa dan kusan kullum tunda cikinta yashiga wata na tara sai cikinta yad'an murd'a, gabanta Kuma saiya fad'i saboda ko kad'an bataso tariga Fauziyya haihuwa,
Yau abun ba iri d'aya bane Dana sauran ranakun, dan ciwon cikin 'karuwa yake da kad'an-kad'an.
Haka tayita daurewa tana cijewa, Koda Salim yadawo gidan wurin 'karfe tara na dare bata yarda yagane halinda take cikiba,
Wasa-wasa haka khairat tayita fama da ciwo har 'karfe d'ayan dare tun tanajin ciwon na d'agawa tahuta har bacci-bacci ke d'ibarta kafin yasake motsawa Kuma ta farka, yanzu yadaina dad'ewa daya motsa ko minti biyu ba'ayi yake sake tasowa, magowa tafarayi tsakar d'aki tana burgima, abun ba sau'ki. Takasa zaune takasa tsaye tsakanin falo da bedroom.
Tsakanin 'karfe shidda na yamma zuwa 'karfe shidda nasafe khairat tagama jigatuwa tafita hayyyacinta, dan za'a iya cewa batasan inda kanta yakeba.
Bayan Salim yadawo daga masallacine yashiga d'akinta yatadata tayi sallah dan yasan ba abun mamaki bane bata tashiba har yanzu.
Halinda ya isketa ciki ba 'karamin d'agamashi hankali yayiba, dan falo yayi Karo da ita a yashe ko d'aga kanta Bata iyawa, ga Jini sai faman bin 'kafafunta yake.
"Subhanallah, khairat ya akayi haka? Dama bakida lafiya baki gayamaniba"
Ido kawai take binshi dashi dankuwa babu baki.