← Book details Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 35

Sashe 23

Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk sunyi bacci lokacin, rufe gidan yayi sannan yanufi d'akinshi yayi wanka ya canja Kaya zuwa na bacci, sannan yafito yanufi dakin khairat, zuciyarshi na tafarfasa, waishi wannan yarinyar zata Kai 'kara aiko yau zatasan takai 'kararsa, zaiyimata abunda takeso amma ba yanda takesoba.

Bud'e bedroom d'in yayi ya hangota kwance kan gado tayi d'ai-d'aya tanata sharar bacci hankalinta kwance "hmm *zakisan koni waye*"

Shiga yayi d'akin ya cire kayanshi gaba d'aya sannan ya afkamata, wulakance yafara murzartar ba sassauci, cikin bacci khairat taji abunda Salim din kemata hankali tashe ta bud'e Ido ta sauke kan Salim d'in, Fara tureshi tayi Amma ko motsawa bayayi saima cigaba dayake da murzarta duk abunda yayimata mai-makon taji dad'i sai wani irin zafi dan bayayimata kome da sauki, ahaka dai har Mai afkuwa ta afku.

Sauka Salim yayi daga kan gadon zuciyarshi cikeda takaici da ba'kincikin yanda yasamu khairat d'in tariga tagama zubarda mutuncinta a waje.

Tunda yasauka kanta take zaune bakin gado tana kuka, juyowa Salim yayi ya kalleta kukanta wani mugun haushi yakebashi, shine yakamata yayi kuka ba itaba,

Kallonta yayi yace dallah malama kiyima mutane shiru, kukan ubanme kikiye abunda kike nemane Kuma kinsamu saikuma me?"
"Amma wannan abun dakayimin wlh hard mugunta" fusata yayi yace "ke nikemaki mgunta, d'auketa yayi da lafiyayyan Mari, bazato ba tsammani ta dafe kuncinta kafin ta farga ya 'kara zubamata wani marin, saida yayimata Mari biyar lafiyayye, cikin muguwar Zuciya yace "kukan bura'uban me kikeyi, bayan kinriga kingama watsewa a titi, munafukar banza, wlh saikinyi nadamar kasancewa matata"

'mikewa khairat tayi azuciye tace Nika mara, to wlh baka mari banzaba dan wlh saina rama mugu azzalumi macuci, Allah ya isa.....

.......ke nikeke zagi"
"An zageka mugu"
Sha'kota Salim yayi yafara kwallo da ita, Yana dukanta tundaga bedroom har falo, halbi Kam khairat tashashi dan Salim haukacemata yayi, Mai ha'kuri fa bai iya fushiba.

Can cikin bacci Fauziyya tajiyo ihun khairat, da kamar kada tafito saikuma taga rashin dacewar hakan.

Fitowa tayi tanufi d'akin khairat, ganin yanda Salim yadage yanata jibagarta yasa Fauziyya saurin Isa wurin tanabashi hakuri, dakyar tasamu yarabu da khairat, ta fiddashi daga d'akin yakoma d'akinshi yanata huci.

Kallonta Fauziyya tayi tace "kekuwa miya had'aku haka har kikajama kanki wannan duka"

Harararta khairat tayi tace "Ina ruwanki" taja dogon tsaki "mtswww munafincin banza kawai"
Tashi tayi da kyar tanufi bedroom jikinta ko'ina ciwo.

Murmushi Fauziyya tayi tace "bani nakashe zomonba rataya akabani, badan niba da bansan irin dukan dazakishaba, Allah dai wadaran mutumin dabaisan arzikiba"

Komawa Fauziyya tayi d'akinta, a zuciyarta tana tunanin meye khairat tayima Salim har yakemata wannan mugun dukan.

Khairat kuma kasa bacci tayi saboda yanda jikinta ke ciwo, Allah ya isa kawai takejama Salim.

Wani 6angare na zuciyarta Kuma cike da farinciki tunda bu'katarta tabiya Salim ya kusanceta, dama burinta kenan.
daga yauma bazai Kara samuntaba, zatacigaba da harkarta da Sani dan tamafi Jin dad'inshi.

*Muje zuwa Reader's yanzu aka Fara wasan* 🤸🏻‍♀

Mmn khady ce 👎🏻
[9/25, 4:32 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 32

Washe gari khairat da ciwon jiki tatashi, saida tahad'a ruwan dumi ta gasa jikin nata sosai, tanayi tanayima Salim Allah ya isa, waraka tasamu tashafe ko'ina na jikinta sannan taji sauki-sauki.

Fauziyya kuwa tunda takwaci khairat hannun Salim taga irin mugun dukan dayayimata hankalinta yatashi, koda takoma d'aki bacci gagarar idonta yayi, haka tayita juyi Zuciyarta tunani barkatai "Wai miye ke damun Salim duk yabi ya canja yazama wani birkitacce, ita yajuyamata baya Yana fushi da ita, itakuma khairat yayimata mugun duka, wani irin tsorone yakamata kada itama watarana yakamata da dukan, dukda batasan laifinda khairat din tayimashiba harya daketa.

Ranar haka suka tashi gidan sukuku, kowa da 'kunci da takaici a zuciyarshi, khairat Kuma wani sashen na zuciyarta cikeda farinciki Dan tasamu inda zata ma'kala cikin dake jikinta batareda wata gardamaba dole a karba, dan nanda 8month ta haihu aiba Wanda ya isa yace d'a bana Salim bane.

Misalin karfe takwas Salim yafito daga d'akinshi cikin Shirin zuwa wurin aiki, baishiga d'akin khairat ba, saboda mugun haushinta yakeji, d'akin Fauziyya yanufa itama dan zaibata kud'in cefane da bazai shigaba.

Bakin 'kofar yatsaya yafiddo biro da farar takarda yayi d'an shot note yahad'ata da kudin yashiga d'akin.

Duk abunnan dayake khairat tana labe jikin window tana kallonshi, takasa fitowane Dan gani take kamar Yana ganinta zai Kuma rufeta da duka.

Karar ruwa yajiyo daga toilet hakan ya tabbatar mashi da Fauziyya wanka takeyi, ajiye takardar yayi gefen gado tareda kud'in yafito daga d'akin.

Har yanzu khairat na jikin window tana kallo harya fito yabar gidan.

Sauri tayi tanufi bedroom d'inta tabud'e wata loka ta d'auko wata farar takarda tanufi d'akin Fauziyya, har lokacin Fauziyya na wanka, tura kyauren bedroom d'in tayi ahankali yanda baza'ajiba tashiga,

Dube-dube tafarayi har idanunta suka sauka kan kud'i dakuma takardar da Salim ya ajiyema Fauziyya gefen gado, hannu tasa ta kwashe takardar da kudin sannan ta ajiye takardar hannunta tayi saurin fita daga d'akin.

Komawa tayi d'akinta, bedroom tawuce da gudu-gudu kan gado ta zauna tana maida numfashi kusan minti biyar sannan tabud'e takardar.

_"fatan kintashi lafiya, ga kudin cefane nan kiyimin tuwon shinkafa miyar d'anyar kubewa_

Dariya khairat tayi tace "tuwon shinkafa miyar kubewa, hhhhhh sai dai kaci na gidan uwarka Salim amma bana Fauziyya ba"

Sallamar Sani khairat tajiyo, amsawa tayi tareda fitowa daga d'akin.

Gaisheta Sani yayi cikin girmamawa ta amsa, already dama kayan wanke-wanke killace suke farawa kawai zaiyi.

Matsowa khairat tayi tad'an du'ko saitin kunnen Sani tace "akwai labari, sannan Kuma inamaka congrats dan yau Fauziyya zatabar gidannan"

Zare Ido sani yayi cikeda mamaki yace "haba dan Allah"
"Wlh kuwa Kai dai kazuba Ido kaga ikon Allah"......

Jin 'karar tafiya yasa khairat saurin matsawa daga inda Sani yake tana cewa "gaskiya Sani yanzu kadaina wanke kwanoni su fita, Ni narasa miye ke damunka, kusan kullum yanzu idan kayi wanke-wanke idan zanyi amfani da kwano saina Kuma wankewa"

Murmushi Sani yayi ya kalli Fauziyya dake tahowa wurinshi hannuwanta d'auke da wasu plate, yace "aunty Fauzy ai kece shedar yanda nake wanke-wanke na, yoni idan nayi wanke wanke har she'ki zakiga kwanuka nayi saboda tsabar fita dasukayi"

Guntun murmushi Fauziyya tayi batareda tace komiba ta ajiye plates d'in hannunta tabar wurin, dan tasan yanzu tana iya yin magana khairat tagayamata marar dad'i, shiyasa koda yaushe take ri'ke girmanta dan batason raini.

Nan khairat ta zauna tana taya Sani fira harya gama wanke-wanke, kitchen tashiga tahad'a mashi breakfast tea da bread, Zama yayi yagama sha ya wanke cup din ya ajiye.

Bakin 'kofar d'akin Fauziyya ya tsaya yad'an d'aga murya yanda zata jiyoshi yace "Aunty abada kud'in cefane"

Tunda aka kawo khairat gidan Sani baitaba shiga d'akin Fauziyya ba, iyakarshi ya tsaya bakin 'kofa idanma zai 'karbi kud'in cefane kenan, idan Kuma ba wurinta zai karba ba ko kofar d'akin baya zuwa.

Dubawa Fauziyya tafarayi dan tasan Salim ya ajiyemata kamar yanda yasaba, hango takarda tayi kan gado sai dai ba kud'in, d'aukar takardar tayi azuciyarta tace "yaukuma ba kud'in, bari induba Inga miye ya rubuta"

Bud'e takardar tayi tafara karantawa tun kafin ta'karasa karantawa jikinta yafara kyarma tana gamawa tafashe da kuka tana mai-maita kalmar "innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un"

Tashi tayi jikinta na kyarma, kanta yad'au zafi, zuciyarta tana bugawa da sauri da sauri, hawaye nacigaba da ambaliya a fuskarta,

Yanzu Ashe dama Salim zai iya d'aukar wannan mummunan matakin akaina, akan laifinda banjiba banganiba, yanzu dama ashe zanga ba'kar rana mai d'auke da mummunan tarihi a rayuwata "Allahuma ajirni fi masibati wa khalibli khairan minha" nayi tawakkali gareka Allah nasan kowane mutum Yanada irin tashi 'kaddarar na yarda ni wannan itace tawa, Allah kabani ikon cinye wannan jarabawa dakayimin, Allah sa hakan yazama Alkhairi arayuwata"

Daya daga cikin trolley dinta ta d'auko tafara had'a kayanta da duk abunda tasan zata bu'kata, irin 'kananun kayan bu'kata tazuba cikin hand bag d'inta ta rataya sannan ta d'auko hijab d'inta tasaka tajawo trolley d'inta tafito tasa key tarufe d'akin tana share hawaye tasaka key d'in a bag d'inta.

Sani da khairat dake tsaye Sani Yana jiran abashi kud'in cefane, khairat Kuma tana jiran ganin abunda zaifaru sai ganin Fauziyya sukayi Jaye da trolley tabi hanyar barin gidan.

Saurin Shan gabanta sukayi har suna had'a baki "lafiya Fauziyya meya faru"

Shiru Fauziyya tayimasu da kamar kada tafad'a saikuma taga idanma bata fad'aba dole su sani domin Hausawa nacewa idan andafa boye ba'aci boye.

Handbag d'inta tabud'e ta fiddo takarda tami'kama khairat, amsa tayi tana tambayar "na miye wannan"?

Goge hawaye Fauziyya tayi tace "kiduba mana Zaki gani"
Bud'e takardar khairat tayi tana gama karantawa taja wani dogon salati, "shiko Salim meya kaishi yanke wannan mummunan hukunci"
amsar takardar Sani yayi yaduba "ya subhanallah" yafad'a tareda dafe kanshi da hannu biyu
"Amma Ina hankalin oga Salim yatafi haka, me yayi zafi Shiba wutaba"

Dafa kafadar Fauziyya khairat tayi tace "yanzu Ina zakije"
"Ina zanje Wanda yawuce gidan iyayena ai banida inda yafi can"
"Hakane bakida inda yafi gidan iyayenki, amma dazakibi shawarata kije gidansu Salim kigayama Mama, maybe tasa yajanye wannan matakin daya d'auka"

Kallo Fauziyya tabita dashi batare datace komiba, amsar takardar tayi daga Hannun khairat ta linke ta maida jikka taja trolley dinta tabar gidan.

Tana fita cikin sa'a tasamu napep tasauke wata mata Nan kusa dasu tashige tagayamashi inda zai kaita, mintuna ishirin da wani abu sun kaita gidansu, bayan ta sallami mai napep tashiga gidan, ko sallama batayiba tana shiga ta saki trolley din tsakar gida ta dur'kusa anan tafashe da wani irin kuka mai ban tausayi.

Da sauri mamarta ta fito daga d'akin jin kukanta tsakar gida dan bataji lokacinda tashigo gidanba.

"Ke Fauziyya lafiya meya faru" kasa magana tayi sai kuka kawai takeyi kamar zata si'ke.

"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un" mama tafad'a "yau Naga ikon Allah tashi mushiga ciki" kamata tayi suka shiga ciki sannan tadawo ta d'auki trolley d'in.

"Fauziyya kigayamin abunda ke damunki, kintsaya kinata kuka wannan kukan bayada amfani agareki"

Takarda tami'kamata tanacigaba da share hawaye.
Chapter 23 · 0% Book details