← Book details Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 35

Sashe 21

Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saurin kamashi khairat tayi ta fiddashi daga gidan ganin Yana neman tonamata asiri, tace "haba Sani miye haka zaka wani fad'i zaune kamar mai Shirin hawa bori, ko Kaine aka mara, iya abunda zakayi kenan, idan kuma haukanka yasa aka ganmu fa"?

"Ba wanda zai ganmu, Kinsan ba abunda natsana arayuwata irin Inga abunda zai taba lafiyar Fauziyya, gaskiya ki canja wani abun banda abunda zaisa adinga dukanta, Kinga wannan kyakkyawar fuskar tata banison abunda zai tabata wlh bakijiba marinnan har cikin raina"

"Naji jeka da Allah, tafad'a tana anguzaahi waje, kada kasa asamu matsala zamuyi waya anjima"

Fita Sani yayi ranshi abace, khairat Kuma da sauri takoma cikin gidan tanajiyo yanda Salim keta zubama Fauziyya ruwan bala'i.

Shiga d'akin khairat tayi tace "lpy dai nakejiyo hayaniya?
"Lpy lao Salim yafad'a yasa Kai yafice daga d'akin zuwa d'akinshi,dan ko kad'an bayaso khairat tasan abunda ke faruwa tsakaninshi da Fauziyyar, Amma hakan bazai hanashi hukuntataba, hukunci Kuma mai tsanani, saita gane kuskurenta.

Kallon Fauziyya khairat tayi tace "lafiya yanaga kina kuka wani aka aikomaki ya mutu?"

Banza Fauziyya tayi da ita tatashi ta d'auke maganin da Salim ya watsamata tashige bedroom tabarta nan.

Tabe baki khairat tayi tace "hmm kyaji dashi banza, nariga nasan kome, dakifad'a da karki fad'a duk d'ayane awurina Kuma zancigaba da bibiyarki har saina cimma burina.

*Kuyi hakuri da duk yanda kuka samu munafama da matsalar NEPA*

Mmn khady ce 💃🏻
[9/25, 4:32 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 29

Koda Salim yakoma d'akinsa zuciyarsa tacigaba da tafar-fasa, "Wai miye ke damun Fauziyya data zabi Shan maganin Hana d'aukar ciki, bayan tasan rashin haihuwarta babbar matsalace tsakaninsu, tana ganifa yanda Mama ta tsaneta saboda rashin Haihuwa"

Zama yayi gefen gadonshi ya dafe kanshi da hannu biyu
"hmmm lallai biri yayi Kama da mutum, shiyasa har yanzu Fauziyya bata Kuma samun wani cikinba, bayan maganinda likita yabada yace indai tasha zata iya samun ciki kodawane lokaci" mi'kewa yayi tsaye yayi taku daya biyu zuwa ukku, "Wama yasani ko batasha maganin da likitan yabada ba tunda ba son haihuwar takeyiba.

Bai ankaraba sai Jin hawaye yayi yanabin kumatunshi, Fauziyya mesa kikamin haka, miyasa Kika zabi Zama cikin 'kunci da tsangwamar mahaifiyata ta sanadiyyar hana kanki Haihuwa da kikayi"

Komawa yayi kan kujera ya zauna yahade hannayensa duka biyu ya matse, jikinshi har karkarwa yake tsananin 6acin rai.

"Yazama dole in d'auki mataki akanki"
Tashi yayi rai 6ace yashiga toilet yashekama jikinshi ruwa ya d'auro Al'walar la'asar sannan yafito ya canja Kaya yafita zuwa masallaci.

Khairat daga d'akinta tana ganin fitar Salim daga gidan tawani daka tsalle tafara rawa tana kwaso shoki, tayi tayi takumayin shaku shaku, sannan takoma zanku, saida tayi rawa tagaji sannan tanufi bedroom tanata faman Nishi kamar wacce tayi tseren gudu.

Zama tayi gefen gado ta d'auko wayarta number Sani ta lalubo ta dannamashi Kira.

Ringing d'aya ya d'aga dama jiran kiranta yakeyi Dan tunda yabaro gidan hankalinsa bai kwantaba ganin yanda Salim yad'auki zafi akan Fauziyya.

"Hello" khairat tafad'a cikeda zumud'i.
"Ina jinki" Sani yafad'a.

"Kai mutumina bom d'inda na d'ana yariga yagama tarwatsewa"

"Hmm khairat nidai gaskiya banji dad'in abunda yafaruba"
"Kamar ya bakaji dad'iba"
"Nifa banison 6acin ran Fauziyya ko kad'an"......

"Kai dallah dakatamani" tafad'a cikin fad'a _in banda iskanci yaushe anayima bakin 'ko'kari kana wani bakason haka, wlh idan ka 6atamin rai zanbaryin kome in kyaleka kaje can kamutu da son Fauziyyar Kuma kasan bazaka ta6a samuntaba........

"Ke dallah dakata, 'karamar Yar bariki, nikike gayama wannan maganar, to wlh ki kiyayeni dan koni Ina tsoron abunda ke kaina, zanshukamaki mugun rashin mutunci, haka mukayi dake cewa nayi kisa wannan kidahumin mijin naki ya d'auki wannan 'kazamin Hannun nashi yad'ora kan fuskar Fauziyya Kuma har mari biyu saboda kidahumanci, to kasani idan Kika kuskura yakara bugunta kome zai iya faruwa"

Tunda Sani yafara bala'e jikin khairat ke kyarma wani irin mugun tsoron Sani ya d'arsu azuciyarta.

"Haba my Sani miye abun d'aga murya Kuma, tafad'a cikin kaskantar da Kai, "kasanfa nidakai Amana ne, baikamata ace kana d'agamin muryaba, shikenan yanzu dai nayima Alkawari Salim bazai Kara Kai Hannunshi ya d'aki Fauziyya ba"

"Dadai yafi"
"Hmmmm" khairat tafad'a
"Hmm, Kuma kifadamin idan akwai magana"
"Babu magana"
"To shikenan tawan dan Allah kiri'ka kiyaye abunda zai sani 6acin rai, yanzu mi kekeyi?"

"Bakome"
"Muhad'u gidan Zuby mana"
"To shikenan muhad'u can d'in barina fito" tsinke Kiran tayi sannan tafad'a toilet tashe'ka wanka a gurguje tayi simple make up tashirya cikin wasu Riga da wando na Pakistan army green ta yafa mayafin kayan wayarta ta d'auka takira number Salim tanata ringing bai d'agaba harta tsinke, kusan sau ukku tana Kira amma no answer, massage taturamashi _Nakira wayarka baka d'aukaba dama zanje wurin kitso ne_ turamashi tayi saida ta tabbatar da massage din yashiga sannan tasaka wayar cikin porse dinta tasa Kai tabar gidan.

Sanye yake cikin shirt dark blue Mai ratsin fari sai wando jeans hannunshi d'aure da fashion watch Fara 'kar, d'ayan hannun Kuma sanye da irin sarkar da maza 'yan gayu ke sanyawa a hannu, Kusan minti goma Sha biyar da zuwan Shi 'kofar gidan Zuby Yana jiran khairat Amma batazoba, ranshi yayi matukar 6aci dan amatse yake gashi itakuma tana neman ta 6atamashi lokaci, wayarshi ya fiddo daga aljihun wandonshi Yana Shirin Kiranta yaga napep ta tsaya khairat tafito kud'i tafiddo ta sallami Mai napep d'in sannan tadoshi inda sanin yake, suna had'a Ido gabanta yayi wani mummunan fad'uwa ganin yanda idanunshi suka kad'a sukayi ja saboda tsabar jarabar dake cinsa.

Saurin shigewa tayi gidan yarufamata baya, tana shiga gidan ta iske zuby falo ko gaisawa basuyiba ta wuce bedroom Sani yabita.

Ta6e baki Zuby tayi a ranta tace "baccin ina samun kud'i wurin khairat da mi zai hana inyimata kwacen wannan guy d'in amma, duk da haka ba hakura nayiba, saina d'ana nima.

(Kuji zuby Wai itama saita d'ana kamar wata mota 🤣)

Khairat tana shiga d'akin ko gama cire Kaya batayiba Sani ya afkamata kamar dabba, haka yayita mid'iddikarta bai sauraramataba saida yabiya bu'katar shi.

Yana gamawa yashiga toilet yasheka wanka yafito yasaka kayanshi, har lokacin khairat na kwance kan gado tana tunani "Wai yau mike damun Sani haka, gashidai yanda ya afkamata ba shiri Kuma bata gama biyan bukatartaba yabarta, gashi Kuma duk yahad'e girar sama data 'kasa, ita tsoron yimashi magana ma takeyi.

Du'kowa yayi saitin fuskarta yace "nizan wuce"
"To" kawai ta iya bashi amsa tajuyamashi baya.

Murmushin mugunta Sani yayi Dan yasan abunda ya aikata yace "to kawai zakice bazaki bani wani abu ba"?

"Bazan badaba dallah ka kyaleni, mtsww taja dogon tsaki ta gyara kwanciyarta, dariya yayi yace "ok bye" yafice daga d'akin.

Harabar gidan ya iske zuby zaune kan kujera tana waya, ganin fitowar Sani yasa ta tsinke wayar ta kalleshi tace "harka fito?"

"Eh" Yacemata kawai yasa Kai yafice.

Murmushi tayi tace "zan kamaka a hannu, zanyima 6arin kud'i fiye da yanda khairat keyima, saina mallakeka, kamar yanda khairat ta mallakeka.

6angaren Salim Kuma tunda aka idar da sallar la'asar yakasa fita daga masallacin tunani kala-kala cunkushe a kwalwarshi.

Yanzu wane mataki yakamata in d'auka akan Fauziyya, kodai inje Ingama Mama?
"Kai a'a gayama mama tamkar 'kara rura wata wutar ne a gidana.

"To kodai gidansu zanje inkai 'kararta?"

"Bazanyi hakaba, idan nakai 'kararta bansan wane mataki zasu d'aukaba"

Kawai bari inbarshi tsakanina da ita zanyi solving din kome batareda Kowa yasaniba.

Wayarshi datayi ringing har sau ukku Bai d'agaba, sannan yaji shigowar massage yad'auka yaduba, ganin sakon khairat ne, Yana gama karantawa yamaida wayar Aljihu yanufi hanyar gidan dan yanasao yayi magana da Fauziyya yanzune zasuyita tunda khairat batanan.

Mmn khady ce 🙏🏻
[9/25, 4:32 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 30

Fauziyya kau tunda Salim yafita daga d'akinta take kuka, tunani yayimata yawa a kwalwarta, "Ina Salim yasamo wannan maganin, itadai tasan batada ala'ka da wannan maganin Amma sai gashi yana tambayarta akanshi, miye Kuma hakan ke nufi?"

Tashi tayi tafara safa da marwa acikin d'akin tanaso ta tuna ala'karta da wannan magani, amma iya tunaninta da dogon nazarinta har yanzu bata iya tuna komiba.

"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Allah kafitar dani daga cikin wannan masifar dake nemen afkamin"

Sallamar Salim tajiyo, da sauri takoma gefen gado ta zauna hankalinta tashe, wani irin tsoron salim yakamata, dan d'azun yabata tsoro sosai, tunda take dashi bata taba ganin mugun 6acin ranshiba irinna wannan lokacin.

Shigowa yayi d'akin ya zauna kusa da ita sannan yakira sunanta,
amsawa tayi kanta sadde tana kallon 'kasa hawaye na d'iga daga idonta.

"Inaso kigayamin gaskiya, banaso ki boyemin kome kigayamin tsakaninki da Allah mi kika Sani dangane da wannan magungunan?"

Cigaba da kuka Fauziyya tayi tama kasa magana.
"Fauziyya tambayarki nake ba kuka nace kiyiminba, kigayamin"

D'ago runannun idanunta tayi Wanda suka canja launi zuwa ja saboda tsabar kuka tace "ka yarda dani Hubby wlhy bansan kome akan wannan maganin ba" tafad'a tana Karo goge hawayen dake zarya kan kumatunta.

Shiru Salim yayi na tsawon minti biyu, sannan yami'ke tsaye yafara Kai komo cikin d'akin Yama rasa ta inda zai bulloma al'amarin.

Gaban Fauziyya ya tsaya idanunshi sun kad'a sunyi jajir saboda tsabar 6acin ran dayake ciki, hannuwanta yakama duka biyu yami'kar da ita tsaye ya zubamata idanunshi masu firgitarwa yace "kigayamin gaskiya Fauziyya, yaushe kika canja, kin canaja hali Fauziyya kinzama ma'karyaciya macuciya, maci amana, kin cuceni kin ha'inceni ashe dama.....

Yarfar da hannuwanta yayi dayake ri'ke dasu cikin 6acin rai, yakoma ya zauna bakin gado yadafe kanshi da hannu biyu, wani bala'in ciwo yakeji kan nayimashi.

Zuwa Fauziyya tayi ta durkusa gabanshi ta d'ora hannunwanta kan cinyoyinsa, lumshe idanunsa Salim yayi hawayensa na d'iga kan hannunta, bin Hannun nata tayi da kallo tanajin ciwon zubar hawayen mijinta.

"Kayafemin hubby wallahi bansan komeba, tsawon shekara nawa muna tare dakai bantaba yimaka 'karyaba, baka taba samuna da wani mummunan Hali........
Chapter 21 · 0% Book details