← Book details Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 35

Sashe 29

Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan akayi setting d'in kome, aka Kira mama da Baban Fauziyya aka gayamasu kome akayimasu cikakken bayani, Kuma aka sanar dasu Fauziyya zata dawo d'akin mijinta Nanda kwana biyu.

6angaren Salim yaso ace gobe suyi asubanci subaro abujar Amma tunda ance kwana biyu dole shima ya zauna sai kwana biyu sutafi tare, Dan bazai iya tafiya yabar Fauziyyarshiba tunda harya ganta, abunda yadad'e yana nema"

*Jama'a Wai Ina Sani da khairat*

Tunda Salim yatafi Sani yadawo da yini gidan, sunata she'ke ayarsu shida khairat, ranarda Salim yakwana d'aya washegari Sani agidan yakwana, Kuma ya yini.

*(Niko nace khairat da Sani kuci karenku ba babbaka, lokacin kune)* 🤣

*Washe gari*

Wurin 'karfe takwas na safe Salim da Fauziyya suka fito cikin shiri, baban walid yahad'asu da driver zai kawosu har gida, har bakin mota sukayimasu rakiya sunata *ALHINI* rabuwa da juna, walida kuwa kuka take sosai saitabi aunty, ganin kukan walida yasa itama Fauziyya zubda hawaye.
Allah sarki sabo turken wawa.

Ahaka suka shiga mota da duka kayansu maigadi yabud'e masu get suka dau hanya.

*$alim da Fauziyya saimuce Allah maidoku gida lafiya*

Khairat da Sani kamar yanda aka Saba, ankwana tare Kuma gari ya waye amma ba'a rabuba gashi har rana tayi azahar tawuce misalin 'karfe biyu da minti arba'in da takwas.

Sani kwance Kan gadon khairat bakome jikinsa dagashi sai boxer, khairat kuma daga ita sai d'aurin 'kirji, tana kitchen tana dafamasu abunda zasuci, sallamar Salim tajiyo bakin 'kofar d'akinta.

Dagudu tafito daga kitchen d'in, ganinshi tayi tsaye hannunshi d'auke da jikkar kayanshi Wanda yatafi dashi, take wata irin zufa ta karyo mata, jikinta yafara 6ari tama rasa miye zatayi.

*Shin tsayawa zatayi kokuwa rugawa zatayi ta 6oye kwartonta*

Mmn khady ce 🤪

*Nasan bakuso natsaya ananba, kuyi hakuri matsalar ba daga gareni takeba tana ga* 👉🏻💡
[9/25, 4:32 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 39

*Martani*
*Gareki Jakadiyar shaci fad'i kike ko fad'i ba'a tambayekiba, kokuma yi ba'a sakiba oho dai, Inda nagodema Allah ko a gidan sarauta Jakadiya cikin jerin bayi take, saboda haka ke tamkar baiwa kike agareni tunda kina biye da labarina Kuma dole sai abunda narubuta Zaki zakaranta ko kinaso ko bakiso,*

*To kisani nibanida lokacinki, sakarai marar aikinyi, tunda wannan ai rashin aikinyine ba'a kasa dakaiba ka kwasa, to kisani Ni Zee Elkaseem Nafi 'karfinki, kitsaya matsayinki idankuma bahaka hmmm.....*

Dagudu khairat tafito daga kitchen, ganin Salim tsaye bakin 'kofar d'akinta hannunshi d'auke da jikkar kayanshi da alama saukarshi kenan.

Wata irin mashahuriyar zufa tahau keto mata ta ko'ina cikin 'kan-'kanin lokaci taji'ke kamar wacce aka watsama ruwa.

Cikin daburcewa tace "am... Ahh.. wai... Ashe dama yau zaka dawo"....

Zubamata idanu Salim yayi Yana karantar rashin gaskiya tattare da ita,

Azuciyarshi yace "itakuma wannan meya sameta haka daga ganina duk tawani rud'e.

"Eh tun jiya muka gama abunda mukeyi Kinga kuwa mizamu jira"

"Ehhh.... Hakane..... To muje d'akinka mana" tafad'a tana 'kare kare 'kofar d'akin.

Sosai Salim yalura khairat bataso yashiga d'akin, saiyaji zuciyarshi nason shiga d'akin dan yaga miye haka Wanda bataso yagani taketa faman kakkare 'kofa.

Murmushi yayi yace "Kuma ko jikkar baza'a amsarminba ayimin sannu dazuwa nasha doguwar tafiya"

Murmushi khairat tayi ta sunkuya cikin ladabi ta 'karbi jikkar "sannu dazuwa ya hanya" tafad'a tana'ko'karin fitowa daga d'akin.

Tagefenta Salim yabi yashiga d'akin, sauri tayi tadawo baya, tana kame-kame tsoronta d'aya kada Salim yashiga bedroom ya iske Sani.

Wata irin ajiyar Zuciya mai 'karfi ta sauke ganin Salim ya zauna falo Kan kujera,

Jin ajiyar Zuciya datayi yasa Salim ya'kara kallonta Yana nazarin halinda take ciki.

Shiru sukayi nawani d'an lokaci kafin Salim yace "yau Kuma da d'aurin 'kirji ake Zama da rana haka"

"Uhum hmm wlh zafi naji Yana damuna shiyasa nacire zanshiga wanka kenan kazo, barima inje ind'an watsa ruwa kaga sai zufa nake"

Bedroom tanufa Salim yabita da Ido,

Sani kuwa yanajin shigowar Salim hankalinshi yayi mugun tashi, kayanshi ya tattara duka yari'ke ahannu hada takalma yakama zagaye ad'akin yarasa Ina zai boye, idanunshi ne suka sauka kan wadrope, da sauri yabud'e yashiga yamaida murfin yarufe, Aiko wani mugun zafi yayimashi sallama, yafara d'iga zufa sai ketomashi take ta ko'ina, abu biyu yahad'emashi ga zufar rashin gaskiya gakuma zafin da ake zubawa agari.

Khairat nashigowa bedroom d'in bataga Sani inda tabarshi ba, dube dube tafarayi tana neman inda yake, labulen d'akin duk ta d'aga baya nan, tabud'e toilet ko taganshi nanma bayanan, Zama tayi bakin gado tana tunanin to Ina yashige, kadafa yaje yafito asirinsu ya tonu,

Kusan minti goma sannan tatuna da wadrope tayi saurin tashi tabud'e, Sani dake ciki ya cure wuri guda yanajin anbud'e murfin wadrope d'in yafasa 'kara, Yana ganin khairat yayi saurinsa hannuwanshi duka biyu yatoshe bakinshi.

Afirgice khairat tad'ora hannunta kan bakinta Alamar yayi shiru, maida murfin wadrope d'in tayi tarufe tasaka key ta kulle tacire key d'in tasaka cikin bedside.

Toilet tashiga tayi wanka, a wur-wurce jitake kamar Salim zaigane kome ke cikin d'akin.

Zama tayi gaban mirror tana shafa, Salim yashigo d'akin,

A firgice tajuyo ta kalleshi, sannan tayi saurin saita nutsuwarta tace "kagaji dajirana yanzu nafito wankan, kakoma falon Mana Ina zuwa.

"Al'wala zanyi toilet dinki inyi sallar la'asar gashi anata kiran sallah masallatai"

Yan soshe-soshe take na rashin gaskiya tace "uhum zakaje masallaci"

"A'a Nan zanyi sallah, nagaji sosai saina huta anjima zanfita"

Wani mugun takaicine yakamata jin yace bazai fitaba, amma saita danne tace "eyyah sannu aifa dole asha gajiya anyi doguwar tafiya"

Shiga toilet din yayi ya d'auro Al'wala ya shimfida prayermat ya kabbara sallah, Yana gamawa yace "Bari inshiga ind'an watsa ruwa kafin in kwanta inhuta, Amma ki gyaramin gadon Naga dukya yamutse"

"To" tace tatashi jiki na kyarma tafara gyara gadon.

Salim nashiga ta ajiye gyaran gadon tad'auko makullin wadrope d'in tabud'e cikin muryar rad'a tacema Sani "yi sauri kafito yashiga wanka"

'ki'kiniyar fitowa Sani yafarayi Amma yakasa saboda jikinshi duka ya 'kage sakamakon dad'ewar da yayi a takure.

'karar bud'e kyauren toilet yasa tayi saurin maida wadrope d'in tarufe tasaka key, tazare key din tari'ke ahannu.

Kallonta Salim yayi yace "bakima gyara gadon ba kenan,?

"Eh uh a..... Da wai canjama bedsheet zanyi saida naduba Naga ashe Shima yayi daud'a, kodai katafi wancan gudan bedroom d'in kahuta tunda kaga shi a gayare yake"

"Barshima kawai nad'an kishingid'a a falo"

Yana fad'in haka yafito falo ya kwanta Kan three seater.

Da sauri tasanyo wata doguwar riga itama tafito falon ta zauna, shiru sukayi jugum suduka Babu Wanda kecema wani uffan.

'kauri khairat tajiyo daga kitchen dagudu tanufi kitchen d'in, sai lokacin tatuno da girkinda tad'ora,

iskewa tayi ruwan ya tsane tsaf abincin ya'kone Yama Zama kamar gawayi saboda 'konewa.

Da sauri tasauke takashe wutar, tadawo falon ta zauna.

Sani ana wadrope duk illahirin jikinshi ya ri'ke, ga wata munafukar yunwa dake kwakularmai ciki.

Ahaka har akayi Kiran sallar magrib toilet Salim yakoma yayo Al'wala yafita zuwa masallaci.

Saida tabishi tale'ka taga tabbass yabar unguwar sannan tadawo da sauri tabud'e Sani, ta taimakamashi yafito daga wadrope d'in, idanunshi sunyi jajir dan tsananin u'kuba.

Koda yafito kasa mi'kewa tsaye yayi, dakyar dai tarakashi yafita gidan, dagashi sai boxer da kyar ya iya sa Riga, wando da takalmi kuwa a hannu yari'ke.

Yana fita ta sauke ajiyar Zuciya.

Shima ajiyar Zuciya yayi dan yana fita daga gidan ji yayi kamar anfiddoshi daga wuta an tsomashi ruwan sanyi.

Salim kuwa Koda yaje masallaci akayi sallar magrib tsayawa yayi saida akayi sallar isha'i yayi sallah sannan yawuce gidansu Fauziyya dan anan ta sauka.

Kara gaida maman Fauziyya da Babanta yayi, Nan sukayimasu nasiha Mai ratsa jiki tareda yimasu addu'ar neman tsari daga masu muguwar aniya.

Basubar gidanba sai 'karfe Sha d'aya nasafe, lokacin khairat tadad'e dayin bacci, saboda haka Fauziyya da Salim d'akin salim sukayi masauki anan suka kwana wannan dare ansha amarci kamar.........

*Washe gari* misalin karfe takwas nasafe khairat tatashi, d'akin Salim tanufa itaga mai miji.

Kusan Karo sukayi da Fauziyya tana Shirin fitowa daga d'akin,

Wata muguwar razana khairat tayi,
Tayi saurin ja dabaya idanunta suka sauka kan 'katon cikin Fauziyya.

Dagudu takoma d'akinta batareda tayima Fauziyyar maganaba, bedroom tawuce tana maida numfashi kamar wcce taga wani abun tsoro, itakao Fauziyya binta tayi da kallo sannan ta girgiza Kai tace "Allah mai iko" tawuce d'akinta tabud'e, yanda tabarshi haka yake, sai yar 'kura dayayi, gyara tahauyi cikin d'an lokaci tagayara ko'ina ta kakkabe tagoge, sanan tafeshe ko'ina da freshener tabi da turaren wuta, Aiko take 'kamshi ya mamaye gidan bama d'akin kad'aiba.

Khairat Kuma tana shiga d'aki ta zauna bakin gado tana maida numfashi, wayarta ta d'auko tafara Kiran number Sani amma harta tsinke bai d'agaba, takuma Kira nanma shiru, takira yakai sau goma Sha biyar amma ya'ki dagawa.

Mmn khady ce 😎
[9/25, 4:32 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 40

💃🏻
*Oyoyo Maman twowins tadawo jama'a kutayani murna, kullum inata cigiya Ina faman Kiran waya bani samu ashe ba lafiya, Allah ubangiji ya'kara lpy, Allah sa zakkar jikine, Allah Kuma yaraya Mana twowins, Allah karo wasu three wins, muzo mukwaso shoki da shaku,shaku, Kai hadama zanku zanyi dan murna*🤣
*Comment d'inki akan littafina Yana matu'kar Sani farinciki, iya wuya muna tare* 🤞🏻

Duk da haka khairat bata ha'kura da Kiran number sani ba, cigaba tayi da Kira.

Sani Kuma Yana ganin Kiran ya'ki dagawa dan gani yake kamar idan yad'aga kome zai iya faruwa, jiyakema kamar idan yad'aga muryar Salim zaiji, dan tun jiya wani mugun tsoron salim yakamatashi.

Khairat gajiya tayi da Kira ta ajiye wayar tahakura,

Sai bayan kusan awa hud'u da Kiran sannan yayi tamaza azuciyarshi yace baridai inkira inji miye yasaka taketa kirana haka, tun farkoma bai kamata in'ki d'agawaba, fad'uwar gaba asarar namiji.
Chapter 29 · 0% Book details