← Book details Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 35

Sashe 34

Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Koma nawa Kika kashemasa Ina ruwana, Nikuma dakika gogamawa ubanme Kika bani"
"Uban mi zanbaki kuwa, sakamakon daya dace dake ne wannan, kina nufin zakiyi bariki ki wanye lapiya, harma kisamu sakamakon samun miji Kamar Salim...

Wani mugun naushi khairat tayima zuby abaki, Nan take ha'korinta guda yacire jini yafara ambaliya.

Itama zuby dukan khairat d'in take, haka sukayita danben bala'i cikin gidan Babu Mai rabasu, ga Sani kwance a sume harta kanshi sukebi suna takawa wurin fad'a.

Kafin kace mi sunyima kawunansu muguwar illah, khairat tafi zuby 'karfi saboda haka zuby tafi jin jiki, sai dai wani mugun cizo da zubyn ta labtama khairat a kafad'a Wanda saida taciro tsokar wurin.

Kayan jikinsu Kuma sun yayyage sunyi fata-fata.

Sani dai Yana kwance rai hannun Allah,

Suma dasuka gaji da damben kowace zubewa tayi tana maida numfashi Babu mai iya tada wani cikinsu.

Azabar ciwon da bakin zuby keyi sakamakon fita da ha'korinta yayi shiyafi kome addabarta, rarrafawa tayi ta d'auko wayarta takira number Alhj Haladu wani abokin tambad'ewarta ne tagayamashi sunanan gida itada mijinta ba lafiya ya taimaka yazo yakaisu asibiti.

Minti ishirin Alhj Haladu ya iso gidan, yayi mamakin yanda yasamesu Kamar wad'anda sukayi wani mummunan had'ari.

Haka ya kwashesu yazuba mota yakaisu general hospital, akace baza'a kar6esuba sai anzo da police,

Ganin suna neman su jazamashi wata fitinar yasa yakaisu wata asibitin kud'i Nan aka kar6esu aka Fara Basu taimakon gaggawa, sannan khairat taro'ki likita dayayimasu awon HIV suduka,

Jininsu aka eba akaje lab, suduka sakamakon d'ayane suna d'auke da cuta Mai karya garkuwar jiki.

Sai dare sannan Sani ya farfado, yaso a sallameshi likita yace gsky baza'a sallameahiba akwai sauran gwaje-gwaje da akeson yimashi, khairat da zuby Kuma tun ranar aka sallamesu,

Khairat tawuce gida cikin tsananin tashin hankali, Wai yanzu itace d'auke da cutar 'kanjamau, Amma Zuby tacika babbar muguwa azzaluma.

Zuby Kuma Zama tayi da niyyar jiyyar Sani, sai dai tunda yaji sakamakon da likita yafad'i na Yanada 'kanjamau yasa yaji wani mugun tsanar zuby muddin Yana ganinta gabanshi zai iya rabata da numfashinta saboda haka korata yayi yace taje gida kawai bayason ganinta.

Hankali tashe zuby tafita daga asibitin cikin tsananin rud'ewa batako kallon gabanta tahau titi tana tafiya kamar wata Zararra by mistake kuwa wata mota tayi ciki da ita, Nan take tace ga garinku Nan.

Allah sarki Zuby anrigamu gidan gaskiya, sai muce Allah ya kyauta namu zuwan.

Mmn khady ce 🤼‍♀
🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 44

*MASU SIYARMIN DA LITTAFI ALLAH YA ISA BAN YAFEBA, KUMA INSHAALLAH KUD'IN BAZAI MAKU ALBARKA BA*

Motar da abun yafaru Kan idonta ce tafara tsayawa kafin wasu motocin duk su tsaya domin taimakon wad'anda sukayi accident d'in.

Kafin ayi wani Abu har police sunzo, nan aka samu aka fiddo Sani Babu Rai tare dashi amma baiji ciwo ko kad'an ba.

Zuby Kuma ansha wahala kafin asamu a fiddota can 'kasan seat itama dai Babu rai amma bataji ciwoba sai Jini dake bin 'kafafunta.

Asibiti aka wuce dasu, kasancewar basuyi nisa dagariba shiyasa aka dawo dasu babban asibitin dake garin, emergency room aka nufa dasu ba Kamar zuby tana matukar bu'katar taimako.

Likitoci ne suka taru akansu domin ceto rayuwarsu, kusan awa biyu kafin asamu numfashin Sani yadawo jikinsa.

Zuby Kuma dama basu dad'e dazuwa asibitin ba ta farfad'o sai dai tayi asarar cikin dake jikinta.

Kwanan Sani da Zuby biyu a asibiti aka sallamesu suka dawo gida, bazaka kallesu kace sunyi wani accident ba, dan babu ko kwarzani a jikinsu, sai dai rashin gudan jininsu dasukayi, Wanda hakan ba'karamin ciwo yayimasuba, bama Kamar Sani Allah yasanyamashi son cikin zuby tun kafin yazo duniya, ashe dai bazai rayu ba, Amma ba yanda zasuyi dole Susama ransu hakuri Allah zai sake basu wani.

Haka suka dangana suka cigaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.

6anagaren khairat Kuma yau sati biyu kenan da tafiyar Sani kullum saita Kira wayarshi yafi a 'kirga Amma baya shiga, sakamakon 6acewar wayarsa lokacinda sukayi accident, hakan ba 'karamin damunta yakeba saboda haka yau ta yanke shawarar fita ko Allah zaisa taganshi kokuma taji labarinsa.

A waya takira Salim tagayamashi zataje gidan zuby, bai hanataba saboda haka tahau shiri, Khalid sai binta yake yana cewa mama Ina zuwa, Amma ko kallonsa batayiba tacigaba da shirinta.

Cikin wasu fitinannun riga da siket na wani had'adden material blue, sannan tadawo pink din gyale da pink din takalmi da jaka ta Sanya, kalaluwan turare tafeshe jikinta dashi, tafito daga sashenta Khalid sai binta yake Yana fad'in inazuwa, tureshi tayi tace "Kai kada kadameni ko kaga Ina fita dakaine, wuce can katafi wurinsu Hanif kayi wasa"

Sukuku yanufi sashen Fauziyya Yana hawaye, koda yaje baishigaba sai yatsaya 'kofar falon.

Haniface tafito daga falon taganshi, Kama Hannunshi tayi tace "Khalid waye ya bigeka? Momynka ce ko? Taho mutafi mu momynmu bata duka"

Binta yayi suka wuce d'akinsu, suka had'u da Hanif suka Fara wasa, cikin d'an lokaci Khalid ya manta da wani bacin rai.

Khairat kuma tana fita daga gidan Kai tsaye makarantar su sani tanufa gidansu na *ALMAJIRAI* ta tambaya ko yananan,
Nan suka sheda mata ai Sani yafi shekara biyu rabonsa da zama cikin wannan gidan.

Tambaya tayi ko sunsan inda yakoma, sukace gaskiya Basu saniba, da dai abokinsa Basiru nanan daya gayamata domin shine kad'ai yasani.

Haka tabar wurin ranta a dagule dan taso ace taga Sani yau, yanzu Kuma Ina zata nufa.

Napep ta tsaida tashiga bayan tagayamashi inda zai kaita suka d'au hanya.

Sani Kuma Yana tare da Zuby d'inshi dan tunda sukayi accident suka dawo baya fita ko Ina kullum Yana gida.

Zuby Kuma bata gajiya da abunda aka Saba, badare ba rana kullum aikin kenan.

Yauma Kamar kullum kwance suke Kan gado suna Raya saunnah, tunda aure ne sai dai muce raya Sunnah.

Lokacin khairat tashigo gidan tanata faman kwad'a sallama amma shiru ba'a amsaba, Zuby da Sani sunyi nisa sun Lula acikin duniyar ma'aurata.

Gajiya tayi da sallama tashiga falon bataga kowaba, bedroom tanufa batareda wani tunaniba.

Wata irin 'kara tafasa tareda dafe kanta da hannu biyu sakamakon mummunan ganin datayi tsakanin Zuby da Sani.

Baya tayi dagudu tana niyyar barin gidan, da sauri Sani yasa boxer yabiyo bayanta lokacin harta Kai bakin get tana Shirin fita yayi saurin ri'keta "khairat.... khairat.... Kitsaya mana, ki tsaya ki saurareni.

'ko'karin kwace hannunta takeyi tana kuka Kamar ranta zai fita " mezanji Sani ka cuceni ka kasheni da raina, ashe dama zuby kake nema..... innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un"

Wata irin tsawa Sani yadaka mata "ke dallah kirufama mutane baki, kiwuce mushiga daga ciki muyi magana kada kitara mana mutane.

Binshi tayi ciki, zuby Kuma tunda khairat takamasu jikinta ke 6ari tana fad'in "shikenan nashiga ukku na lalace, asirina yagama tonuwa yau nabani na lalace.

Suna shigowa tayi firi-firi da ita Kamar kicemata tak ta ranta ana kare.

Zama Sani yayi kan kujera yacema zuby tami'kamashi rigarshi, jiki na kyarma taje ta d'auko takawomashi yasanya.

Khairat na tsaye tana kallonshi, zuby Kuma ta'ki yarda su had'a Ido da khairat.

Sani ya kalleta yace "ki zauna mana"
"Zama, ai banga ta zamaba cikin wannan 'kazamin gidan, yanzu Sani miye baniyima mena rageka dashi amma bazaka iya ha'kuriba ka danne kwad'ayinka saika 'kara da Zuby, tafad'a tana kuka.

Sannan tacigaba da magana cikin masifa da d'aga murya "Sani kacika munafikin Maci amana, ka cuceni ka cuci rayuwata Allah ya isa kaci amanata.......

"Tassss kakeji ya d'auketa da wani lafiyayye mari, cikin tsananin huci da 6acin rai yace "akwai babbar Maci amana irinki Mai Zina da aure, munafika annamimiya, to Bari kiji in gayamaki zuby ba nemanta nakeba aurenta nayi"

Zaro Ido khairat tayi cikin tsananin firgici tace "Aure.....aurefa kace Sani, zubyn ka aura"
"Tabbas Aure" Sani yafad'a cikin gadara.

Dariya khairat tayi Mai Kama da ta6in hankali tace "to kasani Sani ka auri mutuwarka da kanka, muna zamanmu kaje ka kwaso mana 'kamaya-maya saikutashi mu d'unguma muje asibiti likita yayita aunamu Kamar yadi"

"Mi'kewa tsaye Sani yayi yace "ke dakata khairat bangane inda maganaki ta dosaba.....

Kafin yarufe baki khairat ta kar6e "to Zuby dai 'kanjamau kegaret.......

Kafin ta ida fad'i Sani yaji kanshi na juyamashi yafara gani wani duhu-duhu kawai sai gani sukayi yafad'i sume.

Zuby naganin haka tayo Kan khairat gadan-gadan tacimata kwala, tana fad'in "wlh idan Kika kashemin miji saina kasheki, muguwa."

Itama khairat kwalar Zuby taci tace "gakinan muguwa azzaluma kinsan kinada HIV Kika aureshi danki gogamashi.......

"Na aura d'in ba son abun duniya yakawoshiba, ko kinsan tsakanin aurenmu zuwa yanzu nawa nakashemasa...

"Koma nawa Kika kashemasa Ina ruwana, Nikuma dakika gogamawa ubanme Kika bani"
"Uban mi zanbaki kuwa, sakamakon daya dace dake ne wannan, kina nufin zakiyi bariki ki wanye lapiya, harma kisamu sakamakon samun miji Kamar Salim...

Wani mugun naushi khairat tayima zuby abaki, Nan take ha'korinta guda yacire jini yafara ambaliya.

Itama zuby dukan khairat d'in take, haka sukayita danben bala'i cikin gidan Babu Mai rabasu, ga Sani kwance a sume harta kanshi sukebi suna takawa wurin fad'a.

Kafin kace mi sunyima kawunansu muguwar illah, khairat tafi zuby 'karfi saboda haka zuby tafi jin jiki, sai dai wani mugun cizo da zubyn ta labtama khairat a kafad'a Wanda saida taciro tsokar wurin.

Kayan jikinsu Kuma sun yayyage sunyi fata-fata.

Sani dai Yana kwance rai hannun Allah,

Suma dasuka gaji da damben kowace zubewa tayi tana maida numfashi Babu mai iya tada wani cikinsu.

Azabar ciwon da bakin zuby keyi sakamakon fita da ha'korinta yayi shiyafi kome addabarta, rarrafawa tayi ta d'auko wayarta takira number Alhj Haladu wani abokin tambad'ewarta ne tagayamashi sunanan gida itada mijinta ba lafiya ya taimaka yazo yakaisu asibiti.

Minti ishirin Alhj Haladu ya iso gidan, yayi mamakin yanda yasamesu Kamar wad'anda sukayi wani mummunan had'ari.

Haka ya kwashesu yazuba mota yakaisu general hospital, akace baza'a kar6esuba sai anzo da police,

Ganin suna neman su jazamashi wata fitinar yasa yakaisu wata asibitin kud'i Nan aka kar6esu aka Fara Basu taimakon gaggawa, sannan khairat taro'ki likita dayayimasu awon HIV suduka,

Jininsu aka eba akaje lab, suduka sakamakon d'ayane suna d'auke da cuta Mai karya garkuwar jiki.
Chapter 34 · 0% Book details