← Book details Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 35

Sashe 3

Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.
sallama Salim din yayi tare da shigowa gidan, Fauziyya a inda take zaune ko motsawa batayiba ta amsa sallamar ciki-ciki,
Mamakine yakama Salim ganin yau Fauziyya batayimashi irin tarbar data Saba yimashiba, da sauri yanufi inda take ya ajiye jikkar hannunsa ya tallafota yahad'ata da jikinshi, haba my wife yau laifin menayi aka kasa tarbata kamar yanda aka Saba" kuka Fauziyya tafashe dashi ta kwace jikinta daga rungumar da Salim yayimata tashige d'aki.

Sani dake la6e a zaure Yana lekensu wani irin farincikine ya cika zuciyarshi ganin Fauziyya tayi fushi sa Salim.

Rarrashinta Salim yashigayi dukda baisan laifin dayayimataba, Bata kulashiba sai kuka datakeyi, da kyar yasamu ta tsaigaita kukan sannan tacemashi "Mama tazo d'azu Kuma tace tananemanka"
Ajiyar Zuciya Salim yayi, yanzu yagano inda matsalar take, wato duk yanda yake tausasa mama yana mata nasiha ashe batajiba saida tazo tagayama Fauziyya ba dad'i, dafe kanshi yayi yace "oh my God, Fauziyya kiyi hakuri nasan mamace ta batamaki Rai Dan Allah kiyi hakuri kada kisa damuwa aranki, zanje Kiran datakemin inshaAllah Kuma zannunamata rashin dacewar abunda tayimaki.

Haka Salim yacigaba da rarrashinta har aka Kira sallar isha'i tare sukafita suka d'auro Al'wala, Salim ma agida yayi sallar, ranar haka suka kwana sukuku, Dan duk yanda Salim yaso yaja Fauziyya da magana amma taki sakin jikinta dashi, dan bakaramin batamata rai mamar Salim tayimataba, kanta taji Yana saramata, tashi tayi ta dauko paracetamol ta balli guda 2 tawatsa baki tabi da ruwa, sannan tanufi wadrope ta d'auko kayan bacci wata rigace maisharara marar nauyi da siririn hannu ta sanya, sannan tahaye gado jikinta duk yamata nauyi.
[9/25, 4:31 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 5

*Gareki SAMIRA YUSUF wannan shafin nakine, naji dadi sosai akan yanda Kika fahimce yanda labarina yake dakuma sakon danakeson isarwa garemu mata, Kai harma da mazajenmu, Ina fata wannan labari nawa yazama IZNAH agaremu baki daya*

Washe gari
Misalin karfe 9 na safiya Salim yayi sallama gidan mamarshi, bayan sun gaisa yasamu wuri ya zauna cikin d'aya daga cikin kujerun dake dakin, Bayan sun gaisa Salim yace "Mama jiya Dana dawo gida Fauziyya tace kina nemana,"

D'aure fuska tayi kamar bata taba dariyaba, tace "eh nemanka nakeyi dan in gayamaka kasan yanda zakayi da wannan juyar matar taka wacce bata Haihuwa, nifa jikoki nakeso ingani dagwai-dagwai bi da bi amma har yanzu shiru, ba wani labari, to wlh bazan lamuntaba dole kasan nayi"

"Haba mama, dan Allah kidaina irin wannan maganar, baikamata ace kina irin wannan tunanin ba, duka shekararmu nawa da aure ne, da har za'afara Kiran Fauziyya juya, duka-duka shekara biyu ne, wasufa har shekara goma sukeyi basu Haihuba, Kuma bayan tsawon wannan shekarun idan sunada rabo saikiga sun haihu....

"Dakata Salim" tafad'a cikin d'aga murya da 6acin rai "Nizaka gayama duka shekararku biyu da aure, to a wannan shekaru biyun idanda ba juya bace da yanzu tayi haramar aje yaro na biyu, amma idayake juya ce Bata Haihuwa har yanzu shiru kakeji,
duk tabi ta kanainayeka ta mallakeka sai abunda tace kakeyi, bakason laifinta ko kad'an, shiyasa wlh tunda kazomin da maganar aurenta raina baisoba, dan dai idan Allah ya kaddara ba yanda mutum zaiyi"

"Nagodema Allah Hajiya dakikasan Aurena da Fauziyya Allah ne ya kaddara, to hakama Haihuwa tsakanina da ita idan Allah ya kaddara zamuyi kome dad'ewa....

"Kai dakata, banison zancen banza zancen wofi, tashi kabani wuri shashasha Wanda baisan inda aka dosaba, to kasani nabaku wata ukku muddin banji wani bayaniba 'karshen zamanka yazo da Fauziyya, dan wlh saika saketa, ehe"

Tana gama fadin haka tashige bedroom tabarshi zaune, yama rasa miye zeyi,
Haka yatashi jiki duk ba kwari yabar gidan.

Koda yaje wurin aiki kasa aiwatar da kome yayi, duk abun duniya yabi ya hademashi, ga Fauziyya taki sakin jikinta dashi tunda Mama tazo gidan, gashi Kuma mama tazomashi dawata irin magana marar makama, "wohoho" yafad'a tare da dafe kanshi.

Bangaren Fauziyya kuwa tunda tatashi takejin jikinta ba dadi, bakinta yayimata d'aci, ga tashin Zuciya dake addabarta,

Sani Kuma tunda yazo yafara wanke-wanke har yakusa gamawa Amma Fauziyya bata leko tsakar gidanba,
Ba karamar damuwa yashigaba, Dan rashin ganin Fauziyya ba 'karamin tashin hankali bane taredashi,

Tunani yacigaba dayi "ko lafiya, kokuwa dai tun abunda mamar Salim tayimata jiyane har yanzu bata huceba,, wata zuciyar tace "kashiga dakin kadubata Mana, wani bangaren Kuma na zuciyarshi yace "a'a kada kayi haka tunda dai matar nan har yanzu bata baka fuskar shigarmata dakiba.

Yana cikin wannan tunanin yaga Fauziyya tafito daga d'akinta da sauri, bakin maguji kusada inda Sani ke wanke-wanke ta durkusa tafara kwaraya amai, "subhanallah" sani yafada "Aunty dama bakida lafiya ne? Kasa ko d'aga Ido tayi ta kalli sanin kakarin amai kawai takeyi, tun tana amayo abunda taci harya kasance bakome cikinta dukta amayar amma dukda haka kakarin amai kawai takeyi, cikin 'kan'kanin lokaci dukta galabaita,

Sani Kuma rasa yanda zeyi da'ita yayi, shiba abun yatabataba, gashi Kuma tayi kwance wurin datayi aman, da alama batada 'karfin dazata tashi tabar gun.

Hankalin sani inyayi dubu yatashi, jiyake dayanada hali daya cirema Fauziyya ciwon dake damunta,

Can murya 'kasa-'kasa Fauziyya tace "sani kaduba falo kan kujera wayata nanan ka d'aukomin"

Da sauri Sani yanufi d'akin Fauziyya, bakin kofa yacire takalminshi sannan yashiga d'akin tsayawa yayi yana 'karema d'akin kallo dan duk yanda yake da gidan zai iya k'irga shigarshi dakin Fauziyya, hannu yasa ya d'auki wayar harzai fita ya kaimata wayar, kamar Wanda yayi mantuwar wani muhimmin abu saiya koma d'akin, bedroom yanufa Kai tsaye, yafara bin ko'ina na d'akin da kallo, idanunshi suka sauka kan rigar baccin Fauziyya dake yashe kan gado, data cire dasafe saboda rashin karfin jiki yasa Bata d'aukeba, hannu yasa ya d'auko rigar ya d'orata akan fuskarshi Yana sha'kar 'kamshin turarenta, yakai kimanin minti 2 ahaka kafin ya sauketa zuwa kirjinshi ya rungumeta Yana fad'in "Ina sonki Fauziyya Ina 'kaunarki, Ina fatan kasancewa dake har 'karshen rayuwata, Fauziyya nayimaki Al'kawarin sai kinzama mallakina kome wuya kome tsanani, ko ana ha maza ha mata saina mallakeka, haka yari'ka surutai kamar wani zautacce maganar Salim ce tadawo dashi hayyacinshi, zaro Ido yayi cikin tsanain tashin hankali ya juyo.

😅 *Tofah reader's Anya sani Bai d'ebo da zafiba kuwa*

*Hmm muje dai zuwa ai Hausawa sunce, KOWA YA DEBO DA ZAFI BAKINSA* 🤔
[9/25, 4:32 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 6

*JINJINA GAREKU YAN GROUP DIN ALMAJIRIN GIDANA NOVEL INA YINKU IRIN SOSAI DINNAN, IYA WUYA ANA TARE*

Saurin fitowa yayi daga d'aki Yana fad'in "Aunty ga wayar" juyowa Salim yayi ya kalleshi a kidemi Dan hankalinshi yagama tashi da ganin yanda ya iske Fauziyyar, karbar wayar yayi daga Hannunshi yace "Sani yi sauri kashiga gidan sister Firdausi ka gayamata Fauziyya batada lpy tazo Dan Allah ta dubata"
Da gudu sani yabar gidan zuwa gidan Firdausin, wata nurse ce makociyar Fauziyya duka gida ukku ne tsakaninsu.

Salim kuwa sani natafiya yataimakama Fauziyya ta wanke jikinta sannan yakaikta d'aki yadawo ya wanke inda tayi amai,

Mintuna dabasu wuce bakwaiba Firdausi tashigo gidan itada Sani, Kai tsaye d'akin Fauziyya tanufa kwance ta isketa tana numfashi sama sama ga wani 'katon bargo data rufa dashi, dan wani masifaffen sanyi takeji sakamakon Zazzafan zazzabin daya saukomata.

Dubata fidausi tayi tare dayimata wasu tambayoyi,
fitsari tasa Fauziyyar tayi tayimata PT sanan tadawo d'akin fuskarta d'auke da murmushi, ta dauko biro da wani takarda tafara rubutu, bayan ta kammala tajuyo ta kalli Salim tace "congratulations Salim, kakusa zama Daddy, Dan Fauziyya tana d'auke da ciki"

Zaman dauri sani yayi a inda yake, sakamakon abunda kunnuwansa suka jiyomashi, Dan tunda fiddusi tashigo yake sauraren abunda ke wakana dangane da rashin lafiyar Fauziyya, inda akayi rashin sa'a yafad'a kan wata roba wacce Nan take ta tarwatse, daga d'aki faiddusi taleko ta window Jin karar abu na fashewa, gagnin sani tayi zaune duk ya had'a gumi Kuma yakasa tashi daga kan robar daya fadamawa dukda kwalleliyar ranar dake wurin, saboda tsananin firgicin dayake ciki.

Salim kuwa cike da farinciki yad'aga hannu sama Yana godema Allah, koba kome Allah yakawomashi 'karshen rigimar mamarshi, yauga Fauziyya d'auke da cikinshi.

Takarda fiddausi tami'kamashi tace "ayi hanzari asawo wannan magungunan tafara sha inshaAllah zata samu sauki"

Karbar takardar yayi yafito tsakar gidan da niyyar yaba sani yaje chemist yasiyo maganin danshi bayaso yayi nesa da Fauziyya saboda yanda dukta galabaita.

Inda sani yafad'i har yanzu Nan yake baitashiba, kallonshi Salim yayi yace "Kai sani, wai kai wane irin sakarai ne?"

Tashi yayi da kyar yace "wlh fad'uwarce najita shiyasa nakasa tashi, ya jikin auntyn? Yatambaya Yana gyara tsayuwarshi,

"Da sauki" Salim yafad'a, sannan yace "anshi wannan kaje chemist kasiyo wannan magungunan" yafada Yana mikamashi takarda da kudi,

Amsa sani yayi yafita daga gidan Yana layi kamar wani mashayi, haka yafara tafiya Yana tangadi kamar Wanda yasha yabugu, duk tsabar damuwace, Shi yanzu takaicinshi dayane ba biyuba, yanda zaiyi yaraba Fauziyya da cikin jikinta.

Gindin wata bushiya ya zauna Yana tunanin yanzu miye abunyi, "dole insan yanda zanyi da cikinnan yazama dole yazube, taya zanyi in zubar mata dashi?" Tamabayar dayayima kanshi kenan wacce yakasa bama kanshi amsarta.

Yakai kimanin mituna goma awurin kafin dubara tafad'o mashi, da sauri yatashi fuskarshi d'auke da murmurshi Dan tunowa dayayi da chemist din kolo, wani chemist ne na wani Christan Mai suna kolo, Wanda Almajirai masu shaye-shaye ke siyen kayan maye wurinsa, can yanufa Yana zuwa yayi sa'a bakowa a chemist din sai kolo Shi d'aya, bayan sun gaisa yace kolo dama wannan magungunan zaka bani yafad'a tare da mi'kamshi takardar, amsa yayi sannan yafara d'auko maganin, saida yagama hadawa yamikamashi yace "kud'inka 450"
Chapter 3 · 0% Book details