← Book details Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 35

Sashe 18

Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ture khairat yafarayi yanamata wani mugun kallo, yace "ke lafiyarki kuwa, miye haka"
"Banida lafiya Sani, kataimaka kabani magani"
Tureta yayi daga jikinshi yace "ni banida maganin dazanbaki kije asibiti adubaki"

Can murya 'kasa-'kasa tace
"Sani ka fahimceni mana, ciwona bana asibiti bane, Kuma kanada maganinsa Sani inaso kabiyamin bukatata konawa kakeso nama Al'kawarin zanbaka, kome kakeso zanyi, plz help meee.....

"Dakata khairat, nagama fahimtar duk abunda kike bu'kata agareni, Kuma batun yauba nake lura da take-takenki a kaina cikin gidannan, bazaki ta6a samun biyan bu'kata daga gareniba khairat, mi kike tunanin zaifaru idan Salim yakamani inacimasa Amana"

"Bazai ta6a kamakaba, Sani kayarda dani Dan Allah Koda sau d'ayane kayimin, wlh Ina cikin matsanancin Hali nakai 'kololuwa wurin sha'awa, Salim ya'ki ya kawarmin da ita"

"Ke dakata khairat" Sani yafad'a cikin d'aga murya.
"Bazaki taba samun abunda kike nema agareni ba, ashe dama 'karya kikeyi babu wani 'kadangaren dayashigo d'aki wata manufar tasa kikayi ihun 'kadangaren"

Yana gama fad'in haka yanufi 'kofa Yana Shirin fita,
Saurin Shan gabanshi khairat tayi a kidemi idanunta sun canja launi tsabar jaraba, tace

"zakayimin ta arziki kokuwa bazakayiba?"
"Bazanyiba, Kuma bakida yanda zakiyi dani"
"Niko keda yanda zanyi dakai Sani, ka tabbatar idan bakiyiminba yau saika bar gidannan, dan bazaiyiyuba amatsayinka na *AL'AMARIN GIDANNAN* har innemi wani abu daga gareka ka hanani"

Gaban Sani yafad'i jin khairat tace zaibar gidan, amma saiya dake yayita maza yace
"Nifa bari ingayamaki abunda baki saniba khairat, tunda kikazo gidannan nakejin haushinki natsaneki, da inada hali wlh sai kinbar gidannan"
"Haushina Kuma sani, meyayi zafi haka kakejin haushina?"

"Saboda abunda kikema Fauziyya, tunda Nike a duniya banta6a jin son wata maceba sai Fauziyya, Kuma bantaba sha'awar wata maceba bayanta, kaina nayimata tanadi, saboda haka Nina Fauziyya ne, Kuma inanan Ina jiran ranarda Salim zai sakarmin ita in Aura,
Kekuma nafarajin tsanarkine daga ranarda Kika Fara batama Fauziyya rai, banison bacin ranta, duk kuwa Wanda yasakata bacin rai bani tare dashi"

Yana gama fad'in haka yazagayeta yafice daga d'akin yabarta tsaye sokoko kamar wata sakarai, magan-ganunshi sunamata yawo akai, Son Fauziyya yakeyi, tabb babbar magana, tunda Uwar data haifeni bantabajin labari makamancin wannan ba, *Almajiri da son Matar gida* to kodai itama suna aikata wani abu ta bayan fage bansaniba.

Zama tayi bakin gado ta tallafe fuskarta da hannu biyu, "lallai Fauziyya kinshiga gabana dayawa, kinhanani Salim sannan Kuma kin hanani Sani, to wlh bazan barkiba saina d'auki mummunan mataki akanki, kaikuma Sani nayi Al'kawarin saina sameka Kota halin 'ka'ka, ni khairat zaku nunama duniyanci daga Kai har Fauziyyar sai nayi maganinku"

Bedroom tashiga ta d'auko wayarta number zuby ta lalubo ta danna mata Kira, ringing d'aya zuby tad'aga takara a kunne "Hello 'kawata inji good News"
"Yanzu dai bazakiji good news ba sai dai kiji bad news" khairat tabata amsa, Nan takwashe duk yanda sukayi da Sani tagayama zuby, dariya zuby tayi irin tasu tayan duniya tace Amma khairat kinabani mamaki, Wai yaushe kika canja ne daga khairat d'inda nasani, kecefa ke Jan maza a'kasa, Amma yanzu mazane ke janki a 'kasa, kinkasa Jan ra'ayin Salim, shima Almajirin naki ya gagareiki why"

"Amma kada kidamu kinsan abunda za'ayi?"
"Sai kinfada"
Cigaba da magana zuby tayi khairat tana saurarenta tana murmushi da alama maganar tayimata dad'i.
"To shikenan haka za'ayi, sai munzo d'in" khairat tafad'a taredayin sallama da zuby sannan ta tsinke Kiran ta ajiye wayar.

Har yanzu magan-ganun Sani kemata yawo a kwakwalwa, Wai son Fauziyya yake, "hahahaha khairat tayi dariya dan abun yamata Suger, Kuma itama zatayi amfani da damarta ta dama.

Fauziyya tunda takoma d'aki Bata fitoba sai yanzu dataji sallamar mamar Salim, khairat ma sallamar mamar ce tafiddota sai wani ciccin magani take,

Sannu dazuwa Fauziyya tayima Mama ta amsamata a wulakance,

Khairat Kuma gyara d'aurin d'ankwalinta tayi taturoshi gaban goshi, ta d'auko kujera ta ajiye tsakar gidan tace mama Bismillah zauna mana.

Kallo mama tabita dashi "mushiga daga ciki mana khairat, magana zamuyi baniso asakamana Ido kina ganin wannan Mai idanun kamar na mujiya ta tsaya ta zuba kunnuwa tana jiran taji mezan fad'a"

Dariya khairat tayi tace "kada kidamu mama, nida ita ai duk d'aya muke a gurinki, inace muduka matan d'ankine"

"Wasu matan ai suna suka tara, me akeyi da macenda batasan arziki ba, tunda ai rashin sanin arzikine Allah ya azurtaka da ciki ka zubar"

"Bangane mi kike fad'aba Mama" khairat tayi maganar tanason Jin 'karin bayani.

Dama abunda Mama ke nema, ta gyara zama ta kwashe labarin Fauziyya duka tagayama khairat, sannan tadad'a da cewa Kinga gayanan yanzu ana neman haihuwar ruwa jallo anrasa, ai Allah ba abokin wasan mutum bane dazai baka kayi watsidashi Kuma daga baya kadawo kace kanaso"

Dariya khairat tayi, tadafa kafad'ar Mama tace kada kidamu Mama ni zan haifamaki jikoki ko guda nawa kikeso a gidannan" tafad'a tana kallon khairat tana wata shu'umar dariya.

Shigewa d'aki khairat tayi dagudu, tafad'a kan kujera idanunta na zubarda hawaye, d'aga hannu tayi sama tace "ya Allah ka azurtani da Haihuwa kodan inhuta da ba'kin cikin mamar Salim, Allah ka tausayamin ka fiddani halinda nake ciki"

Tana daga d'aki amma tana jiyo duk hirar Mama da khairat tun sunayin na hankali har abun yazama kamar wasu tababbu, dan dariya suketa 6abbakawa, har kashewa suke, dan khairat batawani ganin girman mama, ta gama raimata wayo.

Saida sukayi Mai isarsu sannan Mama tami'ke sukayi sallama khairat tace "agaida gida mama" "to gida zaiji" tafad'a tana fita daga gidan.

Khairat Kuma d'aki tawuce zuciyarta cike da farinciki Dan yau ranar sa'a ce a rayuwarta Dan tasamu lmpomation sosai akan Fauziyya, daga wurin sani dakuma mamar Salim, zatayi amfani da wannan damar tabiya duka bu'katunta, ciki Kuma harda mallakar Sani da Salim, dan tayi Alwashin suduka sai sunzama abun biyan bu'katarta.

"Wayyo Allah nashiga ukku..... Tafad'a tana matse 'kafa, dan har yanzu maganin Laure agyara yanata aikinshi, idan abun ya motsa sai dai tayita mutsirniya tana mid'iddika kan gado ita kadai, yanzuma hankalinta yayi 'kololuwa wurin tashi, wata irin matsananciyar sha'awa ta bijiromata.

Saida tagama juyi kan gado idanunta sunyi ja tsabar jarabar dake addabarta, sannan tatashi tashiga toilet tashe'ka wanka, tana fitowa gaban mirror tatsaya ta ca6a kwalliya, wadrope tanufa tadauko wasu kaya atamfa d'inki doguwar riga pieces tasanya sannan takashe d'aurin d'ankwali ture kaga tsiya, amabaliyar turare tayi a jikinta mayafi ta d'auko tayafa sannan ta d'auko wasu plate shoes ta zura kafafunta, sai poss dinta data rike a hannu, d'ayan Hannun Kuma wayartace,

Wayar ta daddana ta lalubo number Salim tadokamashi Kira tanata ringing harta tsinke bai d'agaba, sake kiratayi nanma Bai d'agaba, saida tayimashi Kira hud'u no answer, text ta turamashi _Slm nakira waya baka d'agaba dama zan tambayeka zanje gida in gaida mama dan nayi missing dinta two days_

"Ok" shine abunda Salim ya maidomata reply,
"Dan rainin hankali ashe yana ganin kirana ya'ki dagawa, damuwarkace wannan danni tawa matsalar takusa zuwa 'karshe.

Fitowa tayi tajawo d'akinta tasa key tarufe tasaka key din jaka tafice daga gidan batareda tayima Fauziyya sallamaba...

Tana fita bakin titi tatsaya tafiddo wayarta tana Shirin Kiran number Sani, saita hangoshi Yana tahowa dan lokacin zuwanshi yayi dama bayan azahar yake zuwa cin abincin rana, sauke ajiyar Zuciya tayi ta maida wayarta jikka, murmushi tarikayima Sani harya karaso inda take, Yana Shirin wucewa tace "jimana" juyowa Sani yayi, tace "idan bazaka damuba kazo karakani unguwa mana"

"Gaskiya bazan samu zuwaba dan yunwa nakeji"
"Kada kadamu akwai abunci acan sai Wanda kakeso zakaci, sannan akwai magana mai muhimmaci danakeso muyi dakai"
"Badai wannan maganar bace dan idan itace bazan taba amincewa dakeba, karama kawai kibarni kiyi tafiyarki dan bazaki samu biyan bu'kata ta wajena ba"

"Ba wannan bane kaidai zo muje zakasamu Alkhairi"

Napep ta tsaida, tacema sani "bissmillah shiga" tafad'a tana nunamashi 'kofar napep din, bamusu yashige, itama shigewa tayi, dai-dai lokacin Salim yazo kan mashin Kuma kamar yaga shigar wani a napep din kafin khairat d'in,

Jan napep din akayi akatafi, shima Salim Jan mashin dinsa yayi yabi bayansu.....

*'ka'ka 'Kara 'ka'ka, ga Akuya ga kura* 😳

Mmn khady ce 🏃🏻‍♀
[9/25, 4:32 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 26

Suna a napep suna tafiya, Salim Kuma Yana binsu a machine dinsa, kusan minti goma suna tafiya, rage gudu Salim yayi, zuwa can Kuma saiya juya kan mashin d'in yakama hanyar zuwa gida, a zuciyarshi yace "banga amfanin inkama binsuba, duk inda zataje tatafi ba damuwata bace, wancan Kuma danaga yashiga maybe wani passenger ne aka Fara d'auka, Kai koma dai miye can ita tasani......

Juya akalar mashin dinsa yayi zuwa hanyar gida, sannan Kuma ya fidda duk wani tunani daga ranshi, dan baiga abunda zaisakashi tunanin abunda bayaso ba, Kuma bayason kasancewa dashiba.

Khairat da Sani Kuma tafiyar kusan minti ishirin da biyar yakaisu inda zasu, unguwar irin G R A dan tsit take babu yawan mutane, 'kofar wani had'adden gida suka sauka, pentin gidan dark pink daga waje, sai shuke-shuken flower's dasuka 'kara 'kawata gaban gidan, gaskiya gidan ya had'u ba 'karya, daga wajema kenan inaga anshiga ciki Kuma.

Kud'i khairat ta fiddo ta sallami mai napep, sannan tanufi gate d'in gidan Sani na biye da ita,

Tura get d'in tayi tashiga, shima Sani shiga yayi amma duk a tsorace yake, sai yanzu yake tambayar kanshi wai miyasama yabiyo khairat wannan gidan bayan yasan kudirinta akanshi, jiyayi kamar yayi baya dagudu amma saiya daure yacigaba da binta, fad'uwar gaba asarar namiji.

Sallama khairat tayi batajira an amsaba takutsa Kai cikin falon, kamar yanda tayi haka shima Sani yayi, zuby ce zaune kan d'aya daga kujerun falon taci wani uban kwalliya kamar mai Shirin zuwa gidan biki, takashe d'aurin d'ankwali ture kaga tsiya, gabanta tukunyar shisha ce tarike tiyo d'in tana zu'ka tana feso hayakin tabaki cikin kwarewa, da tsabar duniyanci.

Cikin fara'a zuby takemasu sannu da zuwa,
Khairat zama tayi kusada zuby ta karbi tiyo d'in shisha tacigaba da zu'ka.
Chapter 18 · 0% Book details