← Book details Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 35

Sashe 25

Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mmn khady ce 🙏🏻
[9/25, 4:32 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 35

*Cigiya Cigiya Cigiya, Jama'a ina cigiyar Maman twowins kwana biyu banji comment d'inkiba, Allah sa dai lafiya kike, nayi missing d'inki irin sosai d'innan, khairat da Sani ma sunce in gayamaki sunyi miss dinki*..

*Gaisuwa gareku naji dad'i dakuka kasance cikin tarin masoyana*
Mmn Abdul
Ashfaty
Ummu Aimana
Mmn Mash'hud
Dakuma *Asiya (Muneefa)* inayinki sosai da sosai.

Suna dawowa gida Aunty Safiya takira Mama a waya ta sanar da ita Fauziyya nada ciki, hamdala Mama tayima Allah tace "yau Allah yakawo 'karshen Zarginda Salim da mahaifiyarshi sukema Fauziyya, ashe dama da cikin akayi sakin, Allah kenan maiyin yanda yaso, a duk lokacinda yaso"

Baban Fauziyya ma da'aka sanar dashi yayi matukar farinciki, koba kome yasan sanadiyyar cikinda Fauziyya ke d'auke dashi zata koma gidan mijinta.

Fauziyya kuwa tanajin sanda Aunty Safiya takira Mama tagayamata wani irin farincikine ke Kara lulle6eta, wai yau itace d'auke da cikin Salim, Shafa cikinta tayi Wanda bazaka ganshi kace akwai ciki na wata hud'u ba, tace Allah nagodema koba kome nasan Salim zai Gane banida masaniya akan abunda yake tunanin na aikata.

Tunanin yanda zatayi ta 'karbi wayarta daga Hannun Aunty Safiya take tagayama Salim kyakkyawan Albishir amma tanajin nauyin tambayar ta wayar.

*Bayan sati biyu*

Aunty Safiya zaune falo tana yankema walida farce, Fauziyya tashigo da sallama, sanye take cikin wata ba'kar doguwar Riga, irin na larabawan Dubai, tayi rolling da mayafin rigar, tayi matukar yin kyau, ga wani irin haske mai sheki da fatar jikinta keyi, tayi luf da ita kamar balarabiyar.

Amsa sallamar Aunty Safiya tayi, wuri Fauziyya tasamu ta zauna kan daya daga jerin 'kawatattun kujerun dake d'akin tace "washhh Allah Aunty nagaji sosai, ni wlh jinake kamar na daina zuwa awo d'innan, wlh duk ranar danaje da ciwon kai nake dawowa"

Harararta Aunty Safiya tayi tace "ki daina zuwa awo saboda kina raguwa ko, ke kullum Kara ragwanci kikeyi kamar kanki farau ciki, to wlh idan Zaki saki jiki kidage kisaki, idan Kika koma gidanki yazakiyi da aikin gida, kohaka Zaki ri'ka langabewa, bakisan anaso mace mai ciki tari'ka motsa jikiba, (exercise) hakan ba 'karamin amfani gareshiba, ko Haihuwa kikazo zakiga kin haihu cikin sauki da yardar Allah"

Yanzu kitashi kije ki watsa ruwa zakiji gajiyar taragu, kizo kici abinci wayarki nanan nasakamaki charge saiki d'auko"

"To aunty" Fauziyya tafad'a tanufi d'akinta cikin zumud'i da farinciki, aranta tanacewa Salim shine mutum na farko dazata Fara Kira, yau zataji muryar Hubby d'inta masoyinta, iya tsawon lokacin data d'auka bata tare dashi bakuma tajin muryarsa Koda a waya, ba 'karamar azabtar da zuciyarta hakan yayiba, Dan dai ba yanda zatayi dole ta daure tabi nagaba da itane, ammafa ta azabtu iya azabtuwa.

A bangaren khairat yau tatashi da wani irin zazzabi da ciwon kai, ga wani irin kasala dake addabarta, tun tana daurewa har dai taji bata iyawa duk da tasan dalilin rashin lafiyar nata,

Rasa inda zata sanya kanta tayi gashi Salim tunda Fauziyya tabar gidan baya kulata,

sunan dai suna gida d'aya Kuma tana matarshi amma babu wani abu dazaka gani tsakaninsu Wanda zai nunama itada Salim mata da miji ne.

Daurewa tayi ta lallaba tanufi d'akin Salim dukda jiri dake d'ibarta, da sallama tashiga d'akin, amsa sallamar yayi batareda ya kalli inda takeba.

Zama tayi gefen gadonshi cikin murya 'kasa-'kasa irinta marar lafiya jikinta na kyarma tace "Dan Allah Salim ka taimaka ka kaini asibiti wlh tunjiya banyi bacciba Ina fama da matsanancin ciwon Kai"

'dagowa Salim yayi ya kalleta, yaga yanda tarame sai wani uban fari data 'kara, idanunta duk sun fad'a, kana ganinta zaka tabbatar da tsananin azabar ciwon dake addabarta.

Take yaji wani irin tausayinta yadira azuciyarshi, yace "kije ki shirya inkaiki asibiti"
"To" kawai tace tanufi d'akinta, jim kad'an saigata tafito sanye da wani makimancin hijab, kallo Salim yabita dashi dan tunda yake da khairat yasanta baitaba ganinta da hijab ba, tun kafin tayi aure har yanzuma datayi auren batasa hijab, shi baimayi tsammanin za'a samu hijab cikin kayantaba.

Kan mashin d'insa ya d'auketa suka nufi asibitin.

Suna Isa suka yanki Kati sannan sukaje office din likita.

'yan' tambayoyi yayima khairat tana bashi amsa, inda Kuma taga akwai 'karin bayani tayimashi, siring yasa ya zu'ki jininta yakira wata narse yaturata Lab ayi gwaji, bayan minti ashirin tadawo d'auke da takardar sakamako.

Marar gaskiya ance ko cikin ruwa ji6i yake, hakane kuwa ya kasnace da khairat, dankuwa tunda narse d'in tashigo da takardar sakamakon gwajin jikinta ke kyarma, Amma tana 'ko'karin dakewa dan gudun kada Salim ya fuskanci halinda take ciki.

Amsar takardar likita yayi yasaka farin glass d'inshi yagama dubawa sannan yad'ago ya kalli Salim fusakarshi d'auke da murmushi yami'kama Salim hannu sukayi musabuha, yace "Congratulations, Ina tayaka murna matarka na d'auke da ciki....
Wani muguwar fad'uwar gaba khairat taji, had'eda firgita.
Cigaba da magana likitan yayi, "ciki na tsawon wata hud.....

Kafin likitan ya'karasa fad'in abunda zaifad'a khairat tafasa wata uwar 'kara tareda durkushe inda take tana dafe cikinta, tana fad'in wayyo cikina....zanmutu.. wayyo Salim zanmutu.

"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Salim yafad'a doctor dan Allah taimaka mana, yafad'a Yana ri'ke khairat wacce keta faman magowa tana ri'ke cikinta...

(Oh ni su khairat an iya pretending)🤔

Da sauri likita yakira wannan narse d'in aka Kama khairat aka d'orata kan wani gado dake cikin office d'in, wata Allura likita yayimata kafin ad'auramata drip, bacci kuwa yayi awon gaba da ita.

Ganin tayi bacci yasa Salim fita daga office d'in ya fiddo wayarshi cikeda farinciki yakira number Mama yasanar da ita halinda khairat take ciki, zokaga murna wurin Mama, hada taka rawa, suna gama waya tahau Shirin zuwa asibitin.

Salim fa bakinshi yaki rufuwa saboda farinciki, dan shima yanaso yaga kwanshi a duniya, amma yaso ace wannan cikin tareda Fauziyya ne.

Amma ko khairat d'inma yayi farinciki Ashe dama rabone yasa haka yafaru tsakaninsu sau d'aya tak har ansamu rabo, Allah kenan.

Aifa Kuma sai tunanin Fauziyya yadawomashi sabo fill, dukda dama kullum da tunaninta yake kwana dashi yake tashi.

*Kuyi manage da wannan muhad'u gobe inshaAllah dan jin Yaya zata Kaya tsakanin Mamar Salim da khairat, akwaifa bada'kala*

Mmn khady ce 🤦🏻‍♀
[9/25, 4:32 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 34

*Kunata cigiyata inaji abaya nagayamaku munada matsalar NEPA saina Kai charge nabiya kudi kafin inyi typing, to jiya mai charge din nawa bayanan shiyasa kuka jini shiru, nagode da yanda kuka damu da rashin jina dakukayi masoyana, kunata jajena musamman Yan group Dina ZEE MMN KHADY FAN'S nagode Allah bar zumunci*

Bangaren Salim tunda yafita daga gidan bai 'kara waiwayarsaba saida dare, abunda yabashi mamaki shine har yanzu Fauziyya Bata dawoba, hankalinshi ne yatashi sosai.

'dakinshi yawuce ya zauna Yana tunani kala-kala, "Ina Fauziyya tatafine haka, agogon wayarshi yaduba 'karfe tara da minti talatin da takwas, gabanshine yafad'i, ranshi yafara bashi duk inda Fauziyya take babu lafiya.

To yanzu waye zai tunkara yace Yana nemanta, ga kuma wata irin fitinanniyar yunwa dayakeji rabonshi da abinci tun na safe, gashi bayaso ya tunkari khairat tunda yaga take-takenta na rashin kunya, da rashin tarbiyya.

Mukullan d'akin Fauziyya yad'auko yanufi d'akin yabud'e kitchen yashiga yahad'a ruwan zafi yasha tea dan shikad'aine abunda zai iya had'awa Wanda zeyi saurin korar yunwar dake addabarsa.

Saida yagama yafito zaibar d'akin saikuma yaji Yana mararin Zama cikin d'akin, 'kakmshin dake tashi cikin d'akin yayimashi matukar dad'i.

Zuciyarshi tabashi shawarar kawai yajira anan yaga lokacinda Fauziyya zata shigo, Kuma yau saita gayamashi inda tafita takai wannan daren batareda saninshiba.

Kishingid'awa yayi kan kujera 3 seater ya fiddo wayarshi yakira number Fauziyya Amma switch off, cike da takaici ya jefar da wayar kan kujera, tsakanin lokacinda yadawo gida darana yatarar da Fauziyya batanan zuwa yanzu yakirata yakai sau talatin Amma duk amsa d'aya akebashi shine wayarta akashe yake.

Yana nan har 'karfe Sha d'aya da minti 40 yafara gyan-gyadi bacci na neman kwashe shi, tashi yayi yabud'e bedroom dinta yashiga, gabanshi ne yafad'i ganin d'akin hargitse ga Babu trolley guda cikin jerin akwatunan Fauziyyar, sannan ga Kaya duk an fiddo daga wadrope da alama an d'ebi wasu kaya, hankalinshi ne yatashi yashiga tunani kala-kala, zuciyarshi kawai tabashi yaje gidansu Fauziyya yaga ko tana can.

"Ba shakka tana can, may be, gajiya tayi da abunda nakemata tayi tafiyarta, aiko yazama wajibi agareni inje in rarrashi matata tadawo mu manta da duk wani sabani damuka samu mu zauna mucigaba da baiwa junanmu kulawa.

Tashi yayi yakoma d'akinshi yacanja Kaya, sannan yafito yahau mashin d'inshi yanufi gidansu Fauziyya baiko kula da yanda dare ya tsalaba, unguwar duk tayi tsit bakajin motsin kome sai kukan karnuka da beraye da gyare saboda su lokacinsu ne.

Yana Isa 'kofar gidan yayi tsaye kan mashin d'in bai saukaba dan yama rasa ta Ina zai bulloma al'amarin, yakai kimanin minti biyar sannan yayi tamaza yasauka a mashin d'in yafara kwan-kwasa kyauren gidan.

Maman Fauziyya ce tafara jiyo bugun kofar, tada mai gidan tayi tace "Alhaji tashi kaji jinayi kamar ana buga 'kofa"

Saurarawa sukayi suduka, tabbass nan ake bugawa tashi baban Fauziyya yayi yasaka jallabiya yazura silifas yafito, itama maman Fauziyya hijab tasaka saman doguwar rigar baccinta tabiyo bayan maigidan nata dan Jin lafiya.

Tsayawa baban Fauziyya yayi daga zaure yace "waye" saida gaban Salim yafad'i kafin ya amsa da "nine"
"Kaine wah?" Baban Fauziyya yakuma tambaya
"Salim ne"

Bud'e 'kofar baban Fauziyya yayi dan ya d'auki murya.
Durkusawa Salim yayi ya gaidashi, ya amsa a dakile, sannan yace "lafiya naga kazo cikin wannan talatainin dare haka?"

"Eh to, da sauki dai baba, dama zuwa nayi inji ko Fauziyya tazo nan?"

Shiru baban Fauziyya yayi jin tamabayar rainin hankalinda Salim kemashi, tunda in banda rainin hankali yaushe zaka rubuta takardar saki kaba yarinya Kuma kazo gidansu kari'ka tambayar Wai tananan" to idan batanan gidan waye zata.
Chapter 25 · 0% Book details