← Book details Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 35

Sashe 24

Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amsar takardar Mama tayi ajikinta na kyarma takaranta, tana gamawa ta rafka dogon salati, "garin ya haka yafaru nashiga ukku"

Tashi tayi ta d'auko wayarta number baban Fauziyya takira bugu d'aya yad'aga "sallama tayimashi Yana amsawa tace "Alhaji kazo gida yanzu ba lafiya.

Babn Fauziyya Wanda ko minti goma baiyi da barin gidanba, yadawo hankali tashe.

Khairat da Sani kuwa Fauziyya nabarin gidan suka fashe da dariya suka tafa, Sani yace "gaskiya khairat ke shu'uma ce ko alahira wutarki dabance"

Hararshi khairat tayi tace "idan 6era nada sata daddawa ma da wari, kin wutar Kai kana 'kasana"

"Mubar wannan maganar dai yanzu nidake duk biyan bukatarmuce, Wai ya abun yafaru"

Saitin kunnenshi khairat takai bakinta ta rad'amashi, dariya sukayi suduka.

Sani yace "amma baki tunanin za'a iya agane ba rubutun Salim bane"
"Bani wannan tunanin haka, dan wanda yayi rubutun ya kware a wannan harkar, dan wlh ko sign d'in mutum yakalla yayi irinsa anyi kad'an ace ba maishi yayishiba"

*To waini miye khairat tarubuta jikin wannan takardar, kudai kubiyoni dan jin yanda zan war-ware maku zare da abawa*

*Kuyi manage da wannan, maybe gobe bazakujiniba saboda inada wata 'yar hidima, amma idan Naga da Hali zanyimaku koyaya yasamu*

Mmn khady ce 😩
[9/25, 4:32 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 33

Baban Fauziyya hankali tashe yashigo gidan, dan dagajin kiran da akayimashi yasan bana lafiya bane.

Ganin Fauziyya dayayi ga idanunta sun kumbura sunyi suntum, bayan canja launi dasukayi zuwa ja, gabanshi yafad'i yasan ba lafiya.

Karasowa yayi inda suke yace "lpy mike faruwa haka?"

"Inafa Lpy Alhj, kaduba kaga yaronnan saida yasaki Fauziyya baccin duk irin zaman hakurin datake a gidanshi" tafad'a tana mi'kmashi takardar, karba yayi yaduba "gurgiza Kai yayi Zuciyarshi cike da takaici yace "Allah sa haka shine yafi zama Alkhairi" dukda hakan baimashi dad'iba ko kad'an.

"Ameen" maman Fauziyya ta amsa sannan tace "Amma Alhj inada wata shawara, tunda dai haka yariga ya kasance Kuma kaga duk halinda yarinyar nan take a gidanta Babu Wanda bamu saniba, tundaga tsangwamar da mahaifiyar yaronnan kemata har zuwa 'karin auren dayayi, mai zai hana tad'anyi nesa da garinnan Kota samu tahuta.

Shiru baban Fauziyya yayi sannan yace "Ina kike ganin zata tafi?"

Mai zai hana tatafi Abuja gidan 'yar'uwarta kafin muga abunda hali zaiyi"

"To shikenan saiku kirata kuyimata bayani kafin tatafi ko"

Bayan fitar baban Fauziyya, mama takira Aunty safiya yayar Fauziyya wacce ke aure Abuja tagayamata abunda ke faruwa da 'yar'uwarta a gurguje tace yanzu zata taho nan, idan tazo zakiji sauran bayani daga wurinta.

"To saitazo, da haka sukayi sallama, kallonta mama tayi tace maza tashi kid'au hanya baniso ki Kara awa daya a cikin garinnan.

Tashi Fauziyya tayi jiki a sanyaye ko kad'an bataso tayi nesa da Salim, Amma bazata iya tsallake maganar iyayentaba, Kuma tunda shi Salim din bai San darajartaba har ya iya rabuwa da ita dole itama zata daure tarabu dashi komin irin tsananin sonda takemashi.

Tana kuka tafita gidan, napep ta tsaida yakaita tasha, cikin sa'a kuwa ta tarar saura mutum d'aya golf din tacika, tana shiga suka d'au hanya sai birnin tarayya (Abuja).

Bangaren Salim kuwa tunda yaje wurin aiki haka kawai Yana zaune sai yaji gabanshi na fad'uwa.

Salati kawai yakeyi duk lokacinda yaji faduwar gaban, ranar haka ya wuni sukuku baiyi wani aikiba har lokacin tashi yayi, haka ya tattara iyayen takardun dake gabanshi yabar office d'in.

Tafiya yake kan mashin dinsa, tunda yadoso gidan yakejin fad'uwar gabanshi na tsananta yarasa dalilin.

Ahaka ya isa gidan da sallama yashiga, khairat na zaune kan kujera ta ca6a wata irin kwalliya kamar mai Shirin zuwa biki, tasaka wata matsiyaciyar doguwar riga ta wani tsadadden less takashe d'aurin d'ankwali kamar mai Shirin zuwa gasar zaben sarauniyar kyau
hankalinta kwance

Tanajin sallamar Salim ko kallon inda yake batayiba barantana ta amsa sallamar, saima cigaba datayi da taunar cingum dinta tana wani 'kas 'kas dashi abaki.

Wani mugun kallo Salim ya watsamata sannan yawuce d'akinshi, baima lura da d'akin Fauziyya dake rufeba.

Saida yasheka wanka ya canja kaya, kusan minti goma Yana jiran shigowar Fauziyya yaji shiru.

Wayarshi ya d'auko yaruba Text massage yaturama, shiru kusan minti ishirin da tura massage din amma baiga tazoba.

Tunani yafara a zuciyarshi kodai Fauziyya tagaji da yanda yake shareta itama tayi wuri ta ajiyeshi, idanko hakane baiji dad'iba dole yau su sasanta kansu ya nunamata kome yawuce Amma yajamata kunne akan kada takuma yarda ta aikata makamacin laifinda ta aikata.

Kara d'auko wayarshi yayi yaduba massage din yaga tabbass yashiga amma ya'akayi bata amsa kiranshiba.

Dialing d'in number ta yayi, tadad'e shiru kafin agayamashi inda take ba service, Kara Kira yayi hakan dai suka 'kara mai-maita mashi, kusan sau hud'u Yana Kira amma duk amsar d'ayace cewa inda take ba service.

Tashi yayi yanufi d'akinta, turus yaja yatsaya ganin d'akin rufe, daurewa yayi ya ida isa yakama handle d'in 'kofar ya murd'a nan ya tabbatar da da key aka rufe 'kofar.

Juyowa yayi ya kalli khairat wacce har yanzu tananan zaune inda take tunda yashigo tanata taunar cingum dinta kamar wata tsohuwar karuwa yace "ke Ina Fauziyya tatafi"?

Wani irin kallon ukku saura khairat tayimashi tajuya tacigaba da cin cingum dinta 'kas 'kas 'karas.

Wata irin Zuciya ta 'kuleshi yace "ke ba tambayarki nikeba"? Cikin d'aga murya yake mata maganar kamar zai rufeta da duka.

Juyowa tayi ta kalleshi she'ke'ke tace "kada ka tambayi kaza Hanyar rafi ka tambayi agwagwa kasha labari"

A kufule Salim yanufi inda take da niyyar cin ubanta, dagudu taranta ana kare tashige d'aki tarufe, tana maida numfashi tale'ko ta window taga yanda Salim yake cika Yana batsewa idanunshi sun canja launi zuwa ja, ranshi amatu'kar bace.

Ta tsorata da ganinshi haka, azuciyarta tace mugu ainagama Zama ka dokeni, kamar kasamu jakka.

Daga cikin d'aki tad'aga murya yanda zai jiyota tace "bani nakashe zomon ba rataya aka bani, Kuma dazaka tambayeni Fauziyya ajiyarta kabani dahar kake Shirin buguna, kaje can kanemi matarka"

Cikin 6acin rai yakoma d'akinshi ya zauna yadafe kanshi da hannu biyu yafara tunanin Ina Fauziyya tatafi batareda izininshiba, abunda bata tabayiba iya tsawon zaman dasukayi da ita, gashi yakira number ta anacewa inda take ba service.

Wayar ya d'auko yasake Kira, yanzu Kuma switch off akacemashi. "Oh my God" yafad'a tareda dafe kanshi, Ina tashiga haka?

Wata zuciyar tace "akan me zandamu dan banga Fauziyya ba, ai ita ba 'karamar yarinya bace, duk inda taje zatadawo ta iskeni.

Fita yayi yahau mashin dinsa yabar gidan.

Yana fita Sani yashigo yanata kwad'a sallama, bud'e d'aki khairat tayi tafito tana 'yan waige-waige.

Kallonta sani yayi cikin mamaki yace "yanaga kinata waige-waige kamar wata marar gaskiya"

Kai dole inyi waige-waige Dan yau kad'an yarage inkumashan duka wurin Salim danyazo yatarar matarshi batanan kamar nice na koreta, yatambayeni nace ajiyarta yabani"

"Yo waye yakoreta idanba keba" dariya tayi tace "au ashefa hakane kaga nifa harna manta"

"Dole kike mantawa tunda kingama da wannan babin, Kinga yanzu hankalinmu kwance ciki yazama na Salim Fauziyya Kuma tazama ta Sani" dariya sukayi suduka sannan yace "kawomin abinci yunwa nakeji"

"To acici" tafad'a tana nufar kitchen, fitowa tayi da plate sha'ke da abinci sai ruwa pure water mai sanyi guda biyu kan plate ta ajiye gabanshi.

Haka yafara kwasar girki suna fira hankalulinsu kwance dan yanzu basuda sauran matsala.

*Birnin tarayya (Abuja)*

Misalin karfe hud'u da minti hamsin da shidda motar su Fauziyya tasauka garin Abuja, tun amota kanta ke masifar ciwo ga wani irin tashin Zuciya datakeji, tana sauka daga mota takira Aunty safiya tagayamata motarsu ta sauka, cewa tayi tajira ga driver Nan zaizo ya d'aukota.

Minti Sha biyar tana jira kafin driver d'in yazo, wata had'addiyar mota 'kirar 4matic black colour tayi parking gabanta, driver yabud'e yafito yanamata sannu dazuwa, amsawa tayi duk ta makure jikinta cikin hijab sakamakon wani mugun sanyi datakeji.

Daukar trolley d'in yayi yasaka a but sannan yabudemata bayan motar tashiga yamaida yarufe, sannan shima yashiga mazaunin driver suka d'au hanya.

Suna Isa gidan yaran aunty Safiya su ukku Ahmed da Walid sai karamar su walida, suka fito da gudu suna "oyoyo ga aunty Fauziyya" da kyar ta 'ka'karo murmushi tayimasu tana rungumesu jikinta d'aya bayan d'aya.

Walida uwar surutu da shegen wayo tace "Aunty jikinki da zafi bakida lafiya ne?"

"Shuru Fauziyya tayimata suka nufi 'kofar dazata sadaka da cikin falon.
Lokacin har maigadin yashigar mata da trolley dinta.

Tana shiga Aunty safiya tarugo tanamata oyoyo, Nan suka rungume juna d'an'uwa yaga d'an'uwa, jin jikinta da zafi rau yasa Aunty Safiya saurin rabata da jikinta tace "dama bakida lafiya Kika taho"
Girgiza Kai Fauziyya tayi tace "lpy lao nataho ahanya zazzabi yarufeni, inaga harda gajiyar zaman mota"
"Eyyah sannu muje ciki kihuta kafin baban Walid yadawo sai mukaiki hospital zuwa dare"

Kama hannunta tayi takaita d'akinda akayimata masauki, d'akine had'adde babu abunda Babu cikinsa na more rayuwa, sai sanyin AC daya gauraye d'akin da 'kamshin feshner.

Kashemata Ac din Aunty safiya tayi dan taga tanata rawar d'ari.

Kitchen tanufa tahad'a mata ruwan tea da milk da Milo takawomata, dakyar tasha rabin cup sannan Tasha paracetamol takwanta kan gado taja bargo.

Fidda su walida tayi dasuketa wasa suna hayaniyar muranar ganin Fauziyya tace "muje aba Aunty wuri tahuta kunga batada lpy"

Fita sukayi sukajamata d'akin, bacci ya kwasheta itace bata farkaba sai bayan magrib, jikinta zufa sharkaf Alamar saukar zazzabin, toilet tashiga tawatsa ruwa ta d'auro Alwala tazo ta kabbara sallolinda suka risketa kan hanya, sannan tayi ta magrib, tananan zaune kan prayer mat har akayi sallar isha'i tayi sannan tafita falo.

Zazzaune ta iske kan dining suna dinner, kujera taja ta zauna dan dama yunwa takeji, amma sai dai takasa cin abincin sosai, Aunty Safiya tana kula da duk yanda take tana tausayamata tasan zafin rabuwa da masoyi, gaskiya Salim bai kyautama autarsuba tunda yasakata wannan halin.

Kallonta tayi tace "zamuje asibitin ko?"
"A'a aunty naji sauki sosai inaga basai munjeba, dama harda gajiyar mota Kinga yanzu dana huta ya sauka"
"To Allah sauwake"
"Ameen" Fauziyya tafad'a.
Chapter 24 · 0% Book details