← Book details Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 35

Sashe 15

Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonshi Fauziyya tayi tace "kashiga ka amshi sakon" kallo yabi Fauziyya dashi wacce tana gama gayamashi sakon khairat tabar wurin, saida tashige d'akinta sannan yanufi dakin khairat d'in daga bakin 'kofa yatsaya yace "abada sa'kon" kallonshi khairat tayi ta sakarmashi wani irin murmushi irin nasu na yan duniya, d'aure fuska Sani yayi bai maida mata martaniba kamar yanda take tsammani, danshi yanzu haushinta yakeji tunda tabatama Fauziyyarshi rai,

'kara fad'ad'a murmushinta tayi tace "shigo daga ciki mana katsaya daga bakin 'kofa kamar wani ba'ko"

Jiki a sanyaye Sani yashiga d'akin ya tsaya nesa da ita alamun dai yanajiran sa'kon dazata bada, "haba Sani ya kake wani abu kamar ba'ko kawani tsaya sai wani d'ari-d'ari kake ka zauna mana ga kujera nan inshiga in d'aukoma sa'kon" tafad'a cikin wata irin kasalalliyar murya tana nunamashi d'aya daga cikin kujerun d'akin.

Sani dai jiki ba lakka sukuku kamar kazar da kwai yafashemawa aciki yanufi kujerar data nunamashi ya zauna, ajiye wayar dake hannunta tayi sannan tatashi tanufi bedroom dinta tana tafiya tana juya mazaunai, Sani Kuma yazubamata manyan idanunshi kamar dai yanda takeso, dama tayine danya kalla Kuma ya kalla, juyowa tayi dantaga yanayin dayake ciki, kamashi tayi Yana kallonta bako 'kiftawa, wani murmushin gefen baki tayi sannan tashige bedroom d'in.

Koda tashiga zama tayi bakin gado tana sa'kawa da warwarewa, takai kimanin minti goma sannan tafito lokacin Sani yamaida hankalinshi kan kallon wani Indian film da khairat din ta kunna yanata faman tafiya bama kallo takeba dan hankalinta Yana kan chat,

Gaba d'aya hankalin Sani yagama karkata kan indian film d'in dan wata zazzafar wa'kace akeyi, macen tasaka wani d'an wando Wanda bayada maraba da pant sai riga wacce Kai tsaye zaka iya kiranta brezia, shikuma namijin yasa dogon Wanda da Riga mai maballi Wanda ba'a balleba baki d'aya 'kirjinsa a waje yake, yarinyar tahaye kanshi Yana wani shafa jikinta yana shin-shinarta ta ko'ina.

Da alama wannan wa'kar tagama tafiya da imanin Sani dan har khairat tazo inda yake baisaniba, saida yaji hannunta kan nashi hannun, juyowa yayi a firgice ya khalli khairat sannan ya kalli hannunta dake ajiye kan hannunshi wanda batada niyyar d'aukewa, 'kara maida dubanshi gareta yayi, murmushi tasakarmashi kamar yanda tasaba, wani yarrrr yaji wani abu ya tsirgamshi tundaga kanshi har zuwa babbar yatsar k'afarshi.

D'auke hannunta tayi daga kan Hannun Sani takoma kan kujerar dake fuskantarshi tace "kayi hakuri Sani ashema banida wani sa'ko kayi hakuri na tsaidaka"

Ko magana sani baiyiba yatashi yanufi hanyar fita daga d'akin, harya Kai bakin 'kofa khairat tace "ji mana" juyowa sani yayi murmushi tayimashi tareda kashe Ido ta d'ago yatsunta guda biyu, shima yatsu biyu ya d'agomata Amma baiyi murmushiba, dan yau duk iskancin Sani yau yaga wadda ta dakeshi ta markad'e ta tace ta shanye ruwan.

*Kuyi manage da wannan, da yau bazanyi typing ba, hakanan dai bad'an daure nace Bari Sani da khairat su mi'ko gausuwa* 🤪🤪🤪

Mmn khady ce 😃
[9/25, 4:32 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 21

Fauziyya tunda tagama sallar da asuba batakoma bacci ba, kitchen tashiga ruwan zafi tad'ora tasaka Lipton da kayan kamshi bayan yatafasa ta tace tazuba a samis, sannan ta d'ebo dankali yanda zai ishesu harda Amarya ta fere ta fasa kwai shima yanda zai Isa, bayan tagama soya dankalin tasoya wainar Kwan, sannan tajuye kome cikin kyawawan mazubi, sannan tazubama sani nashi ta ajiye gefe.

Saida tagyara kitchen din tashare tagoge ko'ina tsaf, ta fiddo kwanukan wanke-wanke sannan tashiga toilet tashe'ka wanka tafito tashafa mai, tayi simple make up, wata doguwar rigar atamfa tasaka ja Mai manyan flowers baki, bakaramin kyau kayan yayimata ba.

Salim kuwa tunda yadawo masallaci yashiga d'akinsa yad'an koma bacci na 30minute yayi yatashi yashiga toilet yayi wanka ya shirya cikin milk din shadda, yayi matukar yin kyau, sai kamshin daddan turarensa ketashi ajikinsa.

Sallama Fauziyya tayi tashiga d'akin, amsa sallamar Salim yayi, cikin nutsuwa Fauziyya ta tako tana Shirin zama kusadashi yayi saurin rungumeta ya zaunar da'ita kan cinyarshi, k'amshin turarenta ya ziyarci hancinsa, d'ora kanshi yayi saman kirjinta yayi lamo kamar yaronda yasha kuka aka rarrashesa yayi shiru ya lafe jikin uwarsa.

Itama Fauziyya'kamshin turarensa take sha'ka, cikedajin dad'i wani irin farincikine cikeda zuciyarta, ganin yanda Salim din yanuna yayi missing dinta tsakanin daren jiya zuwa yanzu dasafe,

Magana tafara cikin wata irin sassanyar murya "Hubby katashi lpy?"
"Lpy lao my wife"
Yafad'a Yana Kara jawota jikinshi Yana shafata cikin salon soyayyarshi, "Uhum Hubby dama zuwa nayi Inga idan kunshirya kaida amarya ga breakfast can nahad'amana" hancinsa yakai saitin wuyanta yakara sha'kar 'kamshin turarenta, ya sauke wata ajiyar Zuciya yace "Nashirya my soul, a Ina zamuyi break d'in muje d'akinki ko?"

"A'a Hubby, kada muyi rashin adalci mana, kariga kasan daga jiya har zuwa kwana shidda masu zuwa nan gaba duka ranar khairat ne, sai dai muje d'akinta, kokuma muzo nan d'akinka muduka"
"Ok to kikawo mana anan inaga zaifi"
"To" kawai tafad'a tamike daga kan cinyarshi tanufi kofa, hartakusa fita daga d'akin yari'ko hannunta, juwowa tayi ta kalleshi tasakarmashi wani k'ayataccen murmushi, shima murmushi yayimata can 'kasan ma'koshi yace "I miss you" "miss you too" tafad'a sannan tazare hannunta daga nashi tafita daga d'akin.

Dai dai lokacin Sani yashigo gidan da sallama, amsa sallamar Fauziyya tayi "ah Sani Kaine, Ashe zakazo ai nad'aukama bazakazoba dan naga bakada lpy, ya jikin naka?"

"Da sauki Aunty, ai bawani ciwo bane dayawa kinsan kai da jini koyaya aka tabashi" Yana maganar Yana satar kallonta dan yau wani fitinannen kyau tayimashi, kullum kyawunta Kara fitowa yakeyi, kullum ganinta yake wata sabuwa awurinshi"

Allah sarki Fauziyya batasan tunanin da Sani keyiba akanta, ta gabanshi tawuce, nanma binta yayi da kallo azuciyarshi yace "wow tahad'u.... Tahad'u, gaskiya Ina sonki Fauziyya Kuma inaga lokaci yayi dazan mallakeki, hakurinafa ya'kare,"

Yana cikin wannan tunanin Fauziyya tazo tawuce tagabanshi d'auke da tiren data jeromasu kayan breakfast akai, taku take cikin nutsuwa sautin takalminta Yana bada kwas...kwas kan tiles d'in tsakar gidan, binta da kallon sani yakarayi, wani abu yaji Yana tsirgamsahi tundaga kanshi har zuwa babbar d'an yatsar kafarshali, tabbass yasan yanayima Fauziyya sonda babu wani mahalukin dakemata kalarshi duk duniya.

Juwowa Fauziyya tayi ta kalli Sani, wani mummunan fad'uwar gaba taji dan kamashi datayi Yana kallonta, kallonma irinna maza mayun mata, wani irin fad'uwar gaba taji dan kad'an yahana tasaki tire din kayan dake hannunta.

Dakewa tayi tace "lafiya dai Sani, wannan wane irin kallone kakemin haka kamar yau kafara ganina" kame kame yafarayi dan yashagala da kallonta baisan tazo kusadashiba hartakamashi Yana kallonta, dan ya iya takunshi duk tsawon shekarun dasuka d'auka tare bata taba kamashi da laifi kodayaba cikin tarin laufuffukan dayake aikatawa sai yau.

Sosa 'keya yafarayi kamar tsohon munafiki, "a'a aunty bafa ke nake kalloba, wlh Ina wani tunanin ne daban, banma San kinzo nanba" "ok to ga kayan wanke-wanke can nafiddo saikaje kafarayi ko" tana fad'in haka tayi gaba tabarshi nan tsaye yabi bayanta da kallo Yana lashe busashshen lebensa kamar wani tsohon maye.

Tagama jera kome na breakfast din a d'akin Salim kan carpet din tsakiyar d'akin, saukowa Salim yayi daga kan kujera ya zauna kan carpet din yace "Had'amin nawa sauri nake zanfita wurin aiki Kinga nakusa makara" yafad'a Yana kallon kyakkyawar agogon dake d'aure a hannunshi.

Murmushi Fauziyya tayi tace amma kasan banice keda hakkin hadamaba, koka manta bani d'aya bace agidan yanzu, yakamata kaje kayima khairat din magana tazo muyi breakfast din, saita hadama tunda yanzu duk cikin aikintane"

Da kamar Salim din yaki zuwa Kiran khairat din, Amma saiya tashi kawai yanufi dakin khairat din dan bayaso Fauziyyar ta daukeshi marar adalci,..

Sani Kuma tun shigar Fauziyya d'akin Salim wani munafikin kishi ke d'awainiya dashi, jiyake dayanada hali daya fiddota daga d'akin Salim din, amma hakan bazai yiyuba, cigaba yayi da wanke-wankesa zuciyarshi na Kuna.

Da sallama Salim yashiga d'akin khairat, shiru yaji Bata amsaba, Kai tsaye d'akin dayasan nan takwana yanufa, tura kyauren d'akin yayi yashiga, kwance ya isketa kan gado ta baje tayi dai-dai sai bacci take, duk illahirin surar jikinta bayyane take Dan kayan baccin dake jikinta dasu da babu duk d'aya suke.

Tsayawa yayi bakin 'kofa Yana kallonta, zuciyarshi na rayamata abubuwa daban-daban, wani irin mugun haushin khairat ya dira azuciyarshi, dan daganin yanda khairat ke bacci yasan ko sallar asuba batayiba gashi yanzu har karfe tara saura batada niyyar tashi, wata irin Zuciya takuleshi a harzuke ya isa inda take kwance ya dai-daici cinyarta wacce take yashe yad'aga hannu iya 'karfinshi ya d'ad'a mata wani mugun bugu.

A firgice tatshi zaune kan gadon tafasa Kara tana Kiran "Wayyo Allah Hajiya... ganin Salim gabanta fuska ba annuri yasa tayi saurinsa hannunta tadafe bakinta batareda da karasa abunda zata fadaba, zare idanu tafarayi kamar wacce tayima sarki 'karya.

A kufule Salim yace, nanba gidanku bane dazakiyi yanda kikaga dama, da alama ko sallar asuba bakiyiba kin kwanta kina baccin asara, idan Kinga dama kitashi idan kingama abunda kike Ina jiranki dakina, Kuma banison Bata lokaci minti shabiyar nabaki" yanagama fada yafita yabar d'akin.

Tana ganin yafita tatashi tana Sosa inda ya d'ada' mata bugu a cinya tace "mugu kawai, Kuma wlh saina gyarama zama a gidannan, nan gaba ko cewa akayi kayimin kallon banza bazaka iyaba barantana ka iya daga shegen hannunka kace zaka bugeni.

Toilet tashiga tashe'ko wanka tafito tashafa mai, sannan tazauna gaban mirror tayi wani mahaukacin makeup, wadrope tanufa tadauko wasu matsiyatan Kaya English wears riga da siket, rigar karamace da kyar ta rufe cibiya Hannun rigar net ne, Wanda saika duba sosai zaka gane akwai Hannun Dan sajewa yayi da jikinta, ga wani katon wuya da rigar takedashi Wanda Rabin Brest dinta a waje yake, siket dinma ya matseta sosai, Kuma bai kai har kasaba, amma ya wuce gwiwa.

Yani yalolon mayafi ne tadaura akanta, turarurrukanta masu masifar 'kamshi tafesama jikinta sannan tafito daga d'akin tanufi d'akin Salim din, maganar sallah Kuma Babu ita sai dai Atari ta azahar Kuma.
Chapter 15 · 0% Book details