← Book details Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 35

Sashe 27

Almajirin Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amsar wayar Aunty Safiya tayi tafara karantawa Fauziyya nakarayimata bayani inda bata ganeba.

Sauke ajiyar Zuciya Aunty Safiya tayi tace, to ikon Allah sai kallo, to tunda yace haka ki kirashi kigayamashi inda kike yazo saumuji 'karin bayani daga wurishi"
"To shikenan Aunty" haka tafad'a ta amshi wayarta takoma d'aki.

Komawa tayi kan gado ta zauna ta tattaro duka nutsuwarta ta lalubo number Salim ta danna Kira, tanata ringing ba'a d'agaba, sai gab da zata tsinke taji and'aga.

Shiru tayi tana share hawaye, tanajiran taji me Salim zaifad'a.

Cikeda mamakin ganin Kiran Fauziyya Salim yafara magana "my wife kece kodai mafarki nake, Ashe dama Zaki iya tafiya kibarni, haba Fauziyya miyayi zafi haka, kome nayimaki baikamata ki hukuntani ta wannan hanyar ba"

Cikin muryar kuka Fauziyya tace "Hubby nice yakamata infad'i haka bakaiba, saboda laifinda ban aikataba kuma banida masaniya akanshi ka sakeni......

Katseta yayi "ki daina furta kalmar saki Fauziyya, wlh tlh bansakekiba, har yanzu har yau har gobe matsayin matata kike saboda nidai nasan ban sakekiba"

Sauke ajiyar Zuciya tayi, dan ita abun yagama d'auremata Kai, to idan Salim yace baisaketaba waye yarubuta takardar saki ya ajiyemata, kawai dai yanaso yayimata yawo da hankali ne....Amma ga rubutunshi 6aro-baro

"Yanzu kina Ina kigayamin plz"
"Hmm Ina Abuja"
"Dama can Kika gudu, Aiko gobe Ina zuwa, danma yanzu yamma yayi sosai, amma gobe inshaAllah asubanci zanyo inzo in d'auki matata"

Murmushi Fauziyya tayi Wanda saida Salim yajiyo sautinshi, shima murmushi yayimata kafin sucigaba da firar missing d'in juna dasukayi.

*Kuyi manage da wannan da bazanyi typing ba sai gobe ganin yanda masoya keta jira yasa nayimaku wannan,*

Mmn khady ce 🤸🏻‍♀
[9/25, 4:32 PM] Mariya Umar Kn: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻‍♀

*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰

*Daga Marubuciyar* 📝

*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*

And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠

Page 37

*FAN'S ZANGAYAMAKU DALILIN DAYASA JIYA BAKUJINIBA, WLH BACIN RAINE KAWAI, AKWAI WANI BANZA DAKIKI, WAISHI IBRAHIM USMAN BINDIN KAKE KO UBANWA OHO DAI, YANANAN YANA AMFANI DA BASIRAR MU MU MASUYIN LITTAFI KYAUTA, SHIKUMA YANA KWASHEWA YANA SAIDAWA, WAI YABUD'E GROUP BAZAI SAKAKABA SAIKA TURA KATIN 200, KUMA BAWANI LITTAFI BANE NA DABAN YAKE TURAWA SAI NAMU MU MASUYIN FREE, AKA GAYAMAKA IDAN SON KUD'I NE KAFIMUNE, MU BAMUYI NIYYAR SIYARDA LITTAFIN MUBA, BAIKAMATA ACE KAI KANA SIYAR MANA BA, SABODA TSABAR RASHIN KUNYA HAR KIRANKA NAYI TA WAYA WAI DAN IN TABBATAR DUKDA NAGA POST DINDA KAYI NA TALLAR GROUP DIN KAKE KARA JADDADAMIN SAINA TURA KATIN 200 SANNAN KATURAMIN, NIDA LITTAFINA, TO KABUDE KUNNENKA KA SAURARENI DA BABBAR MURYA, WLH KAYI GAGGAWAR DAINA SIYAR MANA DA LITTAFI IDAN KUMA BA HAKABA WLH ZAMUYI MAGANINKA SHEGE ZAUNE GARI BANZA KAWAI, KAJE KANEMI SANA'A DAN WANNAN HAKKIN WASUNE KAKECI, IDAN KUMA KA'KI JI WLH BAKA'KI GANIBA, YAUSHE ZAMU ZAUNA MUYI WAHALAR TYPING DA WAYARMU DA HANNUNMU DA CAHRGE DINMU DA DATARMU SANNAN ACE KUMA WANI YAFIMU CIN GAJIYAR ABUN, BE YIWUWA KURA DASHAN BUGU GARDI DA KWACE KUD'I, DUKDA NASAN IRE IRENKA SUNADA YAWA TO WLH KU GUJI HAKKIN MUTANE KU DAINA, NIDAI NAFAD'A DUK WANDA YA SIYARMIN DA LITTAFI ALLAH YA ISA BANYAFEBA, KUMA KUDIN DAYA AMSA YACI WUTA BAL-BAL* 🔥

*Kukuma FAN'S kudaina biyema irin wadannan banzayen, idankuma zaku iya biyan wani 'katon banza kud'i yaturomaku littafin Dana nashiba, Kara muma mu maida na kud'i Kowa yahuta* 🤒

Khairat Kuma tunda suka dawo gida ta kwanta Kan gado tanata wannan lankwasa, ita gamai ciki, itako Mama sai nan-nan take da ita.

Jitayi tagaji da kwanciyar, wayarta ta d'auko ta dawo falo ta zauna kan kujera tabud'e data tafara chat, Mama na zaune gefe sai jeramata sannu takeyi, Amma saboda tsabar wulakanci batama d'agowa ta kalleta balle Kuma ta amsa.

Kusan minti talatin suna zaune ahaka, khairat sai chat takeyi tana murmushi lokaci zuwa lokaci, kafin tad'ago ta kalli Mama cikin muryar shagwaba tace "Yunwa nakeji, Kuma bazan iya shiga kitchen ba"

Jiki na rawa Mama tace
"Miye kikeso sainashiga na dafa maki, dama ai baikamata ace kinshiga kitchen ba, kamata yayi kizauna kihuta duk wani aiki ki ajiyeshi har Allah ya saukeki lpy"

Murmushin gefen baki khairat tayi tace "ok, tokishiga kitchen kidafamin taliya jallouf kisamin daddawa"

Mi'kewa mama tayi, tanufi kitchen tana fadin "to taliya kikeso, yanzu zandafa maki, Yar Albarka, Allah dai yayimaki Albarka kin kawomana farinciki agida"

Haka mama tashiga kitchen ta ta'kar'kare tafara aiki, minti Sha biyar ta gama dahuwar taliya saiko 'kamshin daddawa ke tashi, zubowa tayi a plate tasako spoon takawo gaban khairat ta ajiye, "to gashi sai ci ko"

Dagowa khairat tayi wacce har yanzu taketa chat d'inta hankali kwance, ta kalli taliyar ta yamutsa fuska.

sannan tace "Mama pork Zaki kawomin banacin taliya da spoon, kamar wata 'yar 'kauye, jiki na kyarma mama tashiga kitchen ta d'auko pork takawo, amsa khairat tayi tasaka cikin taliyar ta d'auko plate d'in takawoshi saitin kirjinta tad'ebo taliyy tana Shirin kaiwa baki, saikuma tawani 6ata fuska, ta maida, ta ajiye plate d'in tace Mama bazan iya cin wannan taliyar ba daddawa yayi yawa, Kuma yanzu banima son taliyar ma d'anwake nakeso"

"D'anwake 'yar nan, badamuwa Bari inyimaki d'anwaken, shiga tayi kitchen ta ta'kar'kare takwaba d'anwake tagama tazubo takwoma khairat, guda d'aya kawai tasaka abaki tafara kakarin amai,

Da sauri mama ta iso gareta tana jeramata sannu, tana tambayarta "kodai bazaki iyacin d'anwakenba?"

Daga Kai khairat tayi tace banason na fulawa, da kinhad'a alabo da wake kinkai ni'ka danaci, Amma Babu kome kabarshi kawai, kiyimin "wainar filawa nakeso"

Jiki na rawa Mama tace "badamuwa ai sai inyimaki, ai kome da dalili akeyinsa, ai bazantaba bari ki wahalaba saboda kinkawomin farinciki arayuwata, nadad'e inason ganin jikana bansamu hakaba saidaga gareki, Allah yayimaki Albarka bari inyimaki wainar fulawar"

Komawa kitchen mama tayi tafara aikin wainar fulawar.

Khairat naganin shigewarta ta kwashe da dariyar mugunta, ganin yanda Mama keta rawar 'kafa akanta wai ita zata samu jika.

Shiko Salim tunda yaji labarin Fauziyya baikarabi takan khairat ba, shirye-shiryen zuwa Abuja kawai yakeyi.

Aranar dai haka Mama ta wuni tana bautama khairat, kamar wata 'yar aikinta, sai dare mama tabar gidan dukta gaji jikinta yayi likis saboda uban aikin datayi, dan Koda tagama girke-girkenta Wanda Babu Wanda khairat taci aciki, saida tashare kitchen d'in tagoge sannan tafito tashare tsakar gidan tayi moping.

*(Ah ni su mama an bautama d'an Sani)* 🤣

*Jama'a Wai Baku cigiyar Sani*

Yau itace ranar da Sani ya yanke zaije gidansu Fauziyya yaga halinda take ciki dan tunda tabar gidan Salim bai'kara ganintaba, Yana Kuma Kiran wayarta lokaci zuwa lokaci amma kullum abu d'aya ake gayamashi shine wayar na kashe.

Wanka Sani yad'auka cikin wata fitinanniyar shadda dark blue, yasha hula kalar shaddar, sai takalminshi black, sanifa yafito yayi gwanin kyau ga wani irin turare daya bad'a sai 'kamshi ketashi ajikinshi.

Koda ya isa 'kofar gidansu Fauziyya tsasayawa yayi Yana tunanin yanda zai 6ulloma al'amarin, yakai minti goma 'kofar gidan kafin yayi tamaza yashiga da sallama.

Mamar Fauziyya na zaune kan tabarma tana Shan iskan yammaci, ta amsa sallamar.

Zama yayi kan wata kujera irin ta roba dinnan dake ajiye gefe guda, ya gaida mama cikin ladabi ta amsamashi.

Shiru sukayi nad'an wani lokaci sannan Sani yace "amm Mama dama zuwa nayi mu gaisa da Aunty Fauziyya"

"Allah sarki, Aiko Fauziyya batanan ai tadad'e rabonta da garinnan"

"Ashe batanan to mama Ina tatafi ne?"
"Tana Abuja"
"Abuja" Sani ya mai-maita kalmar cikeda takaicin rashin tako sa'ar dayayi.

"Sai yaushe zata dawo Kuma"
Eh to Nima bansaniba, Amma zata dawo nan bada dad'ewaba inshaAllah"

"To Allah maidota lpy, Amma nace Kota canja layine Naga idan nakira layinta kullum kashe"

"Bata canja layiba shine dai take amfani dashi, ko d'azu muyi waya da ita"
"Owk zankirata, wlh mama banji dad'in abunda yafaru tsakaninta da Salim ba, tunda Fauziyya tabaro gidannan Nima naji duk ya fitarmin Rai"

"To yaza'ayi da 'kaddarar Allah, haka Allah ya kaddara, idan Allah yasa zamansu Bai 'kareba sai kaga an dai-daita"

Gyara zama Sani yayi yace "bani fatan dai-daitawa tsakanin Aunty Fauziyya da Salim, dan wlh Mama Fauziyya zaman ha'kuri kawai takeyi a gidanshi, wannan mutumin ba 'karamin mugu bane Yana muzguna mata kawai dai Allah yasa ita macece mai ha'kuri amma in banda haka da yanzu igoyoyin aurensu duka sun 'kare, gaskiya Fauziyya mace ce wacce samun irinta a wannan zamanin sai an tona"

Tunda Sani yafara magana Mama ke saurareshi ta sauke ajiyar Zuciya tace "to Allah dai yazama bafi Alkhairi"

"Ameen" Sani yafad'a, shiru yaratsa nawani d'an lokaci sannan yatashi yace" nizan wuce"
"To sai anjima"

Lokacin gab da magrib Sani yabaro gidansu Fauziyya, gidan khairat yawuce Kai tsaye zuciyarshi cike da takaicin rashin ganin Fauziyya,

Zaune ya iske khairat falo tana kallon wani Nigerian film, shima Zama yayi kan kujerar dake fuskantarta, kallo tabishi dashi tace "ah Sani wannan d'aukar wanka haka ina zuwa"?
"Ina zuwa kokuma Ina akaje dai" Yabata amsa

"To Ina kaje haka?"
"Ina zanje kau Wanda yawuce gidansu Fauziyya, sai dai Kuma nayi rashin sa'a ashe Fauziyya tunda tabar gidannan tana Abuja"

Wani mugun dad'ine ya mamaye zuciyar khairat, yanzu hankalinta ya kwanta, dama bataso Sani ya auri Fauziyya saboda tana kishinsa, Kuma yanda yake nuna tsantsar soyayyar Fauziyya tabbas idan ya aureta itakuma zai zubata kwandon shara, wani abun farincikin Kuma tayima Salim nisa Kuma da alama baisan inda takeba, kenan ita wannan Abu ita yayima amfani tajefi tsuntsu biyu da dutse daya.

Sani yakatsemasu shirun yace "nifa yunwa nakeji kisamomin abunda zanci, "akwai abinci kusn kala hud'u wane kakeso inkawoma, akwai d'anwake, akwai taliya dafuwar daddawa, akwai wainar fulawa"

Kallo Sani yabita dashi yace "miye ke damunki haka duk Kika zauna kikayi wannan abun"

Dariya khairat tayi tace "banice nayiba wata 'yar aiki nasamu tayita bautamin baji bagani"
"Yar aiki Kuma, yaushe aka kawota gidannan bansaniba"

Dariya khairat takwashe da ita tace "Mamar Salim ai itace sabuwar 'yar aikin dana samu, Dan yau ta bautamin yanda kasan sarki da bawa, Kuma tayi hakane duk dan cikin dake tare dani"
Chapter 27 · 0% Book details