← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 36

Sashe 9

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har malam Musa ya shigo da zumar tafiya dasu gida sbd likitan da ya fita yanzu ya sallamesu amma kaman yadda aka umurceshi Alhj Hassan ne ya kira ya sanar wa shi kuma ya turo malam Musa ummi bata ce komai ba ta dai bar zubar da hawayen sai azkar da take tayi, duk su biyu bayan su ubangiji ne kadai ya san abin da suke kullawa da warwarewa, suna sauƙa daga motar ummi ta dubi Malam Musa da yake mika mata wani takarda ta karɓa ta buɗe...
"Idan kina da magana ki sameni yanzu a parlor na"
Duban Alaya tayi tare da mata alama akan ta tafi, da kallo Alaya ta bita saide bata saba saɓa maganar mahaifiyarta ba haka ta wuce zuciyarta a kuntace cike da tunanin abin da ummi ke ɓoyewa a gareta sai taji bata ma son ji, kila rashin jin Alkhairin ta ne.
A natse ta tura kofan parlorn ta sanya kai zuciyarta cike da addu'a irin adu'ar nan na fuskantar mummunan abu daga cikin halittar ubangiji wato a'uzubikalimatillahi tammat min sharri ma khalaka, daga tsaye ta tsaya tana kallonshi
"hawwa kina da kafiya da taurin kai!"
Ya mata alama yana taɓe baki.
"Me kake buƙata?"
Sai da ya dara kan yace
"A tambayi kaza hanyar rafi kuwa? Hala kin mance tun ran gini tun ran zane, ba tun yau ba kika kwana da bitar bukatata a gare ki, da Kalma ɗaya tak zaki samar muku Ƴanci"
"idan na amince maka na kuma yi maka duk abin da ka buƙata shine kadai zai sa ka fasa auren da kake shirin kakabawa Ƴa ta na tozarci da rashin galihu?"
"Ko kin amince abu ne mawuyaci a fasa sbd yaro ya gani ya yaba, Marin da ta mishi kuwa daidai yake da ta yankarwa kanta tikiti na rayuwa dashi har abada, abu É—aya na sani ko da kin amince nayi yadda nayi muka bar maganar auren nan to É—iyar Ahmad bazata kara minti guda cikin gidana ba! Daga lafiyarta, cin ta, shan ta da karatunta duk sun yanke daga kaina babu abunda zan kara iya yi mata kuma a rayuwa sbd Ahmad be cancanci abubuwan da nake yi mata a yanzu ba.."

"Me Ahmad yayi maka a rayuwa banda hallaci?  Kai butulu ne, kai azzalumi ne Hassan, ba zan taɓa bari ka samu abunda kake so a rayuwa ba zan barka da SON ZUCIYARKA cikin AL'AJAB NA SO kana ji kana gani ba zaka taɓa samun biyan bukatar ka ba in har dae akan SO ne ka aikata duk abunda ka aikata, Allah yana gani kuma ya san komai idan kaga Fatima ta auri wannan mutumi da ka kawo to haka yake rubutacce ne tun fil azal, ba zan iya chanza mata kaddara ba, addu'a kuma shine maganin komai..."
Tana kai nan ta share hawayen dake gangara mata ta juya ta fice.

Hajj Zeenat dake tsaye tana kallonshi yadda gabaɗaya yanayin shi ya sauya Ranshi ya kai kololuwa wurin ɓaci ta san ba komai bane sai danganta Ahmad dashi da Hawwa tayi har tana ikirarin cewa Ahmad ya fishi daraja da komai a idanunta, taɓe baki tayi ganin yadda ya wuce har yana buga kofa tace a fili
"Kanku aje ji wai mahaukaci ya faÉ—a rijiya yace kanku aje ji ni wankana nake"

Ko da ummi ta dawo bata iya tayiwa Alaya magana ba, kaman Alaya ta shiga ran ummi ta yagi fallen takarda daga takardar ta sbd so take ummin ta fahimci maganar daga zuciyarta yake rubutu tayi me É—an tsawo kan ta ajiye mata ta tashi ta fice daga É—akin.

"Hawayen uwa abu ne me zafi da daraja a idanun ƴaƴa, ummi karki sake zubar da hawayenki akan wannan matsalar kin manta ke kika ce min Aljanna ana kewaye ta ne da abunda rai baya so yayinda ake kewaye wuta da abunda zuciya take so? Ko a makaranta an koyar dani cewa a cikin suratul baqarah Allah yana cewa zai kasance kuna matukar son abu sai ya kasance sharri a gare ku yayinda zai zamana kuna matukar ƙin abu sai ya zama shine alkhairinku, Allah shine mafi sani amma da na zurfafa tunani sai na ji ina da bukatar wannan aure watakila shi zai yi sanadin Chanza rayuwarmu, ba zan kara tambayar ki abin da baki so na sani ba na san in lokaci yayi zan sani, Don Allah karki sake yunkurin dakatar da Abban Jameelah akan auren nan idan har cutarwa yake nufinki dashi!"
gabaÉ—aya hawayen Ummi ya gama jike takardar, kowace uwa bazata so jefa yarta cikin rayuwar da tafi wadda suke ciki ba amma ta san Hassan shu'umi ne zai iya anfani da wannan dama ya jefi tsuntsu biyu da dutse É—aya kenan ko ta amince da kudurinshi sai ya san hanyar da ya bi ya muzgunawa Alaya saboda ita É—in É—iyar Ahmad ce.

Haka suka kwana cikin wannan damuwa amma Alhamdulillah da yake sun fawallawa Allah sai suka tashi wasai da safe kaman basu da wata damuwa ayyukansu suka kama kaman yadda suka saba...

****

Kishingide yake hannunshi rike da shisha Pen yana zuƙa sa'i da lokaci, ɗayar hannun nashi kuwa a kumatunshi daidai inda ta mareshi in ya shafa sai ya saki murmushi yana kallon fuskar yarinyar, Red eyes ɗin shi suka sake rinewa yana wassafa yanayin ƙirar jikinta yadda in tayi motsi komai nata yake girgiza, Allah ya zuba ƙira gata yarinya ƙarama, wannan in har ya same ta lallai yayi zarra cikin abokanshi, kaman yadda yake piya-piya a duk inda ya shiga baya jituwa da kananun kwari sai masu kumbar susa haka a aure ma, dole ne ya gayyaci duk wadda ya san zai iya gayyata ya nuna musu ya ƙere kowa...
"bala'i! This gurl is morethan beautiful.."
Gani yayi ba zai iya jira a dau lokaci ba hakan ya sashi Miƙewa daga kan sofa na rantsatsiyar club ɗin as usual sanye da kananun kaya three quater da shirt da bashi da maraba da vest, fitowa yayi cikin takunshi na nuna isa da jiji da kai wadda ze tabbatar maka da lallai shi wani ne ya isa ga motar shi ya shige tare da bata wuta yayi gida.

Kaman yadda ya fita daga club É—in haka ya shiga cikin parlorn sai de idanunshi da suka sauka kan mahaifiyarsu ne yasa ya É—an seta kanshi..
"Sannu da gida Maami"
Girgiza kai tayi tana kare mishi kallo ba tare da ta amsa ba, ze wuce tace
"Mukhtar"
Juyowa yayi ya dawo ya samu kujera ya zauna nesa da ita
"wani magana ne nake ji daga bakin mahaifinka?"
"Wai zancen aure? Na je na ga yarinya kuma na yaba ni yanzu ma so nake ko gobe ne tunda juma'a ne a É—aura kawai"
"ban gane a ɗaura gobe ba! Ƴar tsana ce? Ba ma maganan nan ba me kayiwa ƴar mutane da har zata mareka a cikin gidansu?"

"Maami yarinyar nan fa dakikiya Æ´ar talakawa ce da alama kaskantacciya ce ko wayewa bata yi ba, daga in É—an shafa fuskarta don tana da kyau da É—aukar idanu shine fa"
Tana girgiza kai cikin takaici tace
"ba kawai bane, ta san girman mahaliccinta ne tana kuma tsoron fushinshi tana kiyaye azabarshi, innalillahi wainna ilaihi rajiun..! Wace É—iyar mutunci ce zaku sa cikin bala'i da uku?"
Yanayin fuskanshi ne gabaɗaya ya sauya ya miƙe yana yiwa mahaifiyar tashi wani kallo dama ya riga ya san ba son shi take ba, ba kuma ƙaunar shi take ba, mahaifinshi kawai ke son shi
"Maami yanzu aurena ne bala'i da uku? Dama na san ba zaki taɓa farin ciki da cigaba na ba Maami ba ni kike so ba, wadda kike so yana chan yana aikin da kike ganin yafi na kowa a duniya, ni dae Allah na gani ba don kamanni ba kai tsaye zan iya cewa ke yaddikona ce...!"
Miƙewar da tayi yasa yayi shiru tare da komawa baya sbd ya mata farin sani bata sake mishi sam, be kuma gameta yace ze faɗa mata wani abu ta tsinka mishi mari ba don ba yau suka fara ba
"Ina maimaita maka wallahi Mukhtar kaji tsoron Allah ka sani komai zaka yi mai sauki ne da raina nin da kake, uwa nake a gareka baka isa ka faÉ—amin duk abunda ya ke bakinka in zuba maka ido ina kallonka ba don ba kai ka haife ni ba.."

"Toh fa, waye ya taɓo rina uwar faɗa.."
"Abba kaima ka sani in kana jin Muryar Maami a sama da ni ne ai Umar ba haka ake mai ba"
Cikin takaici take kallon uba da ɗan, ta rasa Meyasa suke kunsa mata bakin ciki, Abbansun nan ya so muktar har ya wuce misali duk abin da zata yiwa muktar tun yana ɗan karamin shi gani yake ƙi ne har yaron nan ya zo ya kangare, abun takaici kuma har yanzu basu ganin abin da suke aikatawa ba daidai bane, runtse idanu tayi cike da tausayin wannan yarinya da ake shirin jefa ta cikin ka-ƙani-kayi tana ji sadda Mukhtar ya bijirowa da uban nashi shi gobe yake so a ɗaura mishi aure wadda ya zo ya zo, wadda be zo ba duk damuwar su a take mahaifin nasu ya amince akan zai ƙira Alhj Hassan yaji yadda za'a yi shi dae ya kwantar da hankalinshi.

***

A natse ta sanya kafafunta ƙasa ta sauƙa daga cikin motar bayan driver ya buɗe mata kofar, karewa gidan kallo take tana nazari, gidan dae ya fi ƙarfin irin wannan aure da ake shirin aiwatarwa a gobe, tafiya take tana ɗan kalle kalle ko zata hadu da wani ko wata ta nemi iso, chan ta hango wata farar kyakyawar yarinya tana tafiya ne kawai amma daga dukkan alamu hankalinta yayi nisan kiwo, idan ta kula da kyau ma kaman yarinyar na sa yatsa sa'i sa'i tana dauke kwallah, sam yarinyar bata kula ba har seda tayi karo da ita kan tayi mugun komawa baya a firgice idanunta da suke fari tas a waje gabaɗaya.
Chapter 9 · 0% Book details