← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 36

Sashe 19

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa yayi ya fice, da sauri likitar ta ƙaraso ta riketa ganin tana shirin sake collapsing.
"Se hakuri Aunty, Adu'a itace maganin komai ki kara akan wanda kike"
Maami na hawaye tace
"Wallahi ina yi Likita, ina yi bana bacci amma kaman bana yi astagfirullah Allah na tuba Allah"
Tausayinta sossai ya rufe likitan, ita tayi ta kwantar mata da hankali amma ta koma ɗakinta firr ta ƙi tace zata zauna da Alayah gudun sharrin Mukhtar.

Se kallon yadda kasusuwa suka yiwa yarinyar sarka take yarinyar gwanin tausayi, rayuwarta duk ya daidaice sbd Mukhtar, matakin da ta yanke kawai shine na riketa ta nema mata saki wurin Mukhtar shine kwanciyar hankalinsu duka, in ya ga dama ya tara matan duniya a gidanshi yana zina dasu tunda abinda yake so kenan, share hawayenta tayi ganin Alayah na motsi ta riƙe hannunta....

"binty kin farka?"
Kai ta gyaÉ—a tana sake lumshe ido tace a hankali
"Maami cikina kaman ana karta"
"ai dole, taya me juna biyu zata zauna da yunwa sossai haka har ya fitar da ke hayyacinki? Ruqayya na hanya bari in kirata tayi sauri"

"Juna biyu???"
Bata san a fili ta maimaita ba seda Maami ta É—ago ta kalleta tace
"Eh, kina dauke da juna biyu na tsawon sati biyar..."
Dibbbbbb haka duniyarta ya tsaya, komai nata ya tsaya chakk kaman robot ta sake maimaita
"Juna biyu dai?"

*karki manta book 2 na kuÉ—i ne, da Naira É—ari biyar kachal zaki mallaka, a sha karatu lafiya*
3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin sai ki tura shaidar biya ta
09039206763*

                       🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page Thirteen*

*A cikin satin nan ina da hidima sossai so it depend da yanayin comments naku, in yi Page ban ga comments na arziki ba ga gajiyar hidima ga al'amuran yau da kullum gaskiya ba zan iya ba, sai in bari sai sati na sama in cigaba*

Yanayin fuskanta sai ya so ba Maami tsoro don ƙiri-ƙiri ya nuna bata na'am da lamarin cikin, lumshe idanunta tayi tana jin hawayenta na sake yi mata nisa sbd tsabar zubar dasu da ta ke, sai ciwon zuciya mai tsanani da take ji kaman ko yaushe zai iya yin ajalin ta, sam bata yi farin ciki da cikin ba, ba wai bata so bane ba kuma wai ta tsani ɗan bane kawai bata shirya haihuwa da Mukhtar bane cikin wannan hali da suke ciki na rayuwa, bazata taɓa so ɗan da zata haifa ya tashi ta nuna mai muktar a matsayin mahaifi ba, sam be chanchanta ya zama uba ba bashi da nagarta da wannan nasabar taya zai iya baiwa yaronsu tarbiya da taimakon da ya dace?

Dafata da Maami tayi ne ya sa ta buÉ—e rinannun idanunta ta kalleta
"Binty Dukda ban san yanda kike ji a cikin ranki ba nayi imani baki son wannan ciki, na tabbatar ba don wani abu bane sai don hallayyar Mukhtar in har baki shirya yanzu ba sai a zubar a yi miki planning zuwa wani lokaci.."
Da sauri kuma sai ta dafe cikin, gudan jininta za'a zubar? Girgiza kai tayi tana barin hawayenta zuba tace
"Maami ba zan ɓoye miki ba, hasashenki gaskiya ne sede ba zan iya zubar da wannan ciki ba, tunda Allah ya bani ya san dalilinsa na yin hakan watakila sanadin shiryuwar Ya muktar din kenan don Allah a bar min"

Murmushi Maami ta saki tare da shafa kanta tace
"Allah ubangiji ya miki Albarka binty, Allah ya shirya muktar ya san cewa dami a akala ce ya tsinta kar daga karshe yayi faɗuwar baƙar tasa, a lokacin da nadama bashi da anfani"

Shigowar ruqayyan ne ya katse su, da kanta ta zubawa Alayar abinci Maami ta taimaka mata ta zauna kan ta soma bata abincin, cikin natsuwa take karɓa har seda ta ƙoshi kan ta ce ya isa Maamin ta mika mata ruwa ta sha, kan ta sake kwanciya sai bacci, Aunty ruqayya ce tace
"Amma yarinyar nan na da tsananin haƙuri Adda, ina tsoron kar shiga hakkin nata yayi yawa, idan mariƙinta ya mata muguntar haɗa ta da muktar mu da muka san halayyarsa maras kyau kuma be kamata mu zuba idanu tana shan wahalarsa ba kiyi hakuri in abinda na faɗa ya ɓata miki rai"

Murmushi me ciwo Maami tayi tana kallon Alayar tace
"a yanzu ruqayya zaman yarinyar nan da muktar ya fi cin raina fiye da yanda kike zato da asalin hallayyar muktar ɗin, tausayinta nake ji har ƙasan raina da ita nake kwana da ita nake tashi, amma in shaa Allah daga yanzu hakan ya wuce, Fatima ta gama zama da muktar in shaa Allahu, ko da mariƙin nata bai karɓeta ba ni zan zauna da ita har Allah ya kawo mata wani mijin da zai share mata wannan bakin cikin"

Tattaunawa suka cigaba da yi duk akan matsalar Mukhtar, chan sai ga Alhj ya shigo yau kam seda yayiwa Mukhtar faɗa akan abinda yayi wanda hakan be wani ɗaɗa muktar din da ƙasa ba wayan ma ya ajiye a gefe hands free yana zuƙar shisha ɗin shi hankali kwance, bayan ya gama ya kashe.

Ita Maami bata wani yi maganan Alayar da shi ba don ta san duk inda aka je aka dawo yana bayan Mukhtar don ba ganin laifin shi yake ba sam, saida ta kwana biyar a asibitin kan aka sallameta, a wannan karo Maami ita ke yini ta kuma kwana duk yanda ruqayya tayi da ita akan ta bari su kwana ko ta kawo mai aikinta su kwana ta ƙi tace bata so ko kusa Mukhtar ya sake yunkurin cutar da ita, daga asibitin gida suka yi direct ɗakin dake gefen nata Maamin ta mata masauki don ta sake.

Da kanta ta tura aka haÉ—o mata kaya akwati har biyu da wayanta da take ta magananshi sbd son jin Umminta da take, É—aki ne me girma da tsari babu abin more rayuwa na kuÉ—i da babu ciki, Maami ta mata umarni da ta dinga kulle kofan in an yi knocking sai ta tabbatar da waye kan ta buÉ—e don ta san Mukhtar farin sani, ita kuma zata cigaba da kula Dukda ta saka securities hana shi isa sashenta tace duk shigowan shi iyakaci sashen mahaifinshi bata amince ya zo mata sashe ba.

Zaman Alaya a gidan ya matukar yi mata daaɗi duk wani kulawa na me juna biyu tana samu daga Maami, da kanta take shiga kitchen take dafa mata duk wani abu da ta san zai ƙara mata lafiya, haka a asibiti ma an yi recommending ta yawaita cin irin su vegetables, jan nama da dai sauransu, laulayinta ba mai yawa bane saide zazzafar zazzabin yamma, sai kuma wani sa'in amai shima ba sossai ba, kaman yadda ta ɓangare ɗaya Mukhtar ya gigice don duk yanda yake tunanin hukuncin Maami ya wuce nan tayi rantsuwa ko ya kawo mata takardar Alayah ko su haɗu a court ya bata ta karfin tuwo tunda yarinya bata son shi, Alhj hammad din ma bata ragar mai ba gashi yana ɗan busy sbd siyasa da ya kawo kai gadan-gadan.

Damuwar Alayah guda ɗaya takkk na rashin jin mahaifiyarta duk text message da zata yi mata ba reply tayi ta kira tun yana shiga har ya daena, wannan na daga cikin abinda ya shigar da ita sabuwar damuwa da zaƙuwar son ganin mahaifiyarta, suna zaune da Maami suna ɗan taɓa hira yayinda Maamin ke chat kaɗan kaɗan tana murmushi me sanyi sbd da sanyin zuciyarta take magana, Dukda ɓacin rai yake nunawa ita kam lallashin shi take ta kuma lura har da Shagwaɓar da baya rabo dashi in dae yana gabanta kaman ba shi ba.

Kira ne da ya shigo wayan ya sa ta gyara zamanta a natse tayi picking ta sanya a kunnenta cikin ladabi kaman tana gaban na cikin wayan ta soma miƙa gaisuwa cikin kulawa yake amsawa kan a natse yace
"FaÉ—imatu yanzu mijinki da É—an ki suka bar nan"
HaÉ—e fuska tayi kenan kararta suka kai wurin baba.
Kanta ƙasa tace
"Baba kayi haƙuri na jin wani abu na laifina da kayi daga gidan aure saide ƙullin na da girma dole sai na warware maka zaka fahimceni, na san baka daga cikin masu goyon bayan zalunci da kai da me sunanka zuciyoyinku iri ɗaya ne a wanke a kuma dake, cike da gujewa duniya da kyamatar azzaluman cikinta, don Allah ka bani dama zan zo har gida ka ji uzurina"

Ajiyar zuciya ya sauƙe yace
"Ina fata ba hikiman zancen da Allah ya miki bane kika kanainaye ni da ita, ina jiranki"
Daga haka ya yanke wayar, saukewa tayi ta saki ajiyar zuciya bata fata ko kusa baba yayi mata dole na ba Mukhtar Alaya sam bata wannan ra'ayin.

Duban Alaya da sai juya wayanta take tayi tana karantar damuwar fuskanta kaman ma bata san da wayan da Maamin ta gama yi ba tace
"Binty"
Bata amsa ba ta sake cewa
"Fatima.."
Nan ma shiru, Miƙewa tayi ta isa gareta ta taɓa ta sai tayi firgigit ta zubawa Maami idanunta dake cike da ruwan hawaye, Maami tace
"Binty yawan tunani hatsari ne ga lafiyarki, menene? Me damuwar?"

Hawayen ta ne ya gangaro tace
"Maami yau sati na uku ake shirin shiga ban ji daga Ummi na ba, hankalina a tashe yake ina tsoron kar dae wani abu ne ya sameta"
Ajiyar zuciya Maami ta sauƙe kan ta dubeta tace
"In shaa Allah lafiyanta ƙalau kila ɗan wani abu ne kalilan in shaa Allah jibi sai driver ya kai ki ki dubo ta don bana tunanin Alhj Hassan chanji yana nufin furucinsa akan ki"

Murmushi mai ciwo Alaya ta saki ita kam ta riga tayiwa Abban Jameelah farin sani babu ko shakka abinda ya faÉ—a É—in har ranshi ne sede zata je É—in, ko yanka naman jikinta yake zata je taga mahaifiyarta.
Chapter 19 · 0% Book details