← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 36

Sashe 5

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi kuwa Dukda aiki take sede hankalinta rabi da kwata baya tare da ita, gashi dae sun haɗu da Meelah sau biyu amma tsoron tambayarta Alayar take bama ta san ta yadda zata fara ba don mutunci be taɓa hada ta da Jameelah ko na minti ɗaya ba, in zata iya tunawa har miyau Jameelah ta taɓa zuba mata a fuska, wa kuma ya san irin zagin cin mutuncin da suke sha don ma bata da kunnen ji, a gaggauce ta gama wanke wanken da take ta nufi komawa sashensu don duba ko Alaya ta dawo.
Karo ta ci da jikakkun uniform nata daga tsakar daki seda gabanta ya yanke ya faɗi da sauri ta ƙarasa ciki tabbas da tana da kunne zata iya jin irin kukan da Alaya take cikin ciwo, da gudu ta ƙarasa ta ɗago ta tana kokarin maganan su irin na kuramen nan sede babu abunda yake fita, hannun Alaya ta kama se taga ya chanza yayi wani abu blue tinge wadda a turance ake kira (cynosis) gabaɗaya ilahirin hannun, jijjigata tayi ta buɗe idanunta da kyar nan ma duka haka ne alamun ciwon zuciyarta ya tashi, ganin yadda numfashi ke shirin dauke mata kaman bazaka kyapta idanu ka buɗe ka sameta da rai ba yasa ummi Miƙewa da sauri tayi waje..

Tana fita motar Alhj Hassan Dala na parking a tsakar gidan da sauri ta nufe shi, a gabanshi ta tsaya hawaye na zuba mata, duban ta yayi na mintuna ya san in ya kalleta cikin wannan hali ƴar ta ce ba lafiya, baki ya taɓe kan ya koma motarshi  hankalinshi kwance yayi rubutu a jikin wani joter ya ɓalle ya fito, hannu ya sa a aljihu ya zaro kuɗin da baza su wuce dubu talatin ba ya watsa mata da papern, duƙawa tayi tana kuka tana tattarewa cikin sauri sauri daga haka ta miƙe tayi sashensu.

A hannu ta riko Alayar dake tafiya da kyar da karfin hali don bata ma sanin tana É—aga kafa sbd azabar ciwo, baba Musa da dawowarshi kenan yake tambayan shazali me gadi ko Alaya ta dawo shi kuma yana bashi labari ya hango Fitowar su duk hanaklinsu seda ya tashi ummi kuka Alaya kuka, baba Musa ne yayi kundunbalar fita ya samo abun hawa da kyar sbd irin tsaron unguwar, ya cewa malam shazali idan har aka tambayeshi ya ce ya tafi gida an kirashi iyalinshi ba lafiya.

A napep din banda faɗa cikin tausayawa su ummi babu abunda yake, har yaushe wannan rayuwar zaluncin? Ina ma yana da wani iko da ko se ya ga abunda ya turewa buzu nadi akan iyalan Alhj Ahmad marafa, har hawaye yayi jin yadda Alaya ke kirar sunan Allah cikin azaban ciwo, asibitin murtala suka isa sbd nan ne su kan je idan irin hakan ta faru don basu da dalilin na kuɗi ɗan abunda yake basu idan ya ishesu Toh falillahil hamd idan kuma be isa ba sede su bar jinyar a haka idan har an ɗan samu sauƙi hakan yasa kullum Alayar take a wahale babu kuma ƙiba se rama.
   Cikin hanzari aka karbesu aka fidda file ɗin ta aka yi emergency da ita, ummi zama tayi bakin wurin tana zub da hawaye masu zafi, ita kadai ta san irin tashin hankalin da take shiga a duk sadda ciwon Alaya ya tashi irin haka, ita kadai take dashi idan ta rasata ina zata saka rayuwarta?
   Bata da tabbacin ko likitan zuciya ne ya shiga kan Alayar sun dae ɗauki lokaci a kanta kan suka fito, baba Musa yake tambayar su ya jikin nata?
"Baba wannan É—in Æ´arka ce?"

Ya amsa da"eh"
"Kwanaki na bada shawarar zuwa wurin Dr philip sbd kwarewarshi a harkar zuciya chan meddy specialist hospital ban san Meyasa kuka kasa daukar shawarata ba, ina me tabbatar muku yarinyar nan tana kara shiga yanayi me hatsari ne a yawan attack da take samu idan mun iya tseratar da rayuwarta yau gobe babu abunda zamu iya, so prevention is better than cure"

Baba Musa ya jinjina kai yace
"in shaa Allahu zamu yi kokari akan hakan mun gode likita"

Wucewa doctorn yayi yayinda ummi ke ta kallonsu cikin zakuwa da son jin me suke cewa sbd gabaÉ—aya hankalinta yana kan lafiyar gudan jinin ta, Juyowa yayi tare da yi mata bayani bata iya ta ce komai ba se hawayen da take sharewa a kai kai ba basu je Meddy din bane sun je sede irin kuÉ—in da suka ji daga karbar kati ma zuwa ganin Dr ba karamin kudi bane basu dashi babu kuma dalili.

Ummi ce rike da hannun Alaya dake ta aikin bacci sbd alluran da aka yi mata lokaci lokaci ta kan kalli mutanen É—akin, kowa da kalar ciwonshi, ward ne me É—auke da gadaje kusan ashirin dogo ne sossai, Malam Musa ya samu ya tafi sbd gudun matsala zaninta ta kwance ta fiddo papern joter din da ta nannade ta É—aure a wurin ta fara warewa a hankali.

"Kaman yadda na faÉ—a miki a baya na kuma maimaitawa yanzu ma ba zan gaji ba zan sake faÉ—a, hawwa duk wani abunda yake faruwa daku laifin ki ne, lafiyar Æ´arki a hannunki yake kaman yadda lafiyar kunnuwanki suke hannunki, Da kalma É—aya tak! Zaki Æ´anta ku zuwa sabuwar duniya amma kin kasa anfani da wannan dama, a yau Idan Fatima ta mutu karki ga laifin kowa se kanki, ke ce kika kasheta..."

Dukunkune papern tayi tare da runtse ido da karfi hawaye na gangaro mata sossai, da sauri take girgiza kai kan ta ɗaura kanta jikin gadon Alaya ta saki sassanyar kuka, shin ya zata yi? Har abada bata jin zata iya abunda Alhj Alhassan Dala yake so, amma ganin ƴarta a hali irin na dazu ya sa take jin zata iya yin komai sbd samun lafiyarta, in tace komai tana nufin komai amma buƙatar Alhassan ya zarce da tunaninta, Allah ka min mafita... Abunda take ta nanatawa kenan a ranta.

"Ummi!"
Alayah ta faÉ—a tana me dafa ta idanunta da suka sauya sossai suke lumshewa da kansu ta zubawa ummin da ta É—ago take share hawaye a lokaci É—aya tana tambayarta ta farka? Ya jikinta? Me take so? Duk cikin alamu irin ta maganan kurame.

"Yunwa ummi, yanzu karfe takwas na dare babu abunda ya shiga bakina tun safe banda ruwa"
Tayi alamar cikin tsananin jin yunwa ga ciwo, bakin ta duk ya bushe.

Miƙewa ummin tayi tace mata tana zuwa ta fice, maida idanunta tayi ta kulle tana jin yadda surutan matan masu jinya da masu kula dasu na ta tashi kaman kasuwa hakan ne fa ya sa ta tsani asibiti, tana nan kwance har ummi ta dawo ta taimaka mata ta wanke bakin ta, da kanta ta wanke hannu take ciyar da ita dafaffen  doya da Miyar sauce ɗin da ta saya a bakin asibiti daga cikin ledar, bayan ta ci sossai ta ɓula farin ledar da aka kulla mata kunu ta bata ta sha sossai kan ta sha magungunan da ta sayo duk tana bacci lokacin ta sha.

Rokar roba wurin makotarsu tayi ta saka ta tayi alwala ta rama sallolin da ake bin ta, ummin se kallon ta take tana tunanin wani shawara zata yanke, duk wadda ta zaɓa babu sauƙi...

Kwanansu biyu asibitin banda ma'aikatan gidan babu ƙafar wadda suka gani a ahalin gidan dama sun saba Dukda da ciwo matuka, duk faɗar ka da mutum ai ciwo ya fi gaban komai, yanzu haka zasu koma su ɗaura musu da bauta ba tare da kyautatawa ko na minti ɗaya ya shiga tsakaninsu ba, banda abinci da shima se an ga dama a basu da kuma makarantar Alaya ba zasu ce ga wani abun arziki da suke tsinta a rayuwar gidan ba, amma ya suka iya? Ya kuma zasu yi? Nan ne kaddararsu kuma nan Allah ya zaɓar musu su yi rayuwa.

Landline ɗin sashensu ne ya ɗauki kara ko gama tattare sashen ummi bata yi ba sbd tunda suka tafi babu wadda ya dawo se yau, ummin kuma ta hana Alayar kama mata sbd har yanzu jikin se a hankali, ƙarasawa tayi ta ɗauka Muryar Meelah ne ya karade kunnenta
"Ki zo ki yi min gyarar daki"

Shine abunda ta faÉ—a kan ta kashe babu ko amsa sallamar da tayi mata, ummi ce ta tambaya me take so? Nan ta faÉ—a mata, girgiza kai tayi tacewa Alayar ta je ta kwanta zata je tayi mata.
Babu dae yadda ta iya ne haka tana gani ummin ta fice, zama tayi a wurin ta sanya kanta cikin kafafunta tana tunanin abunda kaddara ya zaɓar musu se yaushe ze wuce? Anya kuwa zasu samu chanjin rayuwa?

Kwarai ummi tayi mamakin ganin irin yadda Meelah ta maida É—akin a kwana biyu kaman ba mace ba? Duk wasu ledojin kwalamarta na zube tsakiyar É—akin wasu kayan sawa wasu takalma duk gasu nan É—aiÉ—ai baje a É—akin haka ta soma tattarewa a natse ta jima kan ta samu É—akin ya dawo daidai ta juya ta fita ta tsaya parlorn ta gyara ta koma na Hajiya Zeenat ta fara kenan Meelah ta fita daga dakin uwarta tayi nata ba'a yi mintuna goma ba ta dawo ta tsaya kan ummi tana mata magana cikin tsawa.

Ganin ba jin ta zata yi ba yasa ta dauko sandar mopper da ummin ke aiki dashi ta zungureta wai ita nan kyamar taɓa ummin take, Juyowa ummin tayi saide Meelah ba maganan kurame ta iya ba masifarta ya fito da Hajiya Zeenat
"a'a Shalele mai ta miki ne?"

"Mommy ina sarkar da Abba ya sai min last business trip din shi daga Lagos?"

"Eh na zinarin nan"
Mommyn ta amsa

"Mommy daga shiga ta min shara kawai in fito ban ga sarka ba? Kan uban chan kayyasaaa! Wlh sai ta fitar min da sarkata "
Meelah ta faÉ—a tana wani hararar ummi cikin tsantsar fitsara da rashin kunya.

Mommy ta juya ga ummi tayi mata alama
"ina sarkar da Kika sata a É—akin Meelah?"
Chapter 5 · 0% Book details