← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 36

Sashe 26

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Maami"
Ta kira sunan da tunanin kar ta ga fitan Abba daga ɗakin nata ne, gabanta ta iso ta riƙo hannunta..
"Binty me ya faÉ—a miki?"
Shiru tayi kanta ƙasa ba tare da tayi magana ba sai hawayen da ya cigaba da zuba mata
"kar ki damu na jima da tashi sanadiyar kiran Mukhtar to sai na kasa komawa bacci, ina cikin nafila na jiyo motsi da kuma buɗe kofa hakan ya sa na fito, har ya fice bai san da tsayuwata ba kuma ba zan taɓa faɗa mishi na ga zuwan shi ba, abinda kawai nake son sani shine me yake so da ke?"
"So yake mu yi nesa da ku"
Girgiza kai tayi ta sake riƙe mata hannu
"kar ki É—aga hankalinki Alaya, ban shigo rayuwarku don in lasa muku zuma a baki in kuma janye ba, na san kila har barazanar da yayi mini É—azu ya faÉ—a miki don ki ji ba daaÉ—i karki damu na fi kowa sanin Alhj, gidan shi dae zaki iya bari amma ba dae rayuwar mu ba, mun riga mun zama en uwa, har gobe ni matsayin uwa nake a gareki yaya a wurin umminki kinji?"

Rungume Maamin kawai tayi tana murmushi me haɗe da hawaye, Maami ta zama komai na rayuwarsu, da gaske Allah ya turo musu ita ne don ta taimaka musu ta fitar da su daga uƙubar da suke ciki, lallashinta Maami tayi ta yi har sai da ta ga ta koma bacci kan ta fice daga ɗakin, bata iya ta yi baccin ba ita kam haka ta kwana kai wa Allah damuwowinta, da asuba tare da masu aikinta ta shiga kitchen suka kama aikin breakfast, tsab suka gama ta bar su su shirya ta haura sama tayi wanka, tana fitowa Alaya ma na fitowa, gaishe ta tayi ta amsa fuskanta da fara'a as always tana mata ya jiki, ita dae Alaya na matuƙar mamakin hallayyar Maamin sam bata yarda da sa damuwa a ranta har ya nuna ga fuskanta ba.

Suna isa dining da niyyar cin abinci sai ga Abba ya shigo, Maami ne ta fara gaishe shi ya amsa ba yabo ba fallasa, Alaya ma ta gaishe shi ya amsa da kyar, Maami ce tayi serving nashi ya ja gabanshi ya soma ci, ita dae Alaya juya spoon É—in kawai take kaman yadda ta kula Maami ma ba wani cin kirki take ba, Tv dake aiki daga parlor ne aka soma labaran safiyar...
Da wani hanzari duk su uku suka miƙe tsaye, Abba ne gaba wurin isa cikin parlorn daidai me kanun labaran na cewa
"Mukhtar dai ɗa ne ga ɗan takarar Gomna wadda aka fi sani da honourable Hammad Abdulhameed chanji... In ba'a manta ba Mukhtar dae na da tabo a hukumar na en sanda inda ya ci firsuna na wa'adin shakaru takwas a ƙasar waje to dai gashi nan labari ya sake maimaita kanshi ku biyo ni don jin cikakken labarin"

Kokarin zubewa ƙasa Abba yake Maami da ita ma take jin bata da wani karfi, firgici da damuwa haɗe da wani irin tashin hankali suka rufeta tayi kokarin tura shi a madadin ya kai ƙasa sai ya zube kan kujera yana jiƙewa da wani gumin tashin hankali.
Alayah ce da ita ma karfin hali tayi wurin riƙe Maami suka zauna a tare, babu wadda ya iya magana sai tvn da suka ƙurawa idanu suna jiran kanun labaran kaman kuwa a mafarki aka hasko hannayen Mukhtar ɗaure da ankwa

"A safiyar yau ne en sanda suka yi tattaki har gidan ɗan ɗan takarar nan honourable hammad Abdulmajeed chanji wato Mukhtar hammad chanji inda babu ɓata lokaci suka kame yaron nashi bisa zargin aikatawa yarinya karama ƴar shekara 16 fyade a daren na jiya, inda suka bar yarinyar cikin mawuyacin hali ga wakiliyar mu nan daga asibitin da aka kwantar da yarinyar"
A take aka hasko iyayen yarinyar mahaifinta na kuka, haka en uwanta tsiraru da suke asibitin É—aukewa aka yi aka dawo kan É—an jaridan ya cigaba da cewa
"a wannan lokaci da siyasa ke gab da wanzuwa a jibi jibin nan jama'a dayawa da suke ƙarƙashin tafiyar ta honourable sun soma janyewa, ga kaɗan daga bakunan jama'ar"
Wani aka hasko yana cewa
"mutumin da ya gaza ba É—an shi tarbiya taya zamu yi zaton zae tafiyar da mulki, wannan halaka mu zai yi bama yi.."
Na bayanshi suka amsa da bama yi bama yi, aka sake hasko wani haka dae aka yi ta hasko mutane suna fadin albarkacin bakin su duk babu wani daaÉ—in ji..

Wayan Alhj en jam'iyyarsu suka soma kira sai dae motsin kirki ya gaza, jikinshi banda rawa babu abin da yake, shikenan abin da yake gudu yana tunanin yana da ikon dakatarwa ya faru, wannan shine ta faru ta ƙare ga ƙoshi ga kwanan yunwa! Ya gama shiryawa da Alhj Hassan akan in ya kori su Alayah dole in sun tagayyara su koma mishi tunda shi kadai suka sani sai gashi ɗan da ya fifita ya ɓallo mishi ruwa, ruwan da zai mishi ɓarnan da baya tunanin zai taɓa taruwa ɓallewa zai yi ya shiga gari, da sauri ya ɗauko wayanshi dake ringing ya duba, chairman na party din su ne.

Wani irin faɗa yake da masifa, akan me Abba ba zai tare danshi ba in ya san bunsuru ne yanzu suna ji suna gani haka partynsu zata ci kaye, sun yi duk yadda zasu yi sun danne batun baya amma wannan ya tashi musu kamar wutan daji kowa sai gani yayi a duniya, shi dae ya kasa cewa komai tunda hankalin Ƴan partynsu ya riga ya tashi haka wannan abu ba mai gyaruwa ba ne, Maami da ke zaune kaman mutum mutumi da Alaya da kanta na ƙasa zafin da ranta yayi ba sossai ba tunda dama ta riga ta cire rai da Mukhtar ta san ba zai taɓa gyaruwa ba, girgizan da tayi ma na don abun cikinta ne, hannunta dafe da cikin tana tunanin me wannan ɗa zai ɗauketa a rayuwa? Kawai sai faɗuwar Abba suka gani...

****

"ba za kayi magana ba?"
Shiru yayi yana kallon jibgegen ɗan sandan dake gabanshi cikin su biyar da suke tsaye, be tanka ba sai ma idanunshi da ya lumshe Allah kaɗai ya san abin da yake ji cikin ranshi, ina ma da zai iya saka hannu a kai yayi ta ihu ko duniya zasu fahimci tashin hankalin da yake ciki, duk yadda aka yi ya san zuwa yanzu magana ya riga ya kai kunnen Maami da Alayah, zasu sake yarda da shi a duniya? Menene wannan yake farautar rayuwar shi? Ko dai zunubanshi ne ya soma girba tun yanzu? Kulkin da aka sauƙe mishi a gwiwa ne ya saka shi buɗe idanun yana kallon Police ɗin ba tare da yayi motsi ba, ya tabbatar daga safiya zuwa yanzu da ake durfafan azahar da gwiwowin nan zasu fita da sun riga sun bar jikinshi, tun yana ma jin azaban dukan har ya daina ji, nauyin kirjinshi ya fi mishi azaba fiye da dukan, sai zullumi yake kila ciwon zuciyar Alaya ya tashi, kila Maami tana chan tana ta kuka watakila ma tana asibiti a kwance hawan jininta ya tashi, tsintar bakin shi yayi da furta
"Astagfirullah! Ya Allah ka sassauta musu"

Duk yadda suka yi yayi magana ya ƙi cewa komai, gabaɗaya idanunshi da fuskanshi sun sauya sai gumi yake jika shi, kafafunshi baya ko motsa su haka suka haƙura suka fice, suka je suka sanar wa comissioner, asibiti ya ƙira don jin ko ta farka aka tabbatar musu da ta farka sai dae ba kanta, statement din ta suke son samu su tura shi court don haka ya bada umarni a cigaba da mishi horror kala kala har sai ya faɗi gaskiya.

****

Daga Maami har Alayah babu wadda ya motsa tun da suka shigo asibitin, dangin Maami da na Abba na nan birjik Abba na halin mutuwa ko rayuwa sbd jininshi da yayi hitting fiye da ƙima, Ƴan uwan Maami sai jimami suke yayin da Ƴan uwan Abba ke jefo kananun maganganu wadda kai tsaye Maami suke alaƙantawa da lalacewan Mukhtar, ita dae tana jin su bata tanka ba kuma ta gode Allah da yaddikonta dake wurin ta hana duk sisters din ta magana, Baba ne ya shigo ward ɗin da sauri Maami ta miƙe ta isa gabanshi hannunta ya riƙo
"FaÉ—imatu!"
Kaman jira take ya kira sunanta kawai ta zame ta fashe da wani irin kuka dake cin ta a rai, Mukhtar kila sai ya kasheta ne hankalin shi zai kwanta, in ta bar mishi duniyar sai ya fi jin daaÉ—inta, zuciyarta ya riga ya kuntata fiye da tunani, ita kaÉ—ai ta san me take ji a ranta kunnuwanta kawai ke jin duniya gabaÉ—aya na tsinewa Mukhtar, kukanta sai da ya sa mutane dayawa kuka ciki har da Alayah, mahaifinta ya É—ago ta suka isa kujerun gefe guda suka zauna nasiha ya dinga yi mata akan jarabawar Allah, har misali yake bata da Æ´aÆ´an annabawa suma Allah be bar su ba, ko ta manta jinin Annabi Adam shi ya fara kisa a duniya? Ta mance Æ´aÆ´an annabi Yakub É—an uwansu suka so halakarwa mahaifinsu yayi kuka har idanunshi suka makance? Ko ta mance É—an annabi nuhu da ya kafurce yayi ikirarin hawa tsauni zai taimaka mishi wurin gujewa fushi da azabar Allah kuma Allah ya halaka shi a kan idanun mahaifinshi? Ta natsu ta cigaba da Adu'a idan yana cikin masu shiryuwar Allah zai shirya shi, sossai hankalin ta ya kwanta da nasihun baban, inda ya duba jikin Abba kan ya É—auki yaddikonta suka tafi kafin ya tafi sai da ya sake kwantar musu da hankali ita da Alaya.
Chapter 26 · 0% Book details