Sashe 31
Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ta buɗe idanunta da suka sauya sossai ta zuba mishi su, zare hannunshi yayi daga goshinta chan ƙasa yace
"Are you alright? Da wata matsala ne?"
Da idanu ta amsa shi don bakinta yayi mata nauyin buÉ—ewa.
Gefe ya ɗan kalla sbd yadda idanun suke wani irin tasiri a jikinshi, Miƙewa zaune tayi a hankali tace
"zaka fita ne?"
Sai a lokacin ya É—an kalleta yace
"zan je wurin baba, me kike so in taho miki dashi in zan dawo?"
Murmushi ta É—an saki shima yayi, Dukda babu wani shakuwa na musamman a tsakaninsu babu tsoronshi a ranta kaman kwanaki, hasali ma tausayinshi ya fi komai tasiri a gareta sai kuma tausayin É—an cikinta.
"Nama"
Ta faÉ—a a tsakanin lips É—inta
"wani iri?"
Idanunta ta É—an juya da alamun tunani kan tace
"ko wani iri me daaÉ—i dai"
"an gama maman unborn, na tafi"
"Allah ya tsare"
Ya amsa kan ya fice daga ɗakin, ajiyar zuciya ta sauƙe kan ta ɗan yi murmushi.
Tuƙi yake a natse yana murza siterin motar tsakanin hannuwanshi, wani irin yanayi yake ji a jikinshi da ma zuciyarshi, jinshi yake sabon mutum a hankali ya miƙa hannu ya kunna karatun alqur'ani da ɗazu yayi downloading Dukda manyan surorin da be iya bane sai dae jinshi akwai saukar da natsuwa, gidan baba malam ya isa saida ya shiga ciki suka gaisa da kakkaninshi da wasu Aunties din nashi kan ya tafi parlorn baba, maraba ya mishi suka zauna aka kawo abinci fura kaɗai ya sha, da tambayoyi baba ya fara abubuwa dayawa be sani ba hakan yasa baba ɗauko komai daga farko, Allah ma ya sa shi ɗin akwai kwakwalwa da kam ba karamar wuya ze ci ba wurin koyon addini, kuma abin ka da wadda ya saka kai sossai ya natsu ya ɗauki karatuttukan ranan, sai goma na dare ya mishi sallama ya fito.
Sai da ya tsaya ya sayi kaji gashin oven da aka yi su cikin wani hadaddiyar sauce na albasa da kuma Irish guda huɗu da su youghurt kan ya nufi gidan, a parlor ya sami Maami dake ta zuba ƙamshi tana kokarin tafiya part din Abba, da murmushi ta tare shi tare da wara hannunta ya matso yayi Hugging ɗinta tace
"ka dawo?"
"Eh Maami na dawo"
"ya karatun? Fatan an yi abin arziki"
Yana murmushi yace
"Eh Maami, na koyi dayawa har fa baba na mamaki"
Kai ta jinjina cikin jin daaÉ—in da ya kasa boyuwa mata tace
"Masha Allah, Allah ya sa a É—ore a haka"
Ya amsa da Ameen
Ledar hannunshi me kaji biyu ya miƙa mata
"Maami gashi a tafi wa Abba da shi"
Karɓa tayi ta mishi Adu'a kan ta juya kitchen zama yayi yana jiran ta fita don kunyar haurawa wurin Alayah yake a kan idanunta, a tray ta haɗa musu kan ta fito ta mishi sai da safe.
Sai da ta fice daga sashen ya miƙe ya shiga kitchen ɗin, yadda ya ga ta haɗa ya haɗa Dukda be iya ba duk ya ɓata jikin plate ɗin haka dae ya kokarta kan ya saɓi tray din ya haura sama dashi, a hankali ya ɗan yi knocking kan ya buɗe ya shiga tana tsaye ta gama saka night gown ɗinta kenan wadda dogon Cotton gown ne har ƙasa da tsagu gefe da gefe, cikinta ya ɗan tasa kaɗan akan rigar ya mata kyau sossai, murmushi yayi mata ta ɗan mayar mishi kan ta nufo shi ta karɓi tray din.
"Sannu da dawowa"
"yauwa fatee"
A ƙasa ta ajiye tray ɗin kan tattausan rug carpet dake shimfide a wurin, ya ƙarasa ya zauna ita ma ta zauna, shi yake cire mata ƙashi sai ya bata tsoka, Dukda ba wani hira suke ba moment ɗin ya mishi daaɗi ashe haka samun cikakken natsuwa yake? Godiya kawai yake yi wa Allah da ya bashi daman zama mutum a karo na biyu, sai da tace ta ƙoshi kan ya kyaleta ta miƙe ta shiga toilet ta barshi yana ci, brush tayi ta fito ta isa kan gado ta kwanta lamo gabanta na faɗuwa Allah Allah take ya gama ya tafi, tana kallonshi ya gama ya tattare wurin ya kai bakin kofa ya ajiye kan ya dawo ya shiga toilet ɗinta ya wanke hannu tare da kuskure baki ya fito.
Yana fitowa tayi hanzarin rufe idanunta tana damke blanket da take ciki dukda iyakarshi kan kwankwasonta ne, taku yake yana nufan gadon inda yake tafiya da bugun zuciyarta, murmushi ya saki ganin yadda take mirmisa idanun sai motsi gashin idanunta ke yi wai ita a dole tayi bacci, a ɗan space da ta bari ya ɗosana duwawunsa ya sanya hannu daga gefenta kan gadon ya tokare hakan ya bashi damar yi mata rumfa da faffadar kirjinshi, fuskanta ya zubawa ido yana ƙare mata kallo, tsawon dakika goma, kasa juran kallon tayi ta fara buɗe idanun a hankali har suka faɗa cikin nashi, murmushi ya ɗan saki yace
"Me baccin ƙarya"
Ta ɗan yi murmushi, idanunta ta kai kan hannunshi dake saitin kwankwasonta daga kan idon hannun har ya ɓace zuwa cikin half jumfar dake jikinshi wadda iyakacinshi damtsen shi daga sama duk tatoos ne a kwance, kallon hannun da take shima ya saka ya ɗan kalla, hannunta ta kai ta ɗan shafa tace tana maida idanunta cikin nashi
"Yana fita?"
Kai ya gyaÉ—a mata
"A da ne ba'a samo technologyn cire shi ba, amma yanzu ana iya gogewa"
Ta haɗiye miyau tace chan ƙasa kaman yadda shima yake mata magana
"Da me ake gogewa?"
"Da wuta kaman yadda aka yi shi da wuta"
Idanunta ta É—an zare
"kuma ba zafi?"
Cikin kwaikwayan maganan ta ya ce
"akwai amma mijinki jarumi ne"
Murmushi tayi, shiru ya É—an ratsa su idanunshi dake ta yawo bisa kanta duk ya bi ya tsarga ta, har gwara suna maganan ma da suna zaune shirun nan.
"Gobe in Allah ya kaimu zan fara zuwa makaranta"
Kai ya gyaÉ—a yace
"Allah ya kaimu in zan tafi Hameed auto motors sai in yi dropping naki from their za ki duba motar da ya miki sai mu fara koyon driving"
Cikin jin daaÉ—i ta mishi godiya, idanunta ta É—an lumshe ta sake cewa
"in na tashi ina so zan je asibiti ne na duba ummi"
Da sauri ya ɗan kalleta Sharp ya mance da zancen mahaifiyar tata, tunanin haduwarsu na farko kuma na ƙarshe yayi inda ya tureta a hanya har ta faɗi a sume, a take yanayin shi ya sauya, hankalinshi ya so tashi sai yaji hannunta kan kumatunshi ta ɗan shafa dole ta sa ya maida idanunshi cikin nata
"Karka damu, ummi tana da sauƙin kai da fahimta, bazata ƙi ka ba musamman in ta farka ta samu ka sauya kana kuma kular mata da ni yadda ya kamata"
Ajiyar zuciya ya ɗan sauƙe yace
"in shaa Allahu kan ta farka É—in zan tabbatar da na baki kulawar da ba zata iya gane ki ba ma ta ganki"
A tare suka yi murmushi, hamma ta saki
Yace
"bacci ko?"
Kai ta gyaɗa mishi, ya duƙa yayi pecking goshinta a hankali ya ɗago idanunshi akan lips ɗinta baya so ya kai nan don bashi da control a fannin, kuma ba zai iya kusantarta ba har sai ya je asibiti ya tabbatar da lafiyanshi, bargonta ya ɗan ja ƙasa yayi pecking cikinta tafin hannunshi ya ɗaura a kai, yace a hankali
"Kuyi bacci cikin aminci, Allah ya bamu alkhairi"
Ta É—an yi murmushi tare da furta Ameen kan ya ja mata blanket É—in har kirjinta ya sake pecking cheek É—inta kan ya juya ya nufi kofa tana ta kallonshinshi saida ya dau tray din kan ya kashe mata wuta ya fice, ajiyar zuciya me karfi ta sauke a hankali ta furta
"Alhamdulillah"
Sake dunkule wa tayi a cikin bargon a take natsatsen bacci ya dauƙeta, shima yana isa ɗakinshi ya watsa ruwa ya kwanta saida ya sake bitar karatun su na ɗazu kan bacci ya ɗauke shi.
Karfe huɗu da rabi alerm ɗin shi ya tashe shi, a natse ya miƙe ya shige toilet yayi alwala ya zo ya sanya Black jallabiya da ya mishi kyau sossai ya amshi skin dinshi dole yau zai je ya nemi kaya don da ya tsaya gaban kayakinshi na gidan duk babu na kirki, duka kyauta da su zai yi a yau, fita yayi ya tafi ɗakinta ya tashe ta kan ya fito, a haraba suka haɗu da Abba suka nufi masallaci dake kofan gidansu anan suka yi raka'atanil fajir wallahi be taɓa jin natsuwa irin na daga jiya zuwa yau ba a rayuwarshi, har suka yi sallahn asuba wani irin nishadi yake ji, ko da mutane suke fita shi qur'ani ya ɗauko ya cigaba da bitar ƙarin su na jiya, sai wuraren bakwai ya bar masallacin ya dawo ɗaki ya ɗan kwanta.
Karfe goma daidai ya fito a shirye cikin half jumpa ruwan ƙasa da ya kama shi ya mishi kyau sossai, tuni ya aske kanshi don haka hular shi ta zauna sossai ya fito a babban mutum me cike da natsuwa da haiba, a parlor ya same su, itama ta shirya cikin baƙin lace me adon peach ya mata kyau sossai, gaishe shi tayi ya amsa yana tambayar lafiyanta kan ya duƙa ya gaida Maami itama ta amsa cikin kulawa
"har kin shirya kina ta jirana ko?"
Tace
"A'a yanzu nima fitowana Yaya"
Dining ya wuce ta miƙe don serving nashi sai murmushi Maami ke zabgawa tana kallonsu gwanin sha'awa.