← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 36

Sashe 10

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alaya kam ita ta zata irin cikin kawayen hajj Zeenat ne yanzu su juye abu su ci musu mutunci, a tsorace ta zube ƙasa tana baiwa hajiyar da kai tsaye ta saka ta a top class hajiyoyi masu naira da isa haƙuri, bata taɓa ganin irin ta cikin ƙawayen hajj Zeenat ba don duk yadda zata misalta kyau da haiba irin na wannan mata me cike da annuri ba zai misaltu ba.

Hannu ta sanya ta É—ago ta
"Babu komai ai baki kula bane, yi min iso zuwa ciki ban taɓa shigowa gidan ba sai yau"
Matar sam bata da girman kai irin na manyan masu kuÉ—i É—in nan Alaya ta ayyana a ranta kan ta shige gaba Maami ta bi bayanta har cikin parlor, bata je kiran Hajiya ba seda ta kawo mata ruwa da É—an abun motsa baki kan ta shiga wurin hajiyar ta jima a tsaye kan ta amsa mata ta dawo ta shige kitchen ta cigaba da aikin da take kan a kira sallah ta saki taje tayi.

Cikin ƙasaita Hajiya ta fito Dukda ganin wannan gansamemiyar hajiyar ta san ba irin wacce za'a dagawa kai bane hakan be sa ta saita kanta ba ta samu wuri ta zauna a hakimce tana lura da kyau da kayan alatun dake jikin matar.
"Sannu da zuwa"

"yauwa Hajiya, kece mahaifiyar yarinyar da Abban muktar ya nemarwa aure?"

Daidai Alayah ta fito don tambayar hajiyar abinda ta ce za'a ƙara bayan na time table yau.
Idanu duka ta fitar kaman an danganta ta da wani mummunan abu tace
"Allah ya tsare ni da haihuwar mugun iri, kin ganta chan sai ta dangana ki da kurmar uwarta tunda dae kun ji kun gani, a sauƙa lafiya in kin tashi!"
Tana kai nan ta fice daga parlorn babu ko waiwaye, da farko jin irin gidan da za'a aurar da Alayah ta so ya haɗasu da jamila ne saide jin irin hallayyar yaron tayi tirrr da aurenshi, don a ganinta bashi da wani anfani, ko da uban ya faɗi ya mutu ko uwar dukiyar da zai gada bazasu je ko ina ba zasu ƙare a shaye shaye da bin mata, bata Gaza ba wurin tabbatarwa da Abban jameelar cewa in har dae suna da wani ɗan natsatse sai yayi kokari wurin ganin ya haɗa jamila da shi, be dae tanka ba amma ta san zai yi nazari akan hakan.

A chan parlor kuwa, idanu mami ta zubawa Alayah da kanta ke ƙasa cike da kunyar matar sai a lokacin ma ta fahimci kamanni dake tsakaninsu da muktar din, amma me ya kawota?

"Daughter ko zaki iya rakani wurin mamanki?"
Ta tsinci Muryar hajiyar, da sauri ta É—aga ta kalleta sai matar ta sakar mata kyakyawar murmushi, itama kakalowa tayi ta mayar mata kan tace cikin sanyin muryarta
"Toh Hajiya mu je"
Miƙewa Maami tayi ta bi bayanta har sashensu, da ɗan mamaki take kallon yanayin parlorn, kujerun da suka gama tsofewa duk dollof ɗin su waje Alaya ta nuna mata
"bismillah bari na kira ta"
Tana kai nan ta nufi kofa guda É—aya dake sashen ta bar Maami da tsananin al'ajabi...

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment

                  🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page seven*

Cikin tsananin tausayi da mamaki take kallon sashen nasu sai de tayi matukar kokari wurin boye yanayinta har ta kai zaune tana É—an kallon kofan É—akin da Alaya ta shiga, bata fi minti É—aya ba sai gata da matar da bata bambance dayan biyu mahaifiyarta ce sbd kamanni Dukda Alaya ta zarta ta kyau nesa ba kusa ba.

A hankali Alaya tace
"Hajiya bazata iya jin ki ba"

Tsananin tausayinsu ne ya kara rufe Maami tace
"Sunana Maami bana so ki sake ce min Hajiya, tana iya karatu?"
Kai Alaya ta gyaÉ—a.
Jaka Hajiya binta ta buɗe ta fiddo joter da biro tayi rubutu kan ta mikawa Ummi da biro ɗin, ummi da yanayin matar ya kwanta mata ta karɓa ta karanta cikin tsananin mamaki ta sake ɗaga idanu ta kalli Maami sai yanzu take iya hangen kamannin, tattaunawa mai ɗan tsawo suka yi a rubuce, duk yadda Maami taso ummi ta nuna kirkiri bata son haɗin hakan bai samu ba sai ma bi da tayi ta wata siga irin ta mai hankali da sanin addini wadda hakan ya mugun yiwa Maami daaɗi, taji matukar daaɗin kasancewa dasu daga karshe ta fara jefawa Alaya tambayoyi yawanci akan karatunta ne kan tayi mata alkawari ko ta auri muktar karatun ba zai tsaya ba wadda hakan yayi mugun sata farin ciki tayi ta godiya, su ko cikin kunyar ko ruwan da zasu bata babu Alaya ta fara bata hakuri tayi saurin nuna ba komai da ta tashi tafiya kudi masu yawa ta fiddo ta ajiye duk yadda ummi taso ta bari ta ƙi haka ta tafi cike da tausayin waennan rayuka biyu da Allah ya tsirga mata.

RANAR JUMA'A

Tunda gari ya waye gaban ummi ke aikin faÉ—uwa sbd Maami ta faÉ—a mata a yau ne suka yanke za'a É—aura auren, ta kwana kan sallaya ta kwana tana kaiwa Allah kukanta, da safen kuwa lokaci lokaci ta kan share hawaye, ba irin tunanin da bata yi ba idan har suka tsallake suka bar gidan nan shikenan tayi sallama da Ahmad da komai nashi, idan suka bar gidan saide su koma kaman sauran Abzinawa masu bara a titunan Nigeria, bata da wadda zata komawa a yanzu bata da kowa da zai iya rungumarta a wannan yanayi.

Aiki take saide lokaci lokaci ta kan ɗaga idanu ta kalli Alaya hawaye na zuba a idanunta, daidai sadda Abban Jameelah ya shigo da karfi ya jefa mata ledar hannunshi wadda yayi sanadiyar watsewar alawa da goro dake ciki, a firgice Alaya ta miƙe tsaye tana kallonsu yayinda ummi ta runtse idanunta daidai lokacin da Abban ke cewa Alaya
"Ga Alawar aurenki an ɗaura yau kuma ki shirya da dare zaki bar min gida, nayi matukar jinjinawa kokarin da nayi akan ki alhalin ke ɗin ɗiyar wadda ban taɓa so bane a rayuwata, ke ɗin ɗiya ce da mahaifinki bai taɓa ƙaunata ba, duk wani dama da ya ga zan samu ya kan yi hanzarin sha min gaba ya karɓe hatta kaunar iyayena bai barni da shi ba! Ki sani daga sadda kika fita daga gidan nan ko da sunan ziyara bana kaunar sake ganinki cikinta bare ki kashe aure ki dawo min, in kin fita duk abin da zai same ki ya kare a chan don Wallahi kika shigo min gida duk ya faru dake kiyi kuka da kanki"

Razananniyar kukan da take ta yanke daga karshe tana kallonshi irin kallon da bata taɓa tsayuwa tayi mishi ba, kalamanshi ba abunda zata iya aiwatarwa ba ne taya yana tunanin zata tafi ta ƙi juya baya alhali ta san ta bar mahaifiyarta cikin wannan gida?
"Alhaji mahaifiyata fa? Da kake wannan magana taya zan rayu cikin kwanciyar hankali in kasa waiwayen gidan nan alhali ka san duniyata na cikinta?"

"Wannan kuma ke ya shafa Fatima, abunda na sani mahaifiyarki kamar mallaki na ce babu inda zata kuma ban amince ki shigo min gida ba and this is my final decision"
Daga haka ya fice.

Zubewa tayi akan tile É—in kitchen din tare da É—aura hannu a kai tana me sakin sabon kuka, da sauri ummi tazo ta É—aga ta tare da sanya ta jikinta tana jin yadda jikinta ke É—aukan rawa kuka take kaman ranta zai fita, bata san me tayiwa wannan rayuwa ba, shin ummi bazata faÉ—a mata abin da mahaifinta yayi mai zafi haka ba?

Da kyar ummi ta samu hankalinta ya É—an kwanta Dukda bata bar zubar kwallar ba, idanunta gabaÉ—aya sun sauya haka numfashinta da zafi zafi yake fita, wani mumman zazzabi da ciwon kirji ya kwantar da ita haka ummi ta saka ta a gaba tana zub da hawaye babu mai taimako, Dukda ta sha duk magungunanta saide hakan be kwantar da ciwon da ya fara barazanar ganin karshenta ba, addu'a ummi ta dinga yi har Allah yasa bacci ya É—auketa na wahala.

Haka ta koma cikin gidan ta ƙarasa aikin da suka bari ta dawo ta zauna jugum tana tunanin rayuwa, Dukda ta kasance marar gata irin Alaya saide aurenta bai zo a haka ba, aurenta da rufin asiri da kuma taron mutane aka yi shi, sallah ne kawai ke dagata har dab magarib kan Alaya ta farka, da taimakon Ummin tayi wanka ta sake shan magunguna abinci kam ya kasa shiga cikinta, a kwance kan cinyar ummin ta lumshe idanu bayan ta idar da sallolin da aka biyo ta ta fara jin Shigowar motoci da ƴar hayaniya kaɗan na mutane.

Bata motsa ba har aka yi musu sallama, da gangan ta ƙi amsawa kila in bata amsa ba su juya su koma inda suka fito a yau me rabata da ummi kilan sai mutuwa bare in ta tuna irin furucin Abban Jameelah a kanta, Shigowar Maami ne ya sa Ummi sakin ɗan murmushi bayanta mata ne akallah zasu yi ashirin.

Danginta ne kadan sai dangin mijin da suke ta kananun maganganu na mamakin zuwanta É—aukar amarya alhali É—an ta ne na fari kuma kowa ya san rashin jituwarsu saide tayi kunnen uwar shegu dasu kaman bata san suna yi ba wai an tsikari kakkaura, a hankali da taimakon ummi Alaya ta samu ta zauna tana zub da hawaye ta gaida Maami, cikin kulawa ta amsa kan tace
"Binti ya baki shirya ba?"
Chapter 10 · 0% Book details