← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 36

Sashe 33

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaye take gaban dressing mirror tana shafe tattausan skin ɗin ta da mai fitowanta wanka kenan, wani irin zafi take ji sannan kirjinta ya tokare sossai wadda rabon da ta ji ciwon zuciyarta ya motsa ta mance sai dae rashin ƙiba da nauyinta na nan, ta dae murje ta ƙara kyau sossai, cikinta ya fito sossai sossai bayan ta gama ta feffeshe jikinta da turarukan ta mabanbanta a take ɗakin ya bule da sassanyar kamshin, night gown da be da wani nauyi da tsawo ta saka tana kokarin tufke gashin kanta ya turo kofan ya shigo, ta madubi suka sakarwa juna murmushi.

A hankali ya ƙaraso ya ajiye tray din hannunshi kan ya nufeta slowly yayi Hugging ɗinta ta baya very tide yana zagaye hannunshi bisa kan cikinta a lokaci ɗaya ɗan cikin yayi motsi suka saki dariya a tare
"ka ji min yaro da gulma"
Yace
"kyaleshi ya marabci babanshi watarana sai labari"
Kallonshi tayi sai ta ga ya É—an faÉ—a mata, sajen da ya tara ya mishi kyau ainun, tafin hannunta ta sanya ta É—an shafa sajen tace

"Ya Mukhy menene yake damunka? Jikinka da É—an zafi kuma ramarka tun bata fita har tana nunawa, can you please share ur problem with me? Karka manta turawa fa sun ce a problem shared is a problem solved"

Sakinta yayi ya karɓi ribbon ɗin hannunta yana tufke mata gashin yace
"bani da damuwar komai Fatee, in da ina dashi ba zan ƙi faɗa miki ko Maami ba saboda har duniya ta nade bani da tamkarku"

Bayan ya gama ya ja hannunta suka zauna bakin gado sbd zaman ƙasa na mata wahala yanzu, ya buɗe soyayyayiyar Irish da aka yi ta da liver sauce ya fara bata tana ci, sai da ta ƙoshi ta karɓi spoon ɗin ta dibo zata kai mai baki ya riƙe yana saukewa a hankali yace
"bani da apetite ba zan iya ci ba"
Tace
"kuma dai? Ya Mukhtar kullum fa haka kake cewa da matukar wahala ka sha wani abu ma bare ka ci abinci me nauyi"
Murmushi ya sakar mata.

Miƙewa yayi zai fita da kwanukan ta riƙe hannunshi
"zaka kwana anan? Ko in zo?"
Ya kalleta yace
"bari naje na dawo maman unborn tunda yau so ake a danne min kirji"
Tana dariya ya fice, toilet ta shiga tayi brush ta ƙarasa kimtsawa tana zama yana shigowa sanye da jallabiya coffee Brown me taushi, jallabiyar ya cire ya saura daga shi sai dogon wandon bacci ya haye gadon ta kuwa samu masauki a kirjinshi suka yi Light off bata jima ba bacci ya sure ta.

Sai da ya bari tayi nisa a baccin ya maidata kan pillow ya kwanta, baya so ya tashe ta cikin dare sbd ya san kanshi, juye juye kawai yake sbd baccin da baya samu a kwanakin gabaɗaya, chan kuma zufa yake ta karyo mai Dukda Ac dake ta aiki a ɗakin kusan kure wa tayi, ya yaye bargon yana cigaba da ɗan juye juye, wuraren sha biyu ta farka fitsari idanunta suka sauƙa kanshi.

Taɓa shi tayi sai taji hannunta ya sauƙa kan zufan dake ta gangara a jikinshi, wuta ta kunna sai suka haɗa idanu
"Ya Mukhtar zafi kake ji haka? Ko mu kunna standing fan?"
Yace
"No karki damu zan watsa ruwa yanzu ina jira ne ɗaya yayi gabaɗaya in miƙe nafilfili na"
Sauƙa tayi ta shiga toilet tayi fitsari kirjinta ke damunta da ciwo tana tunanin dole gobe taje meddy, ta fito ta zo ta kwanta ya kashe wutan don ya san bata iya bacci da wuta a kunne.

Bata iya ta yi baccin ba, tana ta kallonshi ga dukkan alama duk daren be yi bacci ba, ya kwana biyu da tayi noticing rashin baccin shi, in yayi ma baya wuce awa guda duk tsanani, tana ta kallonshi har ya sauka ya shiga toilet ya jima wadda ya tabbatar mata da wankan yayi kan ya fito ya sanya jallabiyanshi ya tafi wurin sallahnts ya fara nafilfili, tun tana kallon shi har bacci ya sure ta.

Karfe uku ta sake tashi fitsari ta samu yana karatun alqur'ani da yanzu yayi nisa sossai kuma yana fitar da duk wani makharij da kiyayewa sossai a karatu, ta jinjinawa namijin kokarin shi don yanzu ko ita bazata nuna mishi ibada ba, taje tayi fitsari itama tayi alwala ta zo tayi raka'a huÉ—u kan ta koma ta kwanta, sai asuba ya tashe ta ya wuce masallaci.

Ko da ya dawo a kitchen ya samu Maami tana shirin haÉ—a abin kari
"barka da safiya Maami na"
Tace
"barka dae my son Fatan ka tashi lafiya?"
"Alhamdulillah Maami yau ke da kanki ne a kitchen, to da me zan taya ki nima in samu ladan?"
Cikin raha tace
"Me ka iya? Da Kai da É—an uwanka duk jirgi daya ya kwaso ku ruwan zafi wannan baku iya tafasawa ba in ba da kettle ba"

Yana dariya yace
"Ai kitchen ɗin nan sai ku mata Maami ina ganin kokarinku duk abu da ƙuna, yanka bani ciki"
Sukayi dariya a tare, Maggi ta bashi yana ɓare mata chan yace
"Maami autan ki zuciyarshi tayi yawa, har yau ya kasa sakewa da ni be san kuma bamu da wani lokaci ba"
Itama hakan na damunta har yau be zo ba, babanshi ma na complain na ko ya kira daga sun gaisa shikenan
"ko da shi ke ma Maami kyale shi, dama zaani ne ya tadda muje ni, ga hali kuma ga yanayin aikinshi"
Ya katse ta don ya san tunanin amsar da zata bashi don kar yaga tana kare umar ne ta bar shi take yi.
Wani hiran suka kama har ta gama breakfast din yana tare da ita, shi ne miko wannan miko wanchan, dibo ruwa.

Masu aikinta ne suka fitar da abincin zuwa dining daga shi har Maami suka je suka yi wanka kusan a tare su huÉ—un suka fito, Mukhtar ya ja wa Abba kujera yana zama yace
"Abba yau zaka ci girkina na san sai ya kai maka karo bari na tabbatar da lafiyar kujerar nan kar santi ya kwashe ka"
Dariya suka yi Abba yace
"tafi nan, da de bamu san asalin balbela bane kai yaushe ka iya ko kunna gas din ma? Ko binty ya iya?"
Ya faɗa kaman yadda ya riƙe bakinshi saboda yawan faɗan Binty da Maami take. tana dariyar yadda ya kwabe fuska tace
"Babu abin da ya iya Abba"
Yace
"Maami faÉ—a musu don Allah ba ni nayi ba?"
Tace
"kwarai kuwaaa"
Yadda ta faÉ—a da alamun tsokana a muryarta yasa suka kwashe da dariya Abba na cewa
"faÉ—i gaskiya dai daga jin wannan amsawan naki da walakin goro a miya"

Abincin suka fara ci cikin natsuwa, jujjuya cokalin kawai Alayah take yi, Mukhtar da ya lura yace
"Fatee lafiya? Ko wani abu na damun ki ne?"
Shima ba ci yake ba ruwan zafi yake É—an kurba.

Maami tace
"Binty akwai matsala ne?"
A hankali tace
"Maami kirjina ke ciwo sossai"
Abba yace
"Subhallahi Meyasa baki yi magana tun É—azu ba? Mukhtar tashi maza mu wucenku asibiti"
Duk abincin suka bari Maami taje ta É—auko musu mayafi zuwa lokacin ko tsayuwa Alayah bata iya yi tuni suka yi meddy specialist hospital hankalinsu a tashe.

*Har yanzu dae ana nan a free pages karku manta book 2 na kuÉ—i ne zaki iya biya ta wannan asusu
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin sai ki tura shaidar biya ta wannan layi 09039206763*

🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
     (heart touching story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)

Adabi Writers Association

Book 1
*Page Twenty Four*

Dr Philips ne ya yanke musu tsawon lokacin da suka É—auka suna jiran tsammani, da hanzari duk suka isa kusa dashi kowa na rige-rigen tambayar ya take?
"Akwai contraction between her illness nd the baby, dole za'a yi mata aiki a cire shi a watanni bakwai in ya so a bashi duk wani kulawa a incubator she cannot take it for completely nine months”
Duk jikinsu yayi sanyi, sai da ya basu kwarin gwiwa ya tabbatar musu da ikon Allah in an cire they will be all safe, tuni aka kawo papers Mukhtar ya saka hannu.

Bai sani ba ko don saboda firgicin da yake ciki ne ko kuma wani abu na daban wani irin hajijiya ya kwashe shi saura kiris ya faɗi Abba ya tare shi, suka zauna suka shiga kwantar mai da hankali, nurse ce ta fito tace zasu iya su ganta kan a shiga aikin, duk suka miƙe suka nufi ɗakin, murmushi ne kwance a fuskanta ta kalli Maami ta miƙa mata hannu, da sauri Maami taje ta riƙe Alayah tace
"Maami ko a yanzu na mutu kun gama min komai, kun bani farin cikin da na rasa tsawon shekaru, Maami ko da wani abu ya sameni ina da tabbacin zaku cigaba da kulamin da ummi, idan kuma Allah yayi ikonsa bamu yi sallama ba ku tabbatar mata da cewa na mutu da ƙaunarta kuma ku ce don Allah ta yafemin"

Da sauri Mukhtar ya sa hannu a bakinta ya rufe
"Haba fatee wani irin zance kike yin nan? Mata nawa aka yi wa Cs suke cigaba da rayuwa har ma su cigaba da haihuwa, ki daena irin wannan furuci kin ji, zaki haihu lafiya zaki rayu ki kular min da baby har zuwa jikoki"
Abba ma yace
"zaki samu lafiya kin ji? Allah ya raba lafiya yasa ayi cikin nasara"
Maami dae ta kasa magana sai shafa kanta da tayi tana mata Adu'a suka fice suka bar Mukhtar.
Chapter 33 · 0% Book details