← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 36

Sashe 8

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Alaya na isa ta zube ta cigaba da kukanta tana jin radadin na ratsa ta, da sauri ummi ta ɗago ta tana tambayarta abunda ya faru amma bata amsa ba duk laifin ummin take gani, sai da ummin ta jijjigata da karfi tana mata alama bakin ta na irin ɓaɓatun maganan kurame dinnan
"Alaya ki dawo hankalinki, duk abunda kika ga na yi sbd ke ne da rayuwarki, nima ba zan zuba ido a zalunceki a ɓata miki rayuwa da gangan ba, menene ya faru? Ki min magana..!"

Alama take mata tana sakin wani kukan a haka ta bata labarin abunda duk ya faru, hijabin ummi ta zare mata abunka da farar mace nan da nan jikinta ya tashi yayi jajazir daga wuyanta har kirjinta, wani abu me ɗaci ummi ta haɗiye ta miƙe ta fice chan ta dawo da kƙullun kunu sbd ana yiwa Abban Jameelar tazo ta shafa mata duk wurin kunar ta zauna ta sanya ta a gaba tana kallo yayinda baccin wahala ya ɗauke ta.

Bayan kwana biyu

Tun daga randa ta ƙone bata kara fita daga sashen ba komai ummi ke yi Dukda damuwa da ya mata yawa, yake kuma cin zuciyarta hakan be hana tayi musu duk aikin da suka saba yi ba, Alaya kuwa tun ranar bata iya zuwa makaranta ba duk son ta da boko kuwa.
Yau dae ta miƙe ta shiga cikin gidan don kamawa umminta aiki tana cikin jera abinci taji gyaran muryan Abba da sauri ta juyo se ta kai gwiwowinta ƙasa kanta kasa gabanta na tsananta bugu.

"Muktar ze zo yau ku gaisa, make sure baki yi abunda ze zubar min da ƙima ba, parlorn baƙi na zaku zauna and ki tabbatar kin tsaftace kanki na rana ɗaya dae"
Yana kai nan ya wuce abun shi.

Bata iya ta miƙe daga tsugunon ba tsawon mintuna kan ta yunkura kitchen da bata koma ba kenan tayi chan baya ta fara zirga zirga...
Na shiga uku na wai da gaske Abban Jameelah ke yi? Shikenan haka zamu kare kaman bayi a chan lokacin jahiliyya? Babu irin nazarin da bata yi ba har da tunanin ko ta gudu se kuma ta tuna in ta gudu umminta fa? In ma ta gudun ina zata? Bata san kowa nata ba banda gidan nan da makaranta sai asibiti bata tunanin ta san wani wuri a fadin birnin jihar Kano.

Har aka kira la'asar bata iya ta taɓuka komai ba banda tunani da wani irin fargaba da ya cika mata zuciya fal, ganin lokacin Sallar na shirin fita yasa ta nufi sashensu sukuku da ita haka tayi sallah tana nan zaune ummi ta shigo ko kan tayi maganar yadda ta ganta ɗin taji sallamar iro me kula da shuke shuken gidan alama tayiwa ummi na ana sallama kan ta fice, a mutunce suka gaisa ya shaida mata tana da baƙo a sitting room na Alhaji..

Dawowa tayi tana share hawaye ta faɗawa ummi har abunda Abban Jameelah ya faɗa, bata ce komai ba har Alaya ta juya ta fice da kayan jikinta dogon riga da hijab da ya wuce mata gwiwa kaɗan, da idanu tayi ta bin zazzafar motar tashi kirar McLaren Mp4-12c wacce murafanta ma ta sama ake ɗagasu Red colour mirrors ɗin baƙaken sidik banda sheki babu abunda yake yi har ta isa kofar parlorn, ta dan jima anan tana daidaita bugun zuciyarta da fargaba hade da tsoro da suka cika ta kan ta tura kofar da sallama.

Ba'a amsa ba kutsa kai tayi ciki bata yi gigin dagowa ba ta ƙarasa ta tsaya a tsaye tace ina yini? Ba tare da ta ko zauna ba.
BuÉ—aÉ—É—iyar muryarshi da ta kara zurfi da amo sbd shaye shaye ya dira bisa kunnuwanta
"Kin ƙara mintuna ashirin da biyar daga kiranki zuwa yanzu mind you next time karki kuma, ba'a ɓata min lokaci a banza!"

Sai a lokacin ta iya ɗaga idanu ta kalleshi tana kokarin auna kalaman da yake faɗa mata cike da gadara da isa kaman shi ya ajiyeta, bata ce komai ba se kallonshi da take ba laifi don kyau kam kyakyawa ne na gasken gaske duk inda kake neman namiji wannan din da Abba ya kira da Mukhtar to ya kai, saide dressing dinshi na three quater da armless shirt ya bayyana munanan halayenshi kaman yadda baƙin lips ɗin shi ya nuna karara hayaƙi na aikinshi a wurin, daga kirjin shi zuwa dantsen hannun shi na dama tatoos ne da aka zana ya zanu sossai kaman kan zaki ko damisa ne oho..

Wani irin tsawa da ya daka mata yasa ta razana tayi baya tana wara kyawawan idanunta
"ba'a yi min shiru in ina magana am I clear?"
Bata amsa ba, hakan ya saka shi Miƙewa a harzuke ya nufeta gadan gadan, a tsorace ta fara ja baya yana kara matsowa har ta isa jikin gini ya matso sossai ya mata rumfa yana kare mata kallo
"young, beautiful and stubborn!" Ya faɗa yana taɓe baki
"ba laifi Dad ya iya zaɓe but kina bukatar sabbin karatuttuka a wannan lunatic brain ɗin"
Ya faɗa yana dannan saitin brain ɗin da hannunshi kauda kanta tayi idanunta suka cicciko, ya sanya hannu ya shafa fuskanta a firgice ta Buge hannun tare da sauke mishi marin da bata taɓa tunanin tana da wannan karfin halin ba, kankame jikinta tayi sbd kusancinsu tana kokarin zamewa ya fusgota tare da fusge hijab ɗin jikinta, ƙara ta saki ya Buge mata baki da gwuiwar hannunshi har saida jini ya fita yana furta...

"Shhhhh" idanunshi kaman garwashi da alama ma wani abun ya sha kan zuwanshi nan É—in
"Lallai yarinya kin yi kokari, Marin Muktar abu ne da ya kamata a tafa miki, trash like you, villager, wacce ke cike da rashin wayewa yau ke kika sa hannunki a fuskata, fuskar da mata dubu ke marari hmmm marin nan zan fanshe su ta hanyoyi daban daban ki rubuta ki ajiye the First one za ki tantance yanzu, sauran sai kin zo.."

Ko kan tayi wani yunkuri ya sanya hannu É—aya gaban rigar ta ji kake Kyaaaaat ya farke har farin vest dinta ya bayyana, ihu ta tsala tare da saka iyakar karfinta tana kokuwar kwace kanta sede shi É—in namiji ne da gaske ko gezau ta kasa motsa shi, kuka da ihu take tana neman É—auki daga Allah...

Gaban ummi ne ke ta faduwa tun fitan Alaya É—in ta kasa natsuwa, daga karshe sake aikin da take yi tayi ta nufi sitting room É—in tana kuma jin gabanta na tsananta faduwa.

Tura kofar da tayi ya ɗan yi karar alamar Shigowar mutum ne ya saka shi dakatawa daga abunda yayi niyya chakk, jajayen lumsassun idanunshi ya ɗago ya kalleta irin kallon zaki yi bayanin nan kan ya ja baya yana gyara wandonshi ya juyo, ita kanta ummin wani irin kallon banza yayi ta aika mata har ya isa daidai inda take kan ya daga hannu yayi mata alamar ta matsa, abunda ta gani ne ya daskarar da ita, idanunta na kan Alaya da ta zube bisa gwiwowinta tana gunjin kuka bata ankara ba taji an tureta an wuce, bata iya riƙe balance dinta ba se ta tafi a haka ta faɗi ƙasa sumammiya....!

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment

🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
     (heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page six*

A hankali ummin ke buÉ—e idanunta da suka yi nauyi, zuciyarta na bijiro mata da abin da ya firgitata, da ido ta bi environmemt É—in sai ta fahimci a asibiti take babu tantama hawan jininta ne ya tashi. Idanunta ta kai gefen ta sai suka faÉ—a kan Alaya dake dunkule cikin kujera idanunta a lumshe kaman mai bacci duk sun kumbure alamun ba karamin kuka ta ci ba, wani irin tausayin É—iyar tata ne ya rufe ta, lumshe idanu ta sake yi, ta gama yanke hukuncin amincewa Alhj Hassan da bukatar shi in har dae hakan shi zai sa ya kyale Alaya daga wannan mummunan rayuwar da yake shirin jefa ta, ko a mafarki kai ko a labarin tatsuniya bata fata ace wannan dodo da ta gani da idanunta yana shirin keta haddin É—iyarta a cikin gidan ubanta ya zama mijin Alaya. Me yasa ta kasa rike amanar Ahmad? Me yasa mutuwa ta mata yankan kauna? Ita kadai babu yadda ta iya da Alhassan, dole abin da yake so din nan shi zata yi...
Kuka ne ya kwace mata wadda ya saka Alaya da dama ba bacci take ba tunani take akan sabuwar ƙaddarar dake shirin riskarta tayi saurin ɗagowa da hannu take mata alamar ta tashi? Ya jikin? Ta dena kuka haka pls.
Chapter 8 · 0% Book details