Sashe 34
Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zama yayi ya riƙo hannunta tana kallonshi a hankali tace
"Ya Mukhy ba zaka faÉ—a min abin da yake damunka ba ko? Kana so in mutu ban san menene matsalarka ba ko?"
"Fatee na!"
Ya katse ta, ta lumshe idanu shi kadai ne yake kiranta hakan a duk fadin duniya
"Ya Mukhy"
Yace
"in kina so mu shirya karki sake maganan mutuwa, in shaa Allahu ba zaki mutu ba, not now not any moment from now..!"
Bata yi mamakin ganin hawaye kwance cikin idanunshi ba, peck yayi mata a Goshi ya sake yi mata a lips yace
"Ina sonki!"
Murmushi me kyau ta saki tace
"Nima ina kaunarka Yayana"
Miƙewa yayi saboda Shigowar nurses ya sake mata peck a Goshi yana shafa kanta yace a hankali
"Allah ya raba ku lafiya"
Ficewa yayi ba tare da ya sake kallonta ba sbd hawaye dake zuba mishi, ashe yana da rabon ganin É—an shi ko Æ´ar shi, ajiyar zuciya yake ta saukewa a kai a kai.
Wayan Abba ne ya ɗauki ƙara bayan tsawon lokaci suna zaune, dubawa yayi sai ya ga Umar ne, ɗagawa yayi da sallama suka gaisa yake tambayarshi Maami fa tun asuba yake kiran wayanta ba'a picking.
"Muna asibiti ne da matar Mukhtar za'a yi mata Cs, ga Maamin naku"
A hankali yace
"Allah ya raba su lafiya"
Maami ta karɓa suka gaisa ta ɗora da
"Lafiya kuwa auta kake ta kira tun asuba?"
Don ta ji maganansu da Abban ta sake É—orawa da cewa
"tunda nayi sallah na bar wayan É—aki zuwa kitchen ko da na gama abin kari ma naje nayi wanka ban duba ba kuma ka ga daga wurin karin ne muka yo nan asibiti ko abincin bata ci ba baiwar Allah"
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe ta ɓangaren shi tana jin sautin iska da ya fesar yace
"Ummi!"
Don haka ya ji Maamin na kiranta, da sauri ta miƙe tsaye
"Me ya sameta? Sun ƙiraka daga asibitin ne? Me suka ce?"
"Calm down Maami, ta farka ne cikin dare, farkawan kuma be zo daidai ba sai jikin ya rikice, tun 2 suka ƙira ni akan if possible ayi gaggawar fita da ita i don't want to call you that time so we arranged emergency craft aka ɗauketa daga nan zuwa saudi saboda chan ya fi kusa da nan Lyon, am presently at the hospital Doctors basu fito ba dai tukuna".
Ajiyar zuciya ta sauƙe tana zama cikin sanyi ta soma jero mata adu'ar samun lafiya tana kuma godiya wa autan nata, ta san ko Abban shi ne zai yi wannan dole za'a samu delay ba kaman shi ba da yake da connections masu yawa, bayan sun kashe take yiwa su Abban bayani adu'ar samun lafiya suka yi mata da kuma burin a fito da Alayah lafiya bayan ta warke su tafi chan gabaɗaya.
Some hours later
Dawowansu Abba daga Sallar azahar kenan likitoci suka fito suna musu albishir samun ƙaruwar ɗa namiji yana ma nursery a incubator zasu iya zuwa su ganshi.
Mukhtar yace
"maman fa?"
Cikin murmushi suka ce itama lafiyanta ƙalau bacci ma take, sai a lokacin tsantsan farin cikinsu ya bayyana a take Maami ta karbi wayan Abba ta soma kiran en uwa tana gaya musu matar mukhtar ta sauƙa lafiya, an sha mamaki kam don bakwaini ne aka haifo musu, kan ka ce karfe biyu en uwa da abokan arziki na ta zuwa sai dae a ga yaro a incubator tarr kamanninshi da Mukhtar kaman an tsaga kara.
Shi kam ba'a tantance wani yanayi yake ciki, yana nan zaune tare da Alayah har bayan la'asar ma Abadan kan ta farka, lafiya ƙalau ta tashi jikin kuma da ɗan ƙarfi dayake plaster ne aka mata ba ɗinki ba, ta ji daaɗi kwarai da ta samu labarin ɗan ta lafiyanshi ƙalau, saida aka kimtsata ta ɗan ci wani abu kan Mukhtar ya taimaka mata zuwa nursery don yaron ya ci abinci sai kuka yake, sun so ta matse aje a bashi sai dae Maami tace gwara dae ya ji ɗumin mahaifiyarshi.
Da ita da shi ne gaban incubator É—in wata nurse ta ciro musu babyn, Mukhtar ne ya soma karbar shi ya rungume a kirjinshi sassanyar hawaye na bin fuskanshi a kan lips dinshi yake ta furta
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!"
Adu'a yayiwa yaron don musamman ya koya saboda burin kaiwa ranar da zae ga É—an nashi a duniya Dukda bashi da wani kwarin gwiwa.
Miƙa mata ɗan yayi saboda nurse ta gama taimaka mata ta wanke bakin nonon kar yaro ya sha bacteria saboda kula irin tasu barin ma wannan da yake bakwaini dukda lafiyayye ne, saida ya ba yaron zamzam da dabino kan ya taimaka mata ta soma feeding nashi Dukda zafin da ya ziyarceta, ya sha kuwa yana ta sauke ajiyar zuciya.
Sun jima sossai wurinshi dab Magrib suka fito, ya kaita har É—aki kan ya wuce masallaci.
Kan ka ce kwana bakwai tuni ta koma normal tana komai da kanta har wanka, sai su sa leda a bakin wurin su ɗaure da zani ta yadda ruwa ba zai taɓa ba tayi wankanta, yaddikon Maami ce ta zauna da ita tana kula da ita sossai kuwa, kullum asibitin a cike, Mukhtar ya ce ba za'a yi taron suna ba walima ce a ci a sha ayiwa yaro Adu'a so a gidan Maami aka yi dukda ba yaro bare mahaifiyarshi, yayi hakan ne saboda sanin cewa haka annabi ya umurta da a yi ba irin na yanzu ba da za'a tara jama'a a saka dj wurin suna bayan albarka ake nemawa yaron.
Kowa ya shiga mamakin jin sunan ɗan wai Mukhtar sai dae babu wadda ya ce don me tunda uban shi ne ya sanya mishi hakan, ganin bashi da wani matsala a duk checkups da aka yi sai kawai suka sallame su bayan sun ƙara week kuma har lokacin Alayah bata san ummi bata ƙasar ba, a duk sadda Maami zata yi waya da Autanta ficewa take kuma yana tabbatar mata da tana samun sauƙi sossai yanzu har tana iya gane wadda ke kanta.
A sati biyun sau wurin uku yana zuwa daga wurin aikinshi a Lyon ya koma, taji daaÉ—i kwarai yadda ya É—auki ummin da muhimmanci Dukda be san ma wacece ita ba bayan surukar gidansu, wannan tausayi a jininshi yake.
Yau bayan Maamin ta gama yiwa baby komai yayi bacci a lokacin tabawa suka fito da Alayah daga bayi a bakin gado ta zauna ta soma kokarin shiryawa, ɗakin banda ƙamshin turaren wuta babu abin da yake fitarwa, wani kalar kunu ne da bata ma san ko sunanshi ba banda wani fitinannen kamshin kayan yaji da yake babu abin da yake Dada ne ke aiko mata kullum kuma tana jin daaɗin shan shi, ƙamshin shi da taji ne yasa ta kalli gefen gadon Maami ta tsiyaya mata sai turiri yake murmushi ta saki, jegon gata take ita kam bata da abin cewa ga Maami don ko ɗiyar da ta haifa a cikin cikinta karshen abin da zata yi kenan.
"Oya hanzarta kar kunun ya huce"
Ta amsa da to kan Maamin ta fice, agogo ta kalla karfe goma da rabi, sam bata ji motsin Mukhtar ba yau don haka ta nufi ɗakinshi, a kwance cikin bargo ta same shi zazzaɓi mai zafi ya rufe shi banda rawan ɗari babu abin da yake, da sauri ta ƙarasa kanshi ta yaye bargon tana cewa
"Subhallahi Mukhtar zazzaɓi kake yi shine ka shigo ɗaki ka kwanta kai kaɗai haka? Tashi mu tafi asibiti maza"
Tana kokarin juyawa ya riƙo hannunta, a hankali ya buɗe idanunshi da suke lumshe wa da kansu yace
"Maami ba wani abu bane ba fa, in na watsa ruwa na sha panadol zan samu sauƙi"
Girgiza kai tayi tace
"inaa ba zai yiwu ba Mukhtar, wannan ne kake cewa ba wani abu ba? Yaushe rabon da ka ci abinci a cikinka? Ina fa kula da al'amuranka zazzabin nan ya jima a jikanka kake yin shi tsaitsaiye ga rama marar dalili gwara dae mu je asibitin sai ya fi"
"Maami don Allah dae ba sai na je ba, bari na ƙira Dr Ahmad ma kawai zai zo ya duba ni a gida"
Ba don ta gamsu ba ta miƙa mishi wayan ya ƙira Dr Ahmad akan ya zo gida ya duba shi please, shakuwar dake tsakaninsu a yanzu ya wuce na patient da Dr sai na friends sun zama abokai sossai don a yanzu bashi da abokin da ya wuce Dr. Ahmad, ko kayan suna na ban mamaki ya aiko matar shi dashi kuma sau kusan uku tana zuwa asibiti da abinci niki-niki wa me jego har za'a iya cewa sun ɗan saba da Alayah.
Komawa É—akin Alayah Maami tayi ta samu ta gama shan kunun, dubanta Alayah tayi tace
"Maami ya jikin Ummi? Har yanzu ba wani chanji ko? Kullum da ita nake kwana nake tashi har na haihu ummi bata sani ba"
Ta ƙarasa hawaye na gangaro mata
"Ummi ta farka Alayah tana cigaba da samun kulawa"
Wani irin zabura tayi
"tana iya magana? Tana iya gane komai? Maami don Allah zan je asibitin na ganta! Na san tana chan tana tunanina babu bakin da zata ce a kira ni"
Maami tace
"in shaa Allahu zaki je Alayah, yanzu dae É—auki Wannan mijin nawa ku je ya gaida babanshi babu lafiya likita ma na hanya"
Tana cikin farin ciki kwarai da jin ummi ta farka tana samun kulawar da ya dace, Adu'a tayi ta yiwa su Maami, cikin jin daaɗi ta miƙe ta saka kayanta plain riga da zani, duba system ma dama take son yi sbd lectures dake ta wuce ta nan ma don farkon semester ne da a tsakiya ne ta haihu da ta ga bone, ba laifi kuma dayake tana da fahimta sossai ko a hakan tana ganewa sossai, dama su suna online class sossai sbd yanayin course na su.
Yaron ta É—auka yana ta muimui da baki, ta lakaci hancinshi da sak na babanshi tace
"dube shi, yanzu ya sha baccin shi anjima yace bamu isa mu yi bacci ba"
Murmushi ne kwance a fuskanta in ta ga wannan yaron sai tace oh yau ni Alayah ce na haihu, ni ke da yaro kyakyawa irin Wannan Alhamdulillah!