← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 36

Sashe 11

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi me ciwo tayi ina wani kayan shiryawan mutanen gidan kaman basu san da zaman su ba bare su yi tunanin kyautata mata a yau dai É—aya.
"Maami bani da lafiya ba zan iya tafiya ba, ba zan iya tafiya in bar ummi a wannan gida ba Maami don Allah ki ce ya barni ban shirya aure yanzu ba, don Allah karki rabani da ummi wallahi zan iya mutuwa"
Tayi maganan cikin sanyinta da kuma alamar roƙo da sallammarwa rayuwar gabaɗaya.

Da kyar Maami ta iya mayar da hawayenta tana karbar farin takardar da ummi ta miƙo mata
"ƴata na haifeta da ciwon zuciya! Don Allah ki kula min da ita da lafiyarta, ki riƙe min amanarta, ban san ko zamu sake haɗuwa nan kusa ba amma don Allah ina roƙon ki alfarma guda ɗaya a matsayinki na uwa kema, ki yi min kokari kan karatunta idan kika min wannan alfarma zan kasance me saka miki da addu'ar rahama da jin kan ubangiji har illa ma sha Allah..."

Kasa rike hawayenta tayi ganin yadda Alaya ta koma jikin ummin ta rike hannunta gam tana kuka sossai, Aure yakin mata hakane amma wannan kukan na Alaya ba na auren bane kawai harda na taradaddadin yadda zata rabu da mahaifiyarta alhali an gindaya mata sharudar sake ganinta gashi ummi ba fita take ba, matan wurin dangin mijin Maami sai kananun maganganu suke wasu na taɓe baki saɓanin dangin Maami da tausayi da kuma jin kai aka raine su Dukda iyayensu suma masu arzikin ne sossai da sossai.

Duk yadda Maami ta rarrashi Alaya ta kasa samun galaba a kanta, yadda ta rike ummi seda kowa yayi mamaki duk yadda akyi ta sake ta ta ƙi banda kuka babu abunda take, ummin ma sai hawaye take da kyar da sudin Goshi aka raba su ummi tayi saurin yin daki aka fita da Alaya a yadda take.

Maami ta kasa yin shiru kaman yadda tayi niyya har a sadata da gidan ta ta kalli drivern tace
"Ghali juya motar nan mu tafi gidana"

Ƙanwarta dake gefen ta tace
"Ah yaya binta gidanki kuma?"

"Aisha sa hannu kiji jikin yarinyar nan, ciwon zuciya ke gareta in muka kaita Mukhtar da haukashi ya kashe wannan yarinya me zan cewa mahaifiyarta? Bana tunanin an yiwa waennan bayin Allah adalci wannan zalunci ne wallahi"
Ta karashe tana share hawayen fuskanta tana kuma sake rungume Alaya da har lokacin kuka take sossai.

Duk wasu kananun maganganu da aka yi tayi bata kula kowa ba kuma sun santa babu wadda ya fuskance ta yace komai har ta sada Alaya da É—akin baccin ta ta kuma sallamesu akan sai ta shirya amaryar zata kaita da kanta.

Bayan watsewar kowa ta koma ɗakin inda ta barta nan ta sameta dunkule bisa tsararriyar gadon na Maami, a natse Maami ta ƙarasa ta ɗago ta
"Fatima.. Don Allah ki daena wannan kuka haka, kin san condition naki Its not good for your health kin ji?"

Maamin ta faÉ—a tana share mata hawaye wasu sabbin na zuba tace
"Maami hankalina ba zai taɓa kwanciya ba, ba zan taɓa farin ciki ba ba kuma zan taɓa daena zubar da hawaye ba matukar mahaifiyata na wanchan baƙin gidan, Maami zasu kashe min ita wallahi babu imani a zuƙatan su ko na second guda ya zanyi? Wani mataki zan bi in iya taimakonta a wannan rayuwa da na tsinci kaina? Wayyo Allah na na shiga uku!"

"Baki shiga uku ba É—iyata, umminki bazata mutu ba, abunda nake so dake shine ki fara ceton kanki da lafiyarki kan kiyi tunanin hanyar ceton umminki, babu ta yadda zaki iya yi mata komai idan har kika faÉ—a cikin wani hali, Fatima ina en uwanku? Ko na mahaifiyarki ko naki? Wani irin aiki ne wannan da babu encin kai a ciki?"

"A yadda kika gan mu haka nima na tashi na same mu cikin wannan hali, Ummi bata magana alhali tayi magana a baya, ummi bata da dangi kaman yadda ta shaida min mahaifi na ma bashi da kowa, da ciwon zuciya aka haife ni me naci da ciwon gaske na tashi cikin tsangwama, kyara da mugunta iri iri, ummi bata taɓa bani labarin wani rayuwa nata na baya ko na mahaifi na ba, abunda dae kawai na fahimta shine me gidan na mugun jin zafina da tsana ta sbd wani abu chan da ya hadasu da mahaifi na kaman yadda yake da mugun nufi akan mahaifiyata, matar gidan ta tsani mahaifiyata fiye da kowa a duniya sbd laifin da har yau ban san menene shi ba, muna rayuwa akan wani baƙin siradi a cikin gidan yanzu ya min iyaka da gidanshi alhali na san kashe ummi na zasu yi da bauta wadda basu taɓa godiya akai ba, ummi karfinta ba kaman da ba Maami abubuwan zasu mata yawa, babu ta yadda zan iya ji daga gareta bare in san halin da take ciki, Maami taɓa zuciyata kiji ji nake kaman ze fita daga kirjina sbd azabar bugu da ciwo..."

Hawaye Maami ta share tana shirin magana aka yi knocking a take ta bada izinin shigowa family doc din su ne da suka yi magana kan Shigowarta ta kuma bada umarni a chan kasa akan yana zuwa a mishi iso har ciki.

Allurai ya haÉ—a yayi mata a take ta fara lumshe idanu kan wani baccin wahala ya sake daukar ta.
"Hajiya ya kamata a kaita asibiti sbd yanayinta yana nuna tana wani stage me girma na ciwon nata kuma in tana sa damuwa a rai hakan ka iya kara shi fiye da yadda ya kamata ya tafi"

"za'a yi yadda kace doc, in ta É—an yi kwari zan nemi appointment ko a waje ne sai muje in shaa Allah"
Godiya yayi kan ya fice.

Ita kuwa ta shafa tulin gashin Alaya cikin tausayawa tace
"zan taimakeku Fatima, zan taimaka muku iya yadda zan iya in shaa Allah"
Ta faÉ—a hawaye na gangaro mata...

Miƙewa tayi ta fito daidai lokacin da muktar ke shirin tura kofan ɗakin nata, hade rai tayi tana kare mishi kallo
"lafiya?"

"Ina fa lafiya Maami Meyasa kika hana a kai min matata chan gida aka kawota nan? Akan me?"

"Toh Ubana ka shakeni sai kaji amsa, ɓace min a kofar daki tun muna shaida juna"

Ashar yake shirin wawurowa tayi hanzarin kai hannu ta kuwa samu bakin ta Buge da karfinta, ni dae baya na matsa don na ga kokarin Maami chan fa sama take kallon muktar sbd tsawo da kuma murdewarshi don yana ɗaga karfe ba na wasa ba kuma shi ɗin dan dambe ne mafadacin gaske ne amma Maami ko a gyelenta yana shirin mata rashin kunya zata kai hannu, tana kuma saurin kwaɓarshi ne sbd gudun zunubin da ya ke tarawa kanshi yaji da iya na abubuwan da yake yi mana kar ya hada da fushin Allah akan taɓa iyaye iyayen ma uwa for that matter...

Hanyar da ta nuna mishi take kuma kallonshi cikin fushi ya bi kaman zai tashi sama yana sauka yayi ɓangaren mahaifinshi da hanzari ya san shi kam ya isa da ita kuma zai kwatar mishi yanci wannan ai ba yi ba bane haka kawai yadda yaci burin wannan dare ta kama ta lalata mishi wlh ba'a isa ba, saide duk abunda ze faru ya faru har yana haki ya fara mayarwa Dad ɗin su yadda aka yi.

"Wani lokaci Binta na abunda be dace ba wallahi ta bugeka akan matar da take mallakinka? Ai yanzu ko iyayen yarinyar ka fisu daraja a gaban Allah bare ita bintan, to baze yiwu ba sam, bari naje naji me take nufi? Don a saka ta a daki a kulle aka yi auren? Ina itace ta nuna bata son auren kuma yanzu don bakin ciki tasa Æ´a a gaba ta kulle ta hana ka ita? Ina zuwa ko kuma wuce muje kawai.."
Haka ya tasa ɗan a gaba suka yi ɓangaren Maamin.
(hmmm wallahi maza mu ji tsoron Allah mu sani 'ya'yayen nan kaman amana suke a hannun mu, su É—in kiwo ne da Allah ya bamu kuma ze tambayemu akai a ranar gobe, ba ina magana bane akan duka maza saide ina magana ne akan mazan da basu taimakawa uwa wurin tarbiyartar da yaro, iyaye mazan da suke wofintar da duk wani kokarin uwa akan ganin yaro ya zama nagari, iyaye mazan da duk abunda uwa zata yiwa yaro basu ganinshi as kauna sai mugunta alhali duk duniya babu wadda ya kaita son wannan yaro, iyaye mazan da suke gurbatawa yaransu tunani suke nuna musu babu kaunarsu a rayukan iyayensu mata alhali ba hakan bane, iyaye mazan da basa taimakawa uwa wurin tarbiyartar da yara. Wallahi mu gyara mu saka idanu akan Æ´aÆ´anmu ko zamu samu rayuwarsu ta inganta... Single mothers Allah ya saka muku da alkhairi).

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment

                 🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1
*Page Eight*

"Alhj for goodness sake kar ka sa na fara yi maka musu a gaban yarinyar da yau ne ta soma shiga cikin mu, yarinyar nan bata da lafiya kuma ciwon zuciya ke gareta idan ta mutu a yau wallahi Mukhtar bashi da asara tunda ba darajar ta ya sani ba, ni ban hana a kai mishi matarshi sbd jin daaɗi ba idan ta samu sauƙi da kaina zan sadata da ɗakinta"
Maami ta faÉ—i hakan idanunta akan Alhj da ta janye shi zuwa É—aya É—akinta na saman.
Chapter 11 · 0% Book details