← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 36

Sashe 1

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AL'AJABIN SO
     (heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO... Paid*

*BOOK 1*
*Page 1*

SHIMFIÆŠA
Tarihi yana nuna mana abubuwan da suka faru ne kafin mu a rayuwa!
Rayuwar duniyar cike take da kalubale, haɗari, wahalhalu da musibu daban-daban, kusan in ka ga ka gujewa hakan to fa alƙalamin ƙaddara bata zana maka ita a shafin ƙaddararka ba, a lokacin da kaddara ke wasa da rayuwarka ya rage maka ɗaukan wannan kalubale a matsayin darasi, ka kuma yi haƙuri da jarabawar Allah (S.W.T) a gare ka.
Ni Fatima ban taɓa sanin cewa igiyar ƙaddarar wani na iya shafan na wani har su sarƙe wurin zama abu guda ba sai da na tsinci kaina cikin alkaba'in rayuwa, zafi da kunci suka yawaita a gareni, farin ciki yayi min nisa irin tazarar dake tsakanin sama da ƙasa, na kasa tantance wai ƙaddarar wanene ya shafe ni, shin na mahaifiyata ne ko na mahaifina? Ko kuma nawa ne ni a karan kaina ba'a tsaga ni cikin masu rabauta da duniya ba?
A mafi yawancin lokuta in har nayi irin wannan tunani, na kan samu kaina ne da yiwa gwanin halitta godiya da bai sa mana wani tabbataccen al'amari ba, farin ciki ko baƙin ciki yana da lokaci, komai kuma yayi farko to fa yana da karshe, wani karin maganar ma sai ya ce abinda ya baka tsoro a yau babu shakka ko tantama a gobe ya iya baka tausayi, rayuwar tamkar tafiyar hawainiya ce tana tafe tana chanza launi.

Al'amuran da suka faru a rayuwata sun sanya min karsashin bayar da labarina.

*****

Cikin matsakaicin speed motar ta shigo kayatacciyar harabar gidan, a natse take ratsa duk wasu shukoki da parking lots masu tsari da suka yi wa harabar kawanya zuwa ainihin kofar mashigar babban parlorn gidan kan ta dakata.

Da hanzari kuma cikin sauri wata farar matsakaiciyar budurwa sanye da kayan dake nuni da cewa daga makaranta take don baƙar skirt ne jikin ta wadda iyakacinsa gwiwarta sai farar shirt da baƙar blazer ta ɗaura jan necktie daga wuyanta, farar doguwar safa ce a ƙasan baƙaken sau cikin ta wadda ya shiga har karkashin skirt din na jikinta, a kanta baƙar hula ce wadda ya rufe mata gashi tsab kan ta ɗaura baret dinta a karkace daga sama hakan sai ya baiwa kyakyawar fuskarta daman haskawa da kyau, a hankali ta taka zuwa seat na baya ta sanya tsiraran hannunta ta buɗe kofar.

Wata buduruwar ce again da zasu iya yin sa'anni sanye da irin uniform din wacce ta bude kofar sak ta fito, da mugun kallo ta fara bin wacce ta buÉ—e kofar kan ta ja doguwar tsaki ta hankaÉ—eta ta wuce.
Cikin sauri ta dafe motar don gujewa kaiwa ƙasa a kuma sanyi irin tata na tsantsar natsuwa da zaka hanga daga gareta ta ɗago kyawawan idanunta da suka cika tab da kwalla sbd a makaranta ita da friends dinta yau ba karamin mutunci suka ci mata ba, haka gun shiga mota saida ta zagi iyayenta kaman yadda suka saba sanin cewa hakan ne abun da ke ci mata zuciya yake kuma ƙona ranta a take sossai, gashi yanzu m...

"Alayah...!"
Firgigit ta maida idanunta kan drivern da ya É—auko su É—in ta amsa da
"na'am baba Musa"

Ya ce
"kin mance jakar karatun taki ai yarinyar kirki"

Murmushinta me kyau ta sakar masa tare da komawa inda ta fito ta buɗe ta duƙa ta dauki jakar tata ta rataye daga kafaɗarta guda tace
"Na gode baba, bari na shiga ciki, a huta gajiya"

Da murmushi ya bi ta har ta ɓace ta wani tsiririn hanya saɓanin wadda waccan yarinyar ta shige, sarai ya ga abin da ya faru ya kuma san ba mance jakar tayi ba sauri kawai take ta buɗewa Meelah kofa kar tayi laifi se gashi bata tsira ba.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da furta
"Allah ya kyauta ya rufa mana asiri" daga haka be kara ba ya shiga motar ya kai ta ma'ajiyarta kan ya wuce bakin gate wurin hirarsu.

Alayah kuwa saida tayi É—an tafiya mai É—an nisa kan ta isa É—an wani karamin sashe a natse ta hau varender É—in ta isa kofar tare da turawa bakin ta É—auke da sallama duk da ta san babu me amsa mata, ta san anfanin hakan ne sbd an sha karantar da su cewa sallama a wuri kaman dole ce musamman in zaka shiga gida ko da babu wadda zai amsa a zahiri mala'iku zasu amsa kuma zaka samu ladar hakan.

Idanunta take warawa tana neman hasken rayuwarta, majinginar ta kuma sanyin idaniyarta, ganin bata parlorn yasa tayi hanzarin nufar kofa kwalli ɗaya da sashen dake yanayi da kango wadda bazaka taɓa kawowa akwai irin wannan sashe a cikin tamfatsetsen gidan daga waje ba ke dashi.

Tana sa kai idanunta suka sauka kan abinda take nema kayatacciyar murmushi suka sakarwa juna, kyakyawar farar macece wacce bazata haura 40yrs ba mai tsananin kyau da cikar kamala kai tsaye zaka iya kiran ta da mahaifiyar wannan buduruwar da aka kira da Alaya sbd fusgan kama da suke yi.

Da hannu matar tayi mata alama da
"kin dawo?"

Murmushi cike da fuskarta wadda bazaka taɓa ganin ta dashi a wani wajen ba face nan cikin kangon nasu ta amsa da kai tana alama irin ta maganar kurame
"eh ummi na dawo, ya gida?"

Ba tare da ta tsaya sake jiran maganan ummin ba ta sake yi mata alama bakin ta na furta wa a hankali tace
"Ummi bari nayi sauri na watsa ruwa na shiga cikin gida kar nayi laifi wurin mommy"

Kai kawai ummin tata ta gyaÉ—a kan ta bita da ido har ta shiga bayin nasu, saida ta fara wanke uniform din nata ta shanya sbd bata da tabbacin samun lokacin kanta in har bata yi a yanzun ba kan ta watsa ruwan cikin hanzari, ta É—aura alwala a bakin famfon da banda shi da matsuguni (squats) babu abunda aka bar musu a bayin na more rayuwa.

Dukda hanzari take amma hakan Sam baya nunawa sbd sanyin É—abi'a da natsuwa a jinin ta yake kaman gado ne tayi daga iyayenta duk su biyun, da kallo ummi ke bin ta har ta shafa mai ta nufi Ghana must go É—in su da bayan katifa da sallaya se bakko guda biyun babu komai cikin É—akin.

Sallar azahar ta tayar wadda ta ja lokaci a cikinshi sossai tana sallamewa landline dake parlorn na ɗaukan ƙara har tuntuɓe ta ci garin saurin isa parlorn ta ɗaga kar ta kara laifi, sallama tayi a ɗarare gabanta na faɗuwa don ta tabbatar a kap rayuwarta bata taɓa ɗaga kiran alheri daga mutanen gidan ba.

Ba tare da an amsa daga ɗaya ɓangaren ba aka soma magana cikin faɗa
"Ke! Wato tsabar kin cika cikakkiya wani sabon rashin kunyar da kika tsiro dashi yanzu kullum kuka dawo makaranta se na buga na nemoki kan ki zo ki kama min ayyuka? To na rantse da Allah yau ne na karshe daga wannan an gama! in kin ga dama karki zo kin san kan wacce zan sauke iskancin naki...."

Kit aka tsinke wayar, a hankali ta kai ta ajiye zuciyar ta Sam babu daaÉ—i, damuwa da gajiya na neman fin karfinta dama already sun fi karfin shekarunta ga raunin zuciyarta, a haka ta tashi ta samesu cikin wannan tsanani, a haka ta girma cikin bauta, hantara da zagi wadda bata san farkonshi ba bare karshen shi.

Sau tari se tayi yunkurin yi wa ummintata magana akan wannan rayuwa da suke ciki se taji tausayinta ya danne mata zuciya, bata san daga ina matsalar take ba. Shin ummin tata bata da kowa ne bayan waennan azzaluman mutanen? Me yasa tun tashinta ummin kawai ta sani matsayin uwa, uba da danginta? Babu wadda zai so dawwama cikin ukuba bare ma irin nasun nan, bata da me bata amsa hakan ysa take iya kokarinta wurin taya ummin tata da addu'a kaman yadda ita karan kanta bata gajiya ba a neman mafita daga  mai kowa mai komai.

Dafata da aka yi yasa ta É—ago tana kokarin maida kwallar da suka cika mata idanu..

"Kin gaji ko? Ko bakya jin daaÉ—i ne? Ki je ki kwanta bari naje Naji abinda zaki yi É—in se nayi"
Ummin tata tayi mata alama da hannu wadda tsab take fahimtarta sbd Kusan shi ne First language da ta fara koya a rayuwarta don har so yayi yayi affecing mind É—in ta sai ta ga kaman magana da fatar baki ciwo ne a sadda tana yarinya karama.

Da sauri ta girgiza kai tare da riƙe hannun ummin tace
"Ummi da ina da dama da iko da ba zan taɓa bari ki je inda suke ko su kusanceki ba, ummi na fi jin zafi da ciwo a zuciyata idan naga suna ci miki mutunci suna jifanki da munanan kalamai fiye da abinda ni zasu yi min"

Siririn hawaye ya gangaro mata ummin ta sa hannu ta share, ta ɗaga ido ta sanya cikin nata Dukda rauni da damuwa da suka bayyana mata sossai hakan be hanata sakarwa ummin tata murmushi mai ƙayatarwa ba tace
"Ummi zan je kar na kara yin wani laifi"

Sake mata alama da hannu ummin tayi
"kin tabbatar kina dai lafiya ko?"
Cikin murmushi tace
"lafiya ƙalau ummi"
Daga haka ta juya ta fice murmushin kan fuskanta na disashewa.

Da kallo ummin ta bi ta har ta ɓace mata, da sallama ta tura kofar tamfatsetsen tsararraren parlorn da ya haɗu ya kuma gaji da haɗuwa, a share yake a kuma tsabtace kal kal kaman ka lashe tsabar kyau da walwalin da abubuwan ciki ke yi wadda duk aikin umminta ne tsabtar duk wani muhalli na gidan, wani corridor da shima ba'a bar shi a baya ba wurin kyale kyale da kwayayen fitilu masu kyau aka ƙawatar da cikinshi, akwai kofa guda ɗaya kitchen ne a hade da katon store kofar wurin dining shi suka fi bi nan ɗin na shigar masu gidan ne.
Chapter 1 · 0% Book details