← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 36

Sashe 3

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*karki manta book 2 paid ne a naira 500 kachal ze zo muku immediately after an gama book 1, zaki iya biya tun yanzu ta wannan asusun
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin, se ki turo shedar biyan ki ta wannan layi
*09039206763*

#comment
#Vote

              🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page 2*

Tana Sallar tana zubar da hawaye tana kuma adu'ar Allah ya sassauta musu ya gafartawa mahaifinta da take jin kila da yana nan da ba haka rayuwarsu zata kasance musu ba cikin rashin gata da galihu, wulakanci da tozarci ya zame musu ruwan sha don da yana tsiro da babu masaka tsinke jikin su, cikin matsanancin kaskanci da rashin Ƴanci, ta san ko menene zai tsaya yayi tsayin daka don samar musu walwala da rayuwa mai inganci a matsayinshi na mahaifi kuma miji ga ummin ta, mutuwa mai tonon asiri.

Umminta gani take har yanzu ita ɗin yarinya ce ko gani take da already dama zuciyarta da aka haife ta da rauni na ciwo ba zata iya ɗauka ba shiyasa har yanzu bata iya bata labarinsu daga ita har mahaifinta ba, da yadda aka yi suke zaune cikin wannan baƙar gida, abubuwan da zata ce ta sani akan mahaifinta kalilan ne wadda take tsinta a wurin su baba Musa su ɗin ma se subutar baki ko in tayi wani abu da yayi yanayi da nashi, addu'a sossai tayi kaman kowani bayan sallah tana share hawaye da bayan hannunta se tayi looking very cute and adorable kaman baby.

Ummi ta santa sarai da shegen shagwaɓa wadda rayuwar da suka tsinci kansu a ciki ya koya mata juriya, ta kure ta da ido tana banbance kukan ta ne na sakalta ko kuwa daga zuciyarta yake fita? Se ta fahimci wannan ɗin hawaye ne masu ciwo da dumbin damuwa, ajiyar zuciya ta sauke har Alayah ta miƙe ta mata alama da ta koma cikin gida ta kama aikin dare.

Har ta fice ummin bata ce komai ba, Allah ya gani ba labarinsu bane bata son bata, sam bata so yarinyar ta sawa kanta kiyayya ko fansa ko wani abu makamancin haka a raunataccen zuciyarta da babu cikakken lafiya bare hutu, she cannot risk the life of her only daughter wacce itace hapiness É—in ta a yanzu.

Ita ko Alayah bayan ta koma kitchen din aikinta ta fara cikin son ture damuwowinta sbd umminta, cikin kwarewa da gogewa a girki da ta samu daga umminta ta haÉ—a Miyar kan San banda kamshi babu abunda yake tashi, a gefe É—aya ta É—aura tuwon shinkafarta, kan Ace an kira magarib ta gama ta kuma kimtsa kitchen É—in tsab kaman ba'a yi komai ba, anan kitchen din tayi Sallar magarib, seda ta jira Masu gidan suka fito tukuna hajj Zeenat ta dibar musu abincin su, godiya tayi ba tare da ta samu amsa ba ta É—auka ta fice.

KaÉ—an ta ci ta samu tayi isha da kyar sbd tsananin gajiya da baccin dake É—awainiya da ita Dukda tarin assigments da take dasu gajiya be barta ta bi ta kan bokon ba, tunda ta kwanta a sallayar ko motsi bata yi ba haka bacci ya É—auke ta.

Ummi ta tsira mata idanu tana tuna chan shekara kusan 17 baya.....

****

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!! Hawwa na gode.. Na gode" Abin da yake ta maimaitawa kenan tun a sadda kalmar likitar na tana dauke da ciki sati biyar suka shiga kunnuwanshi, ba zata ce ta taɓa ganin tsananin farin ciki a fuskanshi ba irin na ranan, ɗagowa yayi daga sujudushukr da yayi fuskarshi kamar gonar auduga yayiwa wannan likitar kyauta ta bajinta da ban mamaki.
  Ko a wurin shiga mota shi ya buɗe mata kofar cikin kulawa ta shiga ya gyara mata laffayar da ta ɗaura kan wani tsadadden zani ya zauna mata sossai kan ya rufe ya zagaye ya shige ya tayar suka bar asibitin.
   Hannunta ya kama ya riƙe cikin nashi cikin murmushi ya ce
"hawwa Æ´a mace mai tsananin kama da ke zaki haifarmin in shaa Allah in raine ta kamar sarauniya don ita É—in zata zama princess kuma uwata"
baki ta taɓe cikin murmushin ganin irin kwantaccen fara'a dake fuskanshi tace
   "ni kuwa namiji nake so mai tsananin kama da kai ya zama jarumi, jajirtacce irin ka, mai kulawa da duk wani hakki na ubangiji, wadda ko kallonshi nayi zan tuna da sadaukin maza na."
Cikin murmushi ya lakace mata hanci ya ce
"We shall see! Allah ya bamu me albarka amma ina me tabbatar miki mamana na ajiye a nan" ya karashe yama me shafa ƙasan mararta da hannushi ɗaya, ɗayar na sarrafa stirring mota dariya suka yi a tare tana amsa adu'ar tashi....

*****

Tashin da Alayah tayi a firgice shi ya katse mata tunanin da ta tafi har tsorata tayi, sai ta ga tayi wurin landline da gudu tayi picking sbd saura kiris ya tsinke, da alamu kira ake ita ummin bata ji ba sbd babu kunnen, mintuna biyu taga Alayar ta dawo tare da É—aukan hijab É—in ta ta saka fuskanta sam ba walwala, da hannu ummi tayi mata alama..
  "Menene? Ina zaki je a daren nan?"
Seda ta sauke ajiyar zuciya tace cikin alamar kurame
"Ummi Jameelah ke nema na wai dare yayi bazata iya cin tuwo ba in je in dafa mata indomie in soya mata plantain in kuma dibi Miyar as pepper soup in kai mata É—akin ta"
Shiru ummin tayi kan ta É—ago ta ce
"Ki kwanta bari na je na yi mata"
Da sauri ta girgiza kai tana mata alama
"a'a ummi babu ta yadda za'ayi ina kwance kina chan kina yiwa Jameelah girki bari naje yanzu zan dawo"
Kanta ƙasa har Alayar ta fice..
Lallai dukkaninsu Allah ya amsa adu'o'insu, ya bata mace me tsananin kama da ita kaman yadda mahaifinta ya roka, se kuma ya amsa nata wurin bata halayya mafi rinjayi na mahaifinta me haƙuri, juriya da kuma jin ƙanta, sanin kanta ne Alaya ta ci sunan inkiyarta na princess, smart and beautiful, kwata kwata bata son ganin ummintata na wahala Dukda a ciki ta tashi ta sameta, bata ƙaunar jin wani kalmar ɓatanci in har dae akan umminta ne, hakan ya sa wahalhalu dayawa takan ɗauke mata na ayyukan gidan da kankantar shekarunta, ɗaga hannu sama tayi tana rokon Allah ubangiji ya kawo musu karshen wannan rayuwa da suke ciki don suna tsananin jiggatuwa...
   
Cikin mintuna da basu fi arba'in ba ta gama tare da kai mata har daki, ba zata iya jira ba tunda ta san ko yau ko gobe din ne itace dae zata fitar da kwanukan don haka ta wuce sashensu, da kyar ta iya sauya kayanta ta koma bayan umminta ta kwanta a take bacci yayi awon gaba da ita se lokacin ummin ta juyo ta tofeta da addu'a kan itama ta shafa ta lumshe idanu tana sake sake har bacci ya É—auke ta.

Washegari da safe kaman yadda al'adarsu take a gidan suna Sallar asuba suka miƙe suka fice, ummi na tsaftace gidan yayinda Alayah ke ta zirga zirga a kitchen wurin haɗa breakfast, tayi nisa a aikinta tana cikin soya doya taji ƙarar fashewar abu a lokaci ɗaya ta tsinci gigitacciyar tsawar Hajj Zeenat wadda ta tabbatar umminta ce kawai take yiwa irin wannan tsawa, wani mummunan faɗuwa gabanta yayi wadda ya haddasa bugun zuciyarta tafiya fat fat fat kuma hakan barazana ce ga lafiyarta, da sauri ta saki cokalin hannunta tayi parlorn Dukda ta san laifi take shirin aikatawa amma bazata bar umminta ta muzanta gabansu ba, da gudu ta shiga gaban ummi marin da hajj Zeenat ke shirin sauke mata ya sauƙa kan fuskar Alayah ji kake tassss, tsabar zafin marin da karfin shi seda ta fadi jikin ummin ta baya baya, ko gama dawowa hayyacinta bata yi ba tayi saurin zubewa bisa gwiwowinta tana cewa..

"Mommy don Allah ki yi haƙuri, mun tuba ki yafe mana"
Cikin faÉ—a me hade da ihu hajj Zeenat tace
"ke har kin isa? Ke kika min laifi ko uwarki? Wallahi yau ko zata buÉ—i baki da kanta tace min yi hakuri ba zan hakura ba"
Ummi da har lokacin ranta tafasa yake da marin da hajj Zeenat ta saukewa Alayah idanunta kan flower vase din da ta fasa wadda tunani ta tafi na sadda aka saye shi da yadda aka saya mistakenly ta ture shi ya faɗi ya tarwatse, idanunta gabaɗaya suka sauya duƙawa tayi ta ɗaga Alayah tare da juyawa da ita zasu fice, wani irin fusgowa da hajja Zeenat tayi mata seda suka juyo gabaɗaya ta ɗaga hannu da niyar tsinke fuskar ummin da mari taji karaf an riƙe hannunta.

Da kallo ummi take bin su dukkansu biyu, shimfide cikin idanunta kana iya hangar zafi da turirin zuciya da take fama dashi a lokacin, soyayya da kulawa irin ta uwa ya wuce a ce a zabgawa É—an ka mari me wannan zafi a gabanka ka kasa tabuka komai, wani irin zafinsu take ji barin ma shi, duban su ta sake yi a karo na ba adadi kan ta janye Alaya suka fice daga parlorn.

"Me kenan kake kokarin yi Abban Jameelah? Ƙaskantar da ni a gaban waennan ƙaskantun mutanen? Ka kuwa san laifin da ta aikata min?"
Hajj Zeenat ta faÉ—a a kufule
"ban sani ba kuma bani da ra'ayin sani, abunda kawai na sani shine sau ɗaya tak kika yarda kika sauke hannunki kan hawwa ranki idan yayi dubu to se ya ɓaci, duk abunda kike kallonki kawai nake ba wai bani da ikon hanawa ko dakatarwa bane, ni na san anfanin da hakan ke min don haka ki kiyaye, don yarinyarta ban damu ki mata ko ma menene ba amma banda hawwa"
Yana kai nan ya juya ya buÉ—e wani kofa da ze sada shi da sashen shi ya shige.
Chapter 3 · 0% Book details