← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 36

Sashe 27

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Masallacin asibitin suka je suka gabatar da azahar, Adu'a sossai Maami tayi kan suka fito zuwa ɗakin abinci da aka yi ta kawowa ta saka Alaya a gaba ta ci ita kuma ta sha baƙin shayi, call ne ya shigo ma Aunty ruqayya ta duba kan tace
"Allah sarki umar ne, kila labarin ya je mishi hankalin shi kuma zai dawo kan Adda ruqayya gashi jiya jiyan nan da safe ya koma"
Maami ce ta mika hannu ta karɓa dama ita ma tunanin shi take a ranta, ɗagawa tayi tare da Miƙewa ta matsa daga inda suke sun jima sossai suna magana kuma shi ma ya sake bata kwarin gwiwa, so ma yayi ya zo Dukda ba don Yayan shi ko Abbansu zai dawo ba don Maami ne kawai to amma ba zasu bar shi a wurin aiki ba, abubuwa dayawa na hannunshi.

Har zai kashe tace
"Amma auta ka ji daga shi Mukhtar É—in?"
Daga chan ya É—an yi shiru na seconds kan cikin natsuwa ya ce
"Maami na ji, sai dae har yanzu ba wani abu be ce musu komai ba, kuma ba horon da basu mishi ba"
Ajiyar zuciya ta sauƙe tace
"Toh na gode sai anjima"
A hankali ya sauƙe wayan ya bi da kallo, uwa fa kenan!
Sai kusan la'asar Abba ya farka, ko magana ya kasa, abinci ma da kyar ya sha shayi, kab rayuwarshi be taɓa jin haushin Mukhtar irin na wannan karo ba, wani irin karta ranshi ke yi, Mukhtar da ya yarda dashi shine ya cuce shi, ya tarwatsa mishi siyasa, haushin da yake ji na kowa yasa mutane suka ɗan ragu, guards sun cike wurin sbd Ƴan jarida da suka taru kaman an kira su, ganin haka yasa Maami ta ce ɗan uwanshi ƙanin Alhjn a cikin mahaifinsu zaid ya zauna dashi ita zata koma sbd Alayah, har zata fita ta tsaya ta dawo da baya kadan tace tana kallon Abban da karyayyen kallo zafin kirjinta na fita har a kan harcenta.

"Babu wata uwa da zata yi farin ciki da lalacewan ɗan ta, amma ko babu komai yau na ji daaɗi da muka raba ɗacin lalacewar Mukhtar wadda kai ne sanadi, ko babu komai Allah ya nuna maka ba sai ka zalunci wasu ne zaka yi nasara ko ka fadi ba, Allah baya zalunci kuma ba ya barin me yi, ko ka nufi gyara kuskuren da ka tabka daga yanzu ko kuma ka cigaba da girban abin da kai ka shuka dama na sha faɗa maka akwai ranan ƙin dillanci"
Tana kai nan ta juya ta fice tana goge kwallar ta, idanunta ke haska mata kaman yau ne tana shirin tarbiyatar da yaronta Alhj na rusawa daki-daki, shi karan kanshi be ga laifinta ba sai ma kunya da nauyi da suka rufe shi, idanunshi gabaɗaya sun rufe ya cutar da rayuwar Mukhtar sossai wadda sai a yanzu yake jin be kyauta ba, kunyar mutanen duniya ya rufe shi, tsoro da shakkar kamuwar tsinuwar bakinsu ya lulluɓe shi, shine da kaso mafi tsoka ya sani amma shi a ganinshi duk soyayya ce ashe ba haka ba ne, hawaye ne ya gangaro mishi.

"Yaya ka yi haƙuri kayi kokarin cire damuwa a ranka in shaa Allah komai zai wuce"
Zaid ya faÉ—a, murmushi kawai yayi me ciwo be sake cewa komai ba.

****

"ba mutum É—aya ba ne...!"
Ta faÉ—a da kyar a sadda ta farka cikin kuka, Æ´ar sandar ta gyara tace
"Ki kwantar da hankalinki kin ji? Ki natsu babu wadda zai sake cutar dake yanzu kina hannun hukuma ne kuma ba sa zalunci bare cuta, ki gayamin duk abin da ya faru kin ji?"
A hankali ta ba yar sandar labari ita dai ta san mutum uku ne, kuma sam bata lura da ko sun kai nawa tsaye a wurin ba hankalinta na kan kudin da ta batarwa yaddikonta sai a lokacin mahaifinta yake jin wasu abubuwan ma da be san suna faruwa da ita a gidan ba, kai tsaye wannan Police ta nufi office nasu.

C.P ta kaiwa report din yana dubawa yace a je a sake tuhumar muktar har sai ya faɗi sauran, duk yayi ignoring calls da yake samu daga sama saboda wannan case ɗin ba mai kasuwa ba ne, ko ba familynshi aka taɓa ba sai inda karfinshi ya kare bare na gida ne, cikin kokarin cika umarni wasu daban suka sake nufan ɗakin na Mukhtar don tambayar shi da kyau..

*littafin nan paid ne book 1 ne kaÉ—ai free
Pay ur 500 through dis account
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
Sai shaidar biya ta
09039206763*

🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)

Adabi Writers Association

Book 1
*Page Nineteen*

*Assalamu Alaikum warahmatullah, Fatan duk muna lafiya? Ina ganin ya kamata mu dinga yiwa juna adalci, ina nufin tsakanin makaranta da marubuta, lallai a tafiyar da muke zuwa yanzu na fahimci cewa makaranta ku ke da kaso mafi girma na sanya marubuta aran halin da ba nasu ba su yafa, kuma kun fi kowa yayata cewa marubuta na da girman kai, this and that, ina magana ne based on experience ba da ka ba so duk wadda be ji daaɗi ba yayi haƙuri kuma a gyara, Marubuci zai ɓata lokaci kwarai wurin bincike da rubutu, ya kashe duk wasu abubuwa masu muhimmanci nashi ya zauna don faranta muku dayawa kuna bibiya kuma ana ƙaruwa amma kalmar an gode ma ya zama matsala bare comment, ana tafiya dai a haka saboda burin kowani marubuci ya isar da saƙon da zai anfani al'umma, muna cikin wannan tafiyar na ce yarona ba lafiya zan kai shi asibiti billahi wasu ba su iya cewa Allah ya yaye ba, amma suna gaba gaba a wurin bi na Pc ana cewa ana ta jira shiru, a'a ana kashe musu kwarin gwiwar karatu, an shanya su this and that! Sister ashe babu daaɗi? Yanzu idan na buɗe na ga wannan saƙo saboda bin cewar Manzon Allah na ka faɗi alkhairi ko kayi shiru na ƙi magana sai fa a ce girman kai ne ko wulakanci ko? Toh Allah ya kyauta. Na kawo wannan ne ba don rashin ɗa'a ba don nan ɗin gidan tarbiya ne ba haufi sai don mu tattaru mu gyara, mu zama masu adalci a tsakanin juna, adalcin ne yasa duk ba zan yi Page ba sai na zo na faɗi dalili, don Allah mu karfafawa juna gwiwa wurin zamantakewa da kuma cigaban juna don kowa na da ƙaruwarshi a duk wani tafiya na duniya. Bissalam*

••••

"Astagfirullah"
Ya furta bayan ya shafa dogon adu'ar da ya jima yana yi tun bayan sallame Sallar asuba da ya gabatar, ya godewa Allah maɗaukakin sarki da ya kasance adalin adilai, maji ƙan bayi wadda bai taɓa tantance da yaren da za'a roƙe shi ya amsa ba, don da be san ta yadda zai fara ba, Sallar ma yayi shi ne babu tabbacin isar shi saide ya roƙa akan Allah ya shirya shi ya ɗora shi hanya madaidaiciya, ya kuma bashi ikon gyara kura-kuranshi tun kafin ya koma gareshi a zero, Shigowar wani kurtun Police ne ya sa shi sa hannu ya kare haske tarrrrr da ya bayyana mishi yana kokarin illata jijiyar ganinshi don ɗakin duhu ne yake zaune ciki.

"Ana buƙatar ganin ka"
Ya faÉ—a ya ja baya ya tsaya rike da kulkin shi, a hankali Mukhtar ya fito kafafunshi sun yi kumburar da baya iya taka su da kyau, dafe da gini ya dinga tafiya har suka isa office É—in na C.p, kaman yadda be kalli duk jama'ar da suke kallonshi ba daga jami'ai har civilians haka be tanka maganganun da suke jifan shi dashi ba, ko da suka shigo be É—aga idanunshi ba ya ja ya tsaya, a tunanin shi mahaifinshi ne zai sa a kawo shi ya ganshi alhali shi duk duniya a halin yanzu babu wadda ya tsani gani kaman mutumin da ya kawo shi duniya.

"Mukhtar"
Baba ya faɗa bayan ya gama kallonshi, babu abinda ya firgita shi irin tatoos na jikinshi kasancewar bashi da riga duk wani tatoo da ya kashewa makudan kuɗaɗe wurin zanawa gasu nan raɗau akan farin fatar shi, gashin kanshi da nashi ne yaje aka murde tsakiya ya zama dada aka kuma penta shi kalar ƙasa daga sama duk gasu nan zube har wuraren goshinshi, ɗaga idanu yayi ya kalli Baba ba tare da ya motsa ba, hannu baba ya miƙa mishi sai ya soma takawa kaman me tsoron tafiya ya isa gabanshi ya durkushe bisa gwiwowinshi a karo na biyu bayan fahimtar waye shi a duniya ya fashe da kuka me cin rai, kukan tsantsar takaicin rayuwarshi da nadamar abubuwan da ya aikata gabaɗaya rayuwarshi, kukan baƙin cikin kasancewarshi mashayi, mazinaci, azzalumi tunda yana iya zaluntar kowa ya kwana lafiya hakan kuma ya zamar mishi abin tinkaho a baya, hatta matar aurenshi ya zalunceta to me zai zauna duniyar yayi?

Ya fi mintuna ashirin yana wannan kukan wadda duk jama'ar da suke wurin suka shiga tsantsar mamaki babu wadda zai yarda sbd wannan fyade ne yake kuka kaman yadda Baba ya katse mishi kukan da cewa
"Mukhtar na tabbatar ba kukan halin da kake ciki ba ne kake yi, a duk abin da zai faru kana da yaƙinin mahaifinka zai fidda ka, shi ma kuma bashi da wani tunani in dae akan ka ne ko nawa zai iya kashewa tunda kudi ba matsalar shi bane, Mukhtar kalli jikinka kaman ba na mutane ba? Ka kuwa san haramci tatoo?
Kalli gashin kanka irin askin da annabi ya hane mu dashi ka kwashe rabi da rabi ka bar tsakiya, Mukhtar baka tsoron hukuncin Allah a kanka? Baka tsoron fushin shi ya haɗu da na mahaifiyarka ya haifar maka da babban iftila'i? Ko ka san kuɗi ba zasu taɓa ceton ka daga fushin ubangiji ba?"
Chapter 27 · 0% Book details