Sashe 2
Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga chan karshe ta buɗe wani kofa da ya sada ta da wani babban parlor wadda na matar gidan ne mommy kenan, kaman wanchan shima a share kuma a tsabtace yaji kujerun alfarma ga sanyi da raɓar Ac.
A cikin lumtsuma-lumtsuman kujerun ta samu mommy zaune ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana sanye da wani ɗan ubansun lace na manyan mata taji adon gwala-gwalai hannaye da wuya, hannunta rike da waya kirar Samsung wadda ake cewa Fold tana latsawa, a kan gwiwowinta Alaya ta zube tace...
"Mommy sannu da gida"
Kaman ba da ita take ba, kaman ma bata san da zaman mutum a wurin ba saida ta bushi iska don kanta bayan kafafun Alayah sun fara tsami a tsugune kan ta ce
"wato ke don uwaki tsabar kwakwalwar kanki a toshe yake kaman yadda kunnuwar uwarki kurma suke a doÉ—e Sau nawa zan faÉ—a miki in sake nanata miki karki sake ki haura mintuna talatin daga dawowarku daga makaranta zuwa ganin ki a parlorn nan?"
Kanta a ƙasa idanunta cike da kwallah saide bata bari sun zuba ba tace
"kiyi hakuri mommy sallah na tsaya yi"
"ke a gidan uban wa na zama mommyn naki? Ban ce ki dinga kirana Hajiya ba? Ko kin ga nayi kala da uwarki? Sunnu limamiyar Makka! Tukuna ma me ya hanaki wankewa jameelah bayi yau da har ta kasa shiga bayan ta dawo daga makaranta sai na É—akina taje ta shiga tayi wanka?"
Bata ɗago ba a duniya babu fuskar da bata ƙaunar gani irin ta Hajiya Zeenat sai taga kaman idan ta kalleta zafin da zata ji daga zagi da cin mutuncin sai ya fi wadda take ji idan bata kallon ta.
"Kiyi haƙuri Hajiya makara muka yi"
Maimaicin abun da ta riga ta sani ne tunda tana hakimce Meelah na kwance kan cinyarta da safen ta kawo mata noodles and egg da shi ɗin tace ta dafa mata, bayan ta kawo kuma ta chanza zuciyarta chips da cripsy drumsticks guda biyar take so babu yadda ta iya ta koma ta sake farawa hakan ya makarar da ita sossai, kuma ta san idan ta kuskura ta saka Meelahn letti har aka taɓa ta a school Se Umminta ta mata gashin ruwan zafi sbd mahaifinta baya tolerating duk abunda ya shafi Jameelar.
"Ki wuce kije ki wanke mata bayi, ki chanza mata beddings don ta ce ƙaiƙayi suke mata ki tattara laundry ɗin ta ki je ki wanke sannan ki zo ki ɗaura dinner don kurma ta riga ta ceceki tayi na rana ita me ƴa"
Cikin ladabi ta amsa da
"Toh Hajiya"
Mikewa tayi ta nufi kofan hagu daga cikin parlorn shima yana da karamin parlor da dakuna biyu na hagu ta sake isa ta yi sallama, ba amsa, ta sake yi Dukda ta san Meelahn na jin ta amsawa ne bata yi niyyar yi ba, in kuma ta ƙusa kai ba izini ma wani maganan ne.
A na huÉ—un ne ta riski wani tsawa...
"Ke Dallah Muguwa kawai! Kin dameni da wani shegen murya kaman Drum so kike se kin kurmantar min da kunne kin maida ni kamar kurmar tsohuwarki ne ko kuma me? Mtseeew"
Ba tare da tace komai ba ta buɗe kofar ta shiga, ko kurmar ne da take faɗa ta tabbatar ta shafa muryarta ta shafa na Jameelah ta san ta fita zaƙi da taushin murya nesa ba kusa ba.
Tana zaune cikin É—aya daga cikin kujeru guda biyu dake É—akin hannunta rike da waya tana latsawa haka kunnuwanta sake da babban baby pink headphone saide bata tunanin tana using ganin baya haske, ba tare da tayi kwakwaran kwaraniya ba ta wuce toilet É—in ta wanke shi tsab bayan ta gama ta dawo É—akin bata sameta ba hakan ya sa ta fara cire zannuwan gadon ta chanza wani tare da gyare É—akin tayi mopping da goge goge, hannunta dauke da kayan cikin laundry basket É—in Meelahn ta fice zuwa chan baya inda suke wanki.
Bayan ta zube su ta koma kitchen bayan store akwai wani karamin laundry room dauke da abubuwan shanya, washing mashings da sabulai da omo kala kala wasu a goruna wasu a ledoji, zaɓar waenda ake yi wa Jameelar wanki dasu tayi ta koma ta hau wanki, ta jima sossai tana yi sbd kayan da ɗan yawa saukinta ma babu wani datti sbd sawar mugunta ce sai a sa kaya kala uku huɗu a rana, tana gama sanyawa ta tsuguna a wurin riƙe da kanta dake sarawa, bayanta kaman ta cire ta ajiye sbd yadda yake yi mata wani irin ciwo, hawaye masu zafi ne suka zubo mata tana jan numfashi da kyar ta sa hannu ta goge, ta jima haka kan ta miƙe ta nufi kitchen wanke wanke ta fara na kwanukan rana da aka ɓata bayan ta gama ta goge ta shanya kan ta matsa ta duba time table na abinda zata yi na dare.
Miyar ganda ce ta kan Sa sai tuwon shinkafa, fiddo naman kan tayi daga freezer ta sa a pressure pot ta zuba mishi ruwa me yawa ta ɗaura kan hot plate tare da kunnawa, chan gefe inda ta ga kular abincin su ta nufa ta ɗauka dama ta riga ta san ba daga tukunya yake ba wadda suka rage ne suka juye musu a kular da ya kasance nasu, sashensu ta koma ta samu umminta ta idar da Sallar la'asar kenan, zama tayi gefen ta cikin tsantsar gajiya ganin zaman baze yiwu ba ta zame ta kwanta a wurin tare da lumshe idanunta da suka fi yanayi da na Larabawa farare sol mai ɗauke da baƙi sidik ɗin kwayar ciki, zara zaran gashin har ya sauka fuskanta don tsawo da kyaun su.
zuciyarta a chunkushe ta gaji iya gajiya da irin rayuwar da ta tashi ta same su da mahaifiyarta a kai, wasu kan ce abunda ka saba yau da kullum ya kan shiga jiki ya zame maka jini saide kai bata tunanin ana iya yin sabo da wahala, a hankali ta buÉ—e idanunta jin saukar hannun ummin ta bisa goshinta ta zubawa ummin idanu, banda rama da tsantsar damuwa babu abunda take karanta daga ummin tata.
Murmushinta me kyau ta sakarwa ummi ko kusa ita karan kanta bata Fatan tashin ciwon ta don ta san ummin zata bari da wahala da kuma damuwa, cikin yatsina fuska ta miƙe zaune ta fara yi wa ummin tata magana
"Ummi lafiya ta fa ƙalau na ga kina ta damuwa"
Ummin tana mata kallon tuhuma itama tace
"Ai na daena yarda da maganarki in har dae akan ciwon ki ne, sau nawa zaki ce hakan bayan kina nan kina shan wahala?"
Murmushi ta saki sossai har saida fararen hakwaranta dake jere reras zuwa dimples É—in ta guda biyu suka bayyana.
"Ai ba wai ƙarya ba ce ummi bana so hankalinki ya dinga tashi ne" tana kai nan ta janyo kular abincin tana yi wa ummi alama da
"wallahi Sallar nan ba zan iya yinshi ba matukar banji sauƙar abu cikin ƴar hanji na ba, yunwa nake ji kaman in ci babu".
Murmushi kawai me cike da ma'anoni daban daban ummin da suke tsananin kama da Alayar sai en abu kalilan da bata ɗauko nata ba ta saki kan tayi mata alamar a ci dae da bismillah, inaaa ita kam tayi nisa a cin abincin ta, tunda take a duniya bata taɓa jin abincin da ya kai na umminta daaɗi ba, lokuta dayawa ta kan tambaye ta wai wani makarantar koyon girkin tayi? Lura da ta yi tambayar kan taɓo mata wani fanni chan na rayuwarta yasa ta daena.
Sai da ta fara kai wa geji kan ta lura da ummin tata bata ma soma ci ba, da sauri ta dakata tare da É—ago idanunta farare sol ta dubi ummin da tayi nisa da kallon ta fuskanta dauke da murmushi sannan hawaye na zuba mata daga saman fuskanta.
"Ummi.." Ta faɗa tana sa hannu ta taɓa kafafunta.
Da sauri ta ɗauke kai tana share hawayen wadda nan take Alaya taji abincin ya fice mata daga rai, ba karamin So da shakuwa ne ke tsakanin su ba ko don basu da kowa ne sai junansu oho, amma abunda ta sani yanayin ɗaya baya chanzawa ba tare da ya taɓa na ɗayar ba.
"Ummi menene?" Ta tambaya cikin tsantsar damuwa Dukda ba yau ne na farko da ta kan tsinci ummin tata cikin irin wannan hali ba.
"Babu komai Alayah, kawai kin tuna min da mahaifinki ne da abubuwa guda biyu yanzu".
Itama Alayar yanayinta ne ya sake sauyawa jikinta a sanyaye tayi wa ummin alamar
"wani abu nawa na yanayi da nashi ko ummi?"
Cikin murmushi me bayyana tsantsar ciwo ummi tace
"Cin abincin ku iri ɗaya sak! Haka kuma bai taɓa zama cin abinci ba tare da ya tambayi inda na koya girki ba, wani lokacin ya kan sanyawa iyayena Albarka, na kan zauna cikin murmushi da jin daaɗi ina kallon yadda zai ke ta santin abinci na har ya gama ci, kai har ta kai ta kawo mahaifinki baya iya cin komai koma menene a waje, duk wata ƙasa da ze je se ya ɗauke ni mun tafi tare sbd girki kawai...."
Katsewa maganar yayi ta sa bayan hannu ta É—auke hawayen ta Allah sarki mutuwa, mutuwa baya barin wani don wani yaji daaÉ—i.
A sanyaye Alaya tace
"Allah ubangiji ya gafarta maka Abbana"
Daga nan se walwalarsu ta kau, a koyaushe dama walwalar tasu bata wuce na dakiku, a duk sadda zasu tuna da jigon rayuwarsu kowa da abunda ze ke kitsawa a ran shi.
"Ummi a duk sadda kika yi wani zance na Abba alamu su kan nuna Yana da dukiya, sannan yana da kirki ga mutane da kyakyawar alaƙa, yana da son mutane kaman yadda su ma suke son shi? Ummi ina dukiyar? Ina mutanen nashi? Ummi Don Allah mai ya ajiye mu anan cikin azaba da kuncin rayuwa??" Tayi maganar cikin zubar hawaye, da sauri ummin ta hadiye ƴar walwalarta cikin sanyi da siga na bada umarni tace
"in kin koshi wuce kiyi sallah ki komawa aikin ki..."
Kuka sossai Alayah ta saki kan ta tashi ta nufi bayi.......