Sashe 29
Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Shin kun amsa laifukanku?"
Kusan shine tambaya na karshe da alkalin yayi bayan gabatar da duk hujjoji daga bangarorin lawyoyin masu kare wadda ake kara da masu kara, duk wasu shaidu sun fito karara, Nawwaz ne ya dubi mukhtar da har lokacin be É—ago kanshi ba, har yanzu basu faÉ—a cewa babu Mukhtar cikinsu ba, shima kuma tun da ya fada a gaban su Maami be sake furtawa ba, ko da suka zauna wuri É—aya banda istigfari babu abin da yake yi, be musu magana ba duk kuwa irin surutan da suka dinga yi mishi, sun mishi adalci kenan idan suka sake dulmiya shi cikin damuwa bayan damuwar da suka san yana cikinta?
"A ƙarshe bayan duk wasu hujjoji da shaidu da suka gabata, kotu ta yankewa waennan matasa huɗu shekaru goma goma gidan yari tare da azaba me tsanani, da kuma tarar naira miliyan ɗaiɗai daga kowannensu zuwa ga iyayen yarinya don a cigaba da kula da lafiyarta"
Hannu ya sa ya ɗauki kulkinshi ya buga aka miƙe gabaɗaya, alkali ya juya don komawa office nashi hankali kwance. Yayinda polisawa suka yi kansu tare da ma'aikatan kotu don tabbatar da isansu prison lafiya.
Littafin nan ba kyauta bane, book 2 na kuɗi ne a yanzu mun fara jin ƙamshin karshen book 1 ku hanzarta biya saboda yanzu muka soma tafiyan, zaku iya biya ta wannan asusun
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai shaida ta wannan layi
09039206763
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)
Adabi Writers Association
Book 1
*Page Twenty*
"Ya mai girma me shari'a!!"
Chak kowa ya tsaya a cikin kotun saboda yadda tayi magana da amo, fuskanta gabaɗaya ya cika da zallar gigita da kuma ruɗani wadda ta kasa ɗaura shi a mizanin hankali bare ta iya daidaita tunaninta, bata jira cewar shi ba tunda ya riga ya tsaya ta soma sauƙowa cikin sassarfa har ta isa gaban Mukhtar da ya zura mata idanu baya ko kyaftawa, zuciyarsa na wani irin fusga da wutar ƙaunarta da bashi da masaniyar sadda ta ruru har ta zame mishi wutan daji, ta cinye ilahirin zuciyarshi da duk wani sassa da jini ke gudana.
Gabanshi ta isa ta kalle shi cikin idanu ta ɗago ta kalli alƙalin cikin Muryar roƙo da karaya ta ce
"Don girman zatin Allah me shari'a ka taimaki macen da take dauke da juna biyu na wadda aka yankewa shekaru goma gidan firsuna, ka taimaki uwar da take shirin shiga tsananin tashin hankali saboda yanke wannan hukunci bisa kuskure, ka bamu dama ta biyu ina me tabbatar maka babu hannun mijina ciki..."
Be tanka ba don yanayinta ya fi kama da mahaukaciya wacce take cikin sabuwar kamu, bata damu ba tunda dae yana tsaye ta juya ga Mukhtar da banda kallo babu abinda yake binta da shi ta sanya hannu ta riƙe nashi, cikin karyayyen murya me cike da tausayi a gauraye da son da bata san tana mishi ba saida taji hukuncin da aka yanke mishi ta soma cewa
"Ya Mukhy a rayuwa muna kuskure, kowa yana kuskure kawai abinda ya kama ce mu a duk sadda hakan ta kasance shine muyi imani, mu kuma rayu da wannan consequences É—in da kuskuren mu ya janyo mana, tunaninmu ya karkata ga tunanin tayaya! Ta kuma wani hanya zamu bi wurin gyara wannan kuskure"
Hannunshi ta kara gimtsewa tana roƙonshi da idanunta
"you don't have to blame yourself all for that Yaa mukhy, ba sai ka shigar da kanka cikin bala'in da baka da masaniya bane za'a san ka chanza wlh we all believe you... Ko Maami?"
Ta juya tana kallon Maami da banda hawaye babu abin da take zubarwa sai ta gyaÉ—a musu kai, da sauri ta juyo tana mishi kallon ka gani ko? Sai ta sake cewa da sauri
"Duk yadda kaddara ta zo a haka zamu karɓa mu kuma cigaba da rayuwa, karka nesanta kanka da mu da tunanin mun tsaneka, halayyarka ce bama so kuma ka sauya don Allah kar ka bari in haifi yaron da zai shekara goma cikin duniya ɗaya da mahaifinshi ba tare da ya san shi ba, maraici akwai ciwo Don Allah"
Ta haÉ—a hannayenta wuri guda tana kuka.
Da sauri ya sa hannayenshi duka biyu ya riƙo hannunta ya sauƙar ya mayar da ɗaya kan fuskanta yana share mata hawayenta a hankali cikin sanyi ya furta
"Ban aikata ba Fatee, Na rantse da wadda raina yake hannunsa ban aikata ba..."
Nawwaz da hawaye ke ta zuba mishi saboda sai yanzun ne yaji basu kyauta ba, barin ma da Alayah ta juyo kansu ta haÉ—e hannayenta
"Don Allah kuji tausayin É—an dake kwance a cikina, ku tausayawa mahaifiyar da ita kaÉ—ai ta kan mance adu'a akanta wa kanta da rayuwarta saboda ta shagaltu wurin yiwa wannan É—an nata Adu'a ku tsage gaskiya, kar ku kasance masu Son zuciya please"
Nawwaz ne yace
"Be aikata ba wallahi, hasali ma be san sadda muka yi hakan ba sai bayan mun gama"
Smrt ma ya ce
"hakane wallahi, Mukhtar baya cikin mu"
Alkalin da gabaɗaya jikinshi yayi sanyi da tausayin Alaya da irin maganganunta sai ya dawo ya zauna, kowa ya koma ya zauna shari'a ta sake dawowa daga baya, kai tsaye duk su ukun suka bayyana gaskiya inda yarinyar m ta tabbatar da cewa mutum uku ne ba huɗu ba, shari'a saɓanin hankali sai gashi an wanke Mukhtar, Alayah kaman ta tiki rawa sai ta koma inda mazauninta suka rungume juna da Maami.
Har suka iso gida bayan kammala komai Alaya bata iya ta ce komai cikin motan ba saboda yadda duk ya cike wurin, lallai natsuwa wani rahama ce ta daban, É—akinshi na sashen ya wuce yayi wanka Maami ta tura a kai mishi Abinci, a chan ya ci ya kwanta bacci ba shi ya tashi ba sai azahar yayi wanka ya fito a wurin mashigar suka haÉ—u kiribb da Abba, kallon juna suka yi na seconds kan duk suka nufi ciki don karyawa.
Abin mamaki wai na kwance ya faÉ—i yau Abba ne da Mukhtar suka hadu babu wadda ya iya yiwa dan uwansa magana, Alayah da Maami already sun ci hakan ya sa Alayah isowa gaban dining É—in Sin serving É—in su.
"Abba ina yini?".
Ya faÉ—a saboda gaisuwar kaman dole ce a gareshi
"Lafiya..."
"Ka kuwa san kana buƙatar neman yafiyata? Ashe duk hanyar da ka ɗaura ni kai ina ganin gata da soyayya ce babban halaka ne? Abba baka kyauta min ba sam, kaine sanadin duk wani kuskurena a rayuwa I hate you for that"
Banda kallo da idanu babu abin da yace da Mukhtar din wadda hakan ya saka zuciyarshi hasala ya fara watsawa mahaifin nashi baƙaƙe maganganu cikin ɗaga murya, da gudu Alayah ta ajiye maheer ta tare Mukhtar tana mai rufe mishi baki a lokaci ɗaya tana girgiza kai cikin firgicin kalaman da yake jefawa mahaifin nashi...
Ayi haƙuri da wannan wlh bacci ne ya ci karfi na.
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)
Adabi Writers Association
Book 1
*Page Twenty one*
"Ya Mukhy ka dawo cikin hayyacinka Abba ne fa"
Abba da yake zaune shiru ba tare da ya ce komai ba duk maganganun Mukhtar ɗin ne suke dawo mishi, a hankali ya ɗago idanu ya kalli Maami da ta iso wurin ta tsaya ba tare da tace komai ba, ashe haka take jin nauyi da zafi a ranta a duk sadda yake ba Mukhtar goyon bayan faɗa mata abinda be dace ba ba tare da kwaɓa ba, lumshe idanunshi yayi yana ambaton Allah kan ya buɗe ya kalli Mukhtar da ke ta huci har lokacin Alaya bata sauƙe hannunta daga kan lips ɗin shi ba yace
"Fatima kyale shi, barshi ya faɗi duk abinda ke ranshi ko me zai faɗa na tabbatar babu ƙarya cikinta, na riga na cuci rayuwarshi na mishi illah, ban nemi yafiyarshi bane ba don ban yi nadama ba, nayi shiru ne saboda ban san me zan ce ba, ban kuma san ta wani hanya zan bi wurin taya shi gyara kuskuren da nine silar faruwarsa ba, amma ke ina rokon yafiyarki akan kalamaina na jiya"
Cokalin ya ajiye ya miƙe zai fita Alaya tace
"Abba!"
Tsayawa yayi daidai kusa da Maami ba tare da ya juyo ba tace
"abin da na faÉ—a a kotu É—azu shi zan sake maimaitawa, kowa yana kuskure hakanan kowa na laifi saidai wadda ya fahimci laifin shi ya kuma tuba yayi niyyar gyarawa be yi kuskure ba, hasali ma abin da ake fata kenan, Don Allah karka saka damuwa a ranka Abba.
Ya Mukhtar na fahimci yadda kake ji a ranka, sai dae ba hakan ne ya baka daman aibata mahaifinka ba, babu inda ya bamu wannan daman idan har da gaske ka gyara kuma ka chanza daga Mukhtar na da to kayi kokarin saita harshenka wurin magana da iyaye don Allah ya É—aga darajarsu.
Maami Don Allah da manzonsa kiyi haƙuri, fushi ko rashin yafiya duk ba zai chanza komai ba, mu haɗu duk mu gyara abin da ya ɓaci a baya adu'ar ki ce a yanzu Allah ya ƙarba, muyi kokarin zama one Big happy family Don Allah"
Mukhtar da kanshi ke ƙasa hawayenshi na ɗiga bisa kan dining ɗin a ranshi yake jin Alayah is too good for him, be yi abinda Allah zai bashi ita matsayin mata ba, bayan duk abubuwan da suka faru ji yadda take magana kaman be gallaza mata ba, har ta yafe mishi kenan? Lallai idan zata iya yafe mai kuma har ubangiji zai iya yafe mai ya barshi da mace irin Alayah to shi me zai hana shi yafewa Abba? Maami ya ɗago ya kalla tana zub da hawaye itama idanunta na kan Alayah, har ranta take son yarinyar Allah ya mata baiwa na daban, idanunta ta maida kan Abba da jikinshi yayi matukar sanyi, kwarai suna bukatar cikakken farin ciki na tsawon shekarun da suka rasa a gidan ko da kuwa ba zai tabbata ba, shiyasa yake ganin gazawarshi ya kuma tabbatar komai ya faru tun farko daga shi ne, idanunshi ya lumshe yana jin kanshi na sarawa babu tantama hawan jininshi ne.