← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 36

Sashe 28

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Be iya yayi magana ba sai a sadda ya ji sassanyar Muryar mahaifiyarshi da ma sam be lura da ita ba tana cewa
"Mukhtar kap rayuwarka cikin kowani rana baki na bai taɓa hutawa ba wurin yi maka nasiha akan abubuwan da kake aikatawa, ban taɓa gajiyawa ba da ɗaura ka akan hanyar Allah da manzonsa haka ban taɓa gazawa da kai kukana wurin Mahalicci ba da ya shirya min kai, Mukhtar ka san irin kunar da nake ji a zuciyata daga jiya zuwa yau kuwa? Wani irin rashin imani ne wannan ku haɗu har ku uku ku haikewa yarinya karama ku zalunci rayuwarta da na iyayenta, ku shafa musu baƙin fentin da ba zai taɓa gogewa ba a rayukansu? A yau ba don umar da kake ƙi ya roƙeni da mu zo ko zaka iya faɗa mana sauran abokan cin mushenka, ya kuma yi magana da shugaban yan sandan da ya ci alwashin ba zai taɓa bari ka sarara da azaba ba har sai ka bayyana sauran ka kuma amshi hukunci daidai da abin da ka aikata ba da baka ganni anan ba, ashe abin da ka aikata kenan ya hanaka bacci shekaran jiya?"

Cikin sanyin murya ya ce
"Kiyi haƙuri Maami, bani da kwarin gwiwar neman yafiyarki kasancewar na shafe tsawon rayuwata ina chusa miki baƙin ciki, amma ki yarda da ni kaman yadda na faɗa miki shekaran jiya tun nasihohin Baba ban sake kuskuren aikata wani abu marar kyau ba, na kasance cikin tsantsar nadamar abubuwan da na aikata, na kuma shafe kwanaki cikin tunanin ta inda zan fara gyara kurakuraina, haƙiƙa na san ba zan taɓa gujewa hukuncin ubangiji ba kasancewata me saɓo a gareki, na kuma san ko da kin yafe min zuban hawayen da nayi ta saka ki a baya zai iya bibiyar rayuwata a gaba, Maami ban san ko waninku zai iya yarda cewa ban aikata laifin da ake tuhumata dashi ba, hasali ma ban san sa'adda suka aikata ba Dukda ina a wurin, na bar hakan ne cikin soman taɓin girbe laifuka na, Allah shi ne shaidata sai kuma su da suka aikata"

Idan Maami bata ce ta jijjiga da kalaman Mukhtar ba tayi ƙarya, sai de tana tsoron kar mafarki take, ko kuma wasa yake, shiriya take gani yana sauƙowa ɗan ta? Kuka ta fashe dashi na rasa abin yi, C.p, iyayen yaran da sauran manyan hukuma dake tsaye a wurin basu yarda da zancen shi ba, Baba kuwa hamdala yake adu'o'insu sun karɓu.

"Kai da su waye ne?"
Maami ta sake watso mishi tambayar
Ya É—aga kai kaman zai kalleta sai de kunyar kallonta yake ji, a hankali ya sake maimaita
"Ban aikata ba"
Baba ya ce
"su waye ne?"
A hankali ya faÉ—i sunayen nasu, tuni C.p ya kwashe ya kuma aika a kamo su, sun kuma ba wa baba da Maami hakuri akan za'a mayar da Mukhtar Cell dole dae su haÉ—u a court tukuna a tantance me gaskiya.

Haka suna gani aka maida shi, Maami jikinta yayi sanyi sossai tana kallonshi har aka tafi dashi, ita da baba suka fito baba na sake yi mata nasiha har suka sauƙe ta gida drivern shi ya ja zuwa gidan shi.

Zaune ta samu Alayah tayi zurfi cikin tunani, dafa ta tayi
"Binty ban ce ki daina zama kina wannan tunane-tunanen ba?"
Ajiyar zuciya ta sauke kan ta kakalo murmushi tace
"Maami kun dawo?"
"Eh mun dawo, ya cikin? Ba wani matsala ko?"
Kasancewar tayi karyar ciwon ciki duk don gujewa tafiya ganin Mukhtar da ita ya sa ta kakalo murmushi
"Eh Maami ya daina"
Ajiyar zuciya Maami ta sauƙe, sai taji tana son bai wa Alaya labarin abin da ya faru
"Ko kin san Mukhtar ya ce baya cikin waenda ake tuhuma da wannan al'amari?"

Da sauri ta ɗago kai, one thing da zata iya cewa ta sani akan Mukhtar shi ne da matukar wuya yayi ƙarya
"Kuma Maami a baya ya aikata irin haka aka ce?"
Shiru Maami tayi sai Alayah ta ga kaman tambayar be dace ba
"haka ne, maƙasudin ƙarasa taɓarɓarewar rayuwar shi kenan Alaya, kila da be aikata hakan har ya shiga prison a chan Kasar ba ya haɗu da manyan thugs kila da hakan be faru ba, kaddara ta rigayi fata. Amma a yadda Mukhtar yake magana a yau har cikin raina na gamsu na kuma amince da be aikata ba ɗin, Fatana shine Allah ubangiji ya sanya ya shiryu a gasken"
Alaya ta amsa da Ameen.

Sun É—an tattauna akan jikin ummi inda Maamin ke faÉ—a mata umar ya ce bayan lafawar komai in har babu wani cigaba za'a fitar da ita waje, tana cikin total coma ne tsakanin rai da rayuwa.

Alhj hammad Abdulhameed chanji a yadda al'amari ya zo mishi ta sa dole zuciyarshi ta durkushe, laifukanshi suka dawo suka lulluɓe shi, idanunshi sun rine kwarai a kwanakin da suka biyo baya a jere, kwanakin da suka kasance na zaɓe da kuma kirga kuri'u tare da faɗin sakamako, babu abinda ya fi girgizashi irin mummunar shedar mutane, yana ji yana gani ya faɗi wanwar hakan ta sa ya tafi tunanin kalmomi na karshe da suka haɗa shi da ɗan shi na biyu a lokacin da shi da Mukhtar suka sanya shi gaba da kyara da kuma hantara haɗe da baƙaken maganganu masu zafi don kawai ya dage da iyakar karfinshi wurin hana su saɓon ubangiji, yayi uwa yayi makarbiya akan duk wani mummunan sana'a da zasu yi, a lokacin gani suke kaman sanya idanu ne, toshe cigabansu ne yake tunda baya taɓa bari kayakin su ya shigo Nijeriya bare har ya shigo hannunsu su sayar, sun kasa tuna cewa yana da daman ɗaure su amma ya ki yin hakan a duk son shi su shiryu su dawo kan hanya, lallai da be raini Mukhtar bisa gurbatacciyar hanya ba duk wannan abubuwan ba zasu faru ba, kalaman mutane da shaidarsu a kan Mukhtar da ma shi da ake ɗaurawa laifi da mahaifiyarshi da bata ji ba bata gani ba baza su kawo karshen rayuwarshi ba kuwa?

"Ban taɓa ƙin ku ba, ba kuma zan taɓa hakan ba, zan nesanta kaina da ku Dukda hakan ya zame min wani babban giɓi da abin baƙin ciki musamman in na duba cewa kun tura ni nesa da farin cikina wato mahaifiyata, hakan ba zai taɓa sa na bari kuyi abin da kuke so ba Abba, ku sani in har baku neme ni ba ni ba zan taɓa neman ku ba sai dae idanuna suna kanku, haka kuma a duk sadda na yi ra'ayi zan tako har cikin gidanka in ga mahaifiyata don ita bata ƙi ni ba, bata sanya min bakin cikin da zai farauci farin cikina da nesanta kaina da jama'a ba"

Har ya miƙe sai ya juya yayi taku biyu uku kan ya ja tunga ba tare da ya juyo ba ya soma cewa.

"Idan Yaro ya faɗi tashi yake ya ruga a guje, idan babba ya faɗi ya kan waiwaya ne ya ga me ya kayar dashi, idan ba ku yi nazarin jiya ba gobe ba zata taɓa yi muku kyau ba, ku daurewa zuciyoyinku kuyi rayuwar da zata zamto abin koyi ga na baya abin sha'awa ga na tare da ku, abin kishi ga makiya sannan abin alfahari ga dukkan masoyanku, ku kiyaye saɓani da mutane watarana za'a yi shaida walau da rai walau babu, wannan ɗin kusan saƙon mahaifiyata ne gareni inda take bani kwarin gwiwar zama Kunkuru cikin macizai na zaɓi na raba da ku ne saboda kuma ku rabauta... Na barku lafiya"

Daga wannan rana ba zai ce ya sake ganin umar ido da ido ba, shekaru sama da Goma sha biyar, ya wofintar da rayuwarshi saboda kawai yana gyara musu tasu, umar ya kan zo har cikin gidan amma baya taɓa bari ko da a hange ne su hangi juna, hakan be taɓa damunshi ba sai a yau, hawaye kawai yake zubarwa motsin kofan shi ya ji, be damu da share hawayen ba har Maami ta shigo, kusan yanzu tana rayuwa dashi ne akan dole, haushi da takaicinshi karara yake gani cikin idanunta, abincin hannunta ta ajiye ba tare da ta tanka ba ta juya ta ɗauki na safe yadda ta ajiye shi be taɓa ba, taku uku tayi tace

"Ban sani ba ko har yanzu wannan soyayya ta Mukhtar na nan dankare a zuciyarka, na shiga dumbin mamakin sanin cewa har yau baka iya zuwa inda yake ba baka kuma damu da halin da yake ciki ba, hasali ma maƙiyinku shine yayi uwa yayi makarbiya wurin ganin cewa ba'a zalunci ɗan uwanshi ko an illata shi ba, duk ba wannan ne ya sa na tsaya ba, na tsaya ne in ce maka gobe da misalin karfe takwas za'a shiga court an tsagaita sabd zaɓe, ban roƙi ka shiga lamarin don ɓinne gaskiya ba sai dae akwai buƙatar zuciya ta ɗanɗani azabar aikinta..."
Tana kai nan tayi gaba, kanshi ya shafa yana huro iska, rudanin da yake ciki yasa be san komai akan abin da ke faruwa da Mukhtar din ba, be ba Mukhtar laifi duka ba ya raba ne a tsakaninsu hakan yasa ya mance Mukhtar din na É—an lokaci, kuma a yanzu bashi da wani kwarin gwiwar fuskantar kowa da wannan lamari...

COURT

A yadda aka fito da su zaka yi tsammanin babu wadda ze iya magana cikinsu sbd yanayin wahala da suke ciki wadda ba sabon su bane, shi Mukhtar be iya ya kalli kowa ba, yayinda Alayah ta maida hankalinta kanshi tana kallonshi, har yau bata jin komai akan Mukhtar bayan ƙimar mahaifiyarshi da kakanshi, tunaninta na kai kawo ne akan shin ko shi ya aikata ko ba shi ya aikata ba zata iya cigaba da zama da shi kuwa? Zuciyarta ta riga ta kuntace shi, duk yadda tayi kokarin chusa tausayi da soyayyar Mukhtar a ranta ta kasa bata san cewa duk daɗewar sanda a ruwa baya taɓa zama kifi ba...
Chapter 28 · 0% Book details