← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 36

Sashe 24

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaman wadda kwai ya fashewa a ciki haka yake jan kafafunshi jin gwiwowinshi na shirin sagewa su butulce mishi wurin kasa ɗaukar gangar jikinshi, zubewa yayi kan kujera zuciyarshi na wani irin yamutsuwa tare da kwakwalwan kanshi dake ta aikin tariyo kalamanta, wani irin sanyi yaji yana ratsa shi a hankali zazzafar zazzabi ya soma sauƙo mishi, kalamanta sun mishi nauyi sossai, rashin fahimtar shi da bata yi ba sai ya so haukata shi,
Miƙewa yayi don barin gidan ko zai shaki iska mai kyau sai ga Maami ta shigo.

A hankali yace
"sannu da dawowa Maami"
Kallon shi tayi da mamaki don ba halin shi bane hakan, sai kuma ta kula kaman bashi da lafiya ne kaman bazata yi magana ba sai kuma tace
"yauwa! Lafiya kake kuwa? Ko dai cikin shaye-shayen ka shayo abin da yafi karfin ka?"
Idanunshi ya runtse da ƙarfin gaske wani zafin ya sake ratsa zuciyar shi, dama haka ake welcoming wadda ya ɗauki hanyar tuba? Dama wannan na daga cikin kalubale da illar shaye-shayen ko kuma daga mahaifiyarshi da matar shi ne?

Be iya ya tanka ba ya fice daga gidan, da kallo ta bishi har ya bace kan ta haura stairs, ɗakin Alayah ta tura don dubata sai ta sameta zaune tana game a wayanta kaman ma bata yi kukan matsalar gidan aurenta ba, taji sauƙin abin sossai da ta samu fitar da abin da ke ranta kuma da gaske ta gama zama da Mukhtar.
"Sannu da dawowa Maami"
"yauwa binty ana hutawa ne?"
Kai ta gyaÉ—a tana murmushi
"Maami kin yi waya da asibitin? Sun yarda zasu bari a ganta nan kusa?"
Kai ta gyaÉ—a tace
"Eh mun yi magana, baba ma dai ya bada shawarar a fitar da ita waje kawai amma dai muna nazarin hakan da umar, kar ki damu zata samu sauƙi in shaa Allahu. Yanzu dae albishir"

Murmushi ne kwance bisa fuskanta da ya ƙara mata kyau sossai tace
"Goro Maami fari ƙal ma ba ja ba"
"Kin samu admission a skyline university"
Tsalle ta tashi zata yi da hanzari Maami ta riƙe ta tana dariya, rungume Maamin tayi hawaye na tsillo mata tace
"Alhamdulillah Maami na gode, na gode sossai Allah ya saka miki da alkhairi ya shirya miki zuri'a, Allah ya amsa dukkanin Adu'o'in ki ya biya buƙatun alkhairi"
Cikin murmushi ta amsa da Ameen, sai kuma ta É—ago ta
"Amma me ya sa kika zaɓi cyber security bayan baya cikin duk courses da kika lissafo min kina so?"
Cikin murmushi tace
"haka kawai na ji ina son karantar shi, kila shine Allah ya zaɓa min"
Har daren ranar murna take da samun admission nata, Allah sarki Da ummi na cikin koshin lafiya da sai tafi kowa murna ta tabbatar da hakan.

Da dare ta isa jikin kofa don rufewa kenan taji kaman ana magana murya sama, idanunta ta lumshe babu shakka muryan Abba ne kuma ta tabbatar da Maami yake don kaman magana ne da ya dangancesu Dukda bata jin shi clearly, da jikin kofan ta jinginu ba zata taba son su kasance tasgaro ga rayuwar Maami ba, ita ce mutum na farko a rayuwarsu da ta nuna musu suma mutanene kaman kowa suna da muhimmanci kuma suna da Ƴancin rayuwa yadda kowane mutum ke yi, ita ta basu mafaka a sadda suke tsakiyar rana da kunar zafin ta, da ba don ita ba da kila yanzu babu Umminta don ta tabbatar ba jinya Abban meela ze yi mata ba, sannan ga damar karatu ta bata wadda zai sauya mizanin rayuwarta, amma su kuma suna kokarin dakile farin cikinta da zaman lafiyanta, tana jin irin barazanar Abba har da aurenta yayi mata kan ya zo ya wuce kaman iska.

Ta jima tsaye wurin kan ta isa ga gadonta ta kwanta idanunta runtse tunaninta ya tafi gabaɗaya ga neman mafitar wannan matsalar kuma, cikin bacci ta ji ana buga mata da sauri kuma a ɗan tsorace ta miƙe zaune, idanunta ta kaikaya kan ta sauko gabanta na faɗuwa ta tsaya nesa da kofan

"wa....waye?"
Shiru aka yi sai aka sake knocking
"waye ne?"

****

Zaune su ke a club É—in shi dae ko idanunshi baya buÉ—ewa in banda ma matsawar su Nawwaz babu abin da zai kawo shi club É—in amma sune kaÉ—ai abokan shi su ne masu debe mai kewa cikin sabuwar rayuwar da ya tsinci kanshi, En matan dake ta damunshi ne É—aya ta matso ta shafa shi
"Mukhy whats wrong with you? We dont like this mukhy we want our old mukhy back, menene kake so? Ka zo mu debe maka kewa mu mantar da kai duk wani damuwa, mu baka farin cikin da ka jima baka samu ba..."
Hannun da take shafa shi ya ture ba tare da ya buÉ—e idanun ba
"don't you dare touch me again"
Ya faɗa chan ƙasa ƙasa har yanzu kalaman Alayah ne ke farautar rayuwarshi, idanunshi ya buɗe ya sauke kan smart dake rungume da yarinyar da ta gama lafaza shi a yanzu tsaki ya ja me karfi barikin fa kenan, Tsam ya miƙe tare da miƙawa smart din hannu ya bashi key.

Ture yarinyar smart yayi tare da Miƙewa
"ka san bama barin ka driving cikin situation din nan muje in kai ka inda zaka"
Nawwaz ma Miƙewa yayi suka fito su huɗu zuwa motar shi, da gudu suka bar club ɗin, sauran su biyu duk a Buge suke yayinda smart dake driving ke bankawa cikinshi Shisha, shi dae oga kwata Kwata na kishingide abin duniya ya dame shi, daidai wani unguwa motar ta tsaya chak, idanunshi ya buɗe ya dubi smart
"ya dai?"

"Wlh ban sani ba mukhy ko zaka duba mana don ko na je babu abin da idona zai gani?"
Gaban motar ya buÉ—e ya fice yayin da smart ya buÉ—e mai bonet daga ciki, ganin ya É—an jima yasa duk suka fito, wurin shiru sannan hasken wurin ba sossai bane, layi ne a chakude da gidaje kala uku akwai na masu kuÉ—i jefi jefi haka akwai na daidai misali sai kuma na talakawa da suka fi yawa.

Wata yarinya ce da bata wuci 16 ba ta taho hannunta riƙe da tray tana kuka, kuɗin cinikin ta ta ɓatar gashi matar ubanta bata da sauƙi akan sana'arta shiyasa ta kai yi warhaka bata koma gida ba, ta sa baban ta da Yayanta yanzu sun dawo idan kum yaddikonta ta kanainayesu da maganganun ta ɗaure ta zata kara yi yau ta shiga uku da babanta tunda duk abinda yaddikonta ta faɗa daidai ne, har ta wuce su ma bata maida hankali kansu ba sbd nata matsalar.

Nawwaz ne yace
"kai yarinyar nan tayi smart, anya ba zamu latsa ba?"
Area É—in suka dudduba jin shiru sossai yasa babu wani tunani yadda suka saba kayansu sa'i da lokaci suka bi bayanta, da bakinta suka fara da karfi suka É—aure suka jata gefen ciyayi, sam Mukhtar be san me suke ba don hankalinshi na kan duba motar sbd babu abinda yake so a yanzu irin ya je gida ya kwanta ya cigaba da tunani.

"Smart tada motar mu ji"
Yayi maganan ba tare da ya É—aga kai ba, jin shiru ya sa ya É—ago ya dae san sun fito waje to komawa suka yi? Sake motar yayi yana zagayowa sai de be ga kowa ciki ba, jin kaman nishi ya sanya shi É—aga kai da sauri ya kallesu chan da alama ma sun gama lalata rayuwar yarinya da gudu ya isa ya ture Nawwaz, É—agowa yayi ya tsinkawa smart mari
"Me kuka yi? Me kuka aikata? Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Daidai lokacin yarinyar ta kwalla ihu sai ga hasken touch ana kiran sunan da basu gama gane na wacece ba, da gudu suka yi mota Nawwaz janye da Mukhtar da da alama tsayuwa ya so yi, ihu yaron ya fara yayinda tuni smart ya figi motar baban ne da yake gani dishi dishi ya riƙe plate number ɗin, babu shakka sun kassara rayuwarsu ko daga yadda yayan yarinyar ke kuka sossai yana dagota ya rungume ya san hakan....

*Toh fa, Mukhtar sawu ka taka ko ya abin yake ne?*

*karku manta book 2 na kuÉ—i ne, muna gama book 1 zamu É—aura in shaa Allah zaki iya yin payment É—in ki anan kan a gama É—in
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
Sai shedar biya ta
09039206763 in shaa Allah za'a saka sunan cikin list na paid da muke dasu ƙasa.
Thank you sai na ji ku

🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page Seventeen*

"Me kuka aikata Nawwaz? Akan me zaku yi raping yarinya alhali kun bar yammata sama da hamsin waenda suke shirye da tayin ku? Why? Why??"
Gabaɗaya hankalin shi ya tashi irin yadda ba'a zato, su karan kansu sun shiga mamaki, sun ga dae har a ƙasar da ma ya fi Nigeria tsaro da komai yayi raping yarinya wanda ma sanadiyar zamanshi prison kenan har aka kore shi ya dawo Nigeria da karatu, to me zai dame shi anan da ma ba lallai a bi diddigi ba ko ma an bi suna da kuɗi wadda sun tabbatar a ƙasar nan zai musu maganin komai.
Ganin suna kokarin tursasashi maida komai ba komai bane yasa ya daka wa smart tsawar ya tsayar da motar kuma su fitar mai daga cikin mota, haka ya baɗe idanunshi da toka sai da suka fita ya zagaya ya figi motar kaman baya son ranshi, har lokacin wani irin tension yake ji a cikin jikinshi gidanshi ya ƙarasa a parlor ya zube, ya rasa ma kalar tunanin da zai yi me yaran nan suka aikata haka?
Chapter 24 · 0% Book details