← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 36

Sashe 18

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai tayi tana kauda kanta daga wani abu da yake shirin bata.
"Ya..m...mukhtar menene?"
Kashe idanu yayi yace
"ko kin san menene ko baki sani ba dole zaki sha"
Ya karashe yana janyota zuwa fili abokan shi suka É—auki shewa.
"Game muke kin san Truth or dare?"
Be jira amsanta ba yace
"an yi daring É—ina na bugar dake don haka buÉ—e baki malama"
Idanunta gabaÉ—aya ta fitar, a lokaci É—aya jikinta ya É—auki mazari, me yaya muktar ke nufi? Shayar da ita abun maye ze yi? Hawaye ne suka soma zuba babu birki cikin girgiza kai tace
"Don Allah yaya Mukhtar kar ka yi, kar ka cutar dani, ya muktar hannuna zafi...kirjina ciwo don Allah kar ka sa ni saɓawa mahallicina a dole, karka zalunceni dayawa mana have a pity on...."
Bakin ya murÉ—e se sowa suke suna ambaton sunanshi ya soma bata, duk yanda tayi ganin ta kubce ko bata sha ba hakan be yiwu ba, gimtse hancinta yayi seda ta sha kaÉ—an kan ya sake ta ganin yana shirin kisa, a wurin ta zube ta tura yatsa cikin bakinta ta soma amai, tun tana yi har ta gigice ta fice hayyacinta gabaÉ—aya, wata ce a cikinsu da jikinta yayi sanyi da tausayin Alayar tace
"Gaskiya baku kyauta ba, tunda bata sha me na shigo da ita cikin wannan game naku? Kullum baku da buri da ya wuce ku wulaƙanta ta, mu faɗawa kan mu gaskiya mana kai Mukhy kaine babban wawa, wanda be san abinda yake yi ba, taya zaka shigo da matar aurenka na sunna cikin wannan irin rayuwa, wani irin jahil....."

Gigitaccen marin da Muktar ya sake mata ne ya saka ta kwala ƙara ta yanke maganan, kan tayi motsi saurayinta ya tashi ya rama mata, kwalba mukhy ya janyo ya rotsa mai, a take jini ya fara tsiyaya kaman wasa sai gashi wurin na shirin zama karamin Abbatoir don faɗa ne sossai ya kaure tsakanin saurayin chan da shima ɗan wani ne da kuma Mukhtar kowanne kuma yana da abokan zagi, ita dae Alaya ta samu ta rarrafa ta faɗa ɗakinta ta datse kofa a wurin ta kwanta, kanta se juyawa yake da alama de kayan Mayen ya taba ta, tayi kuka har ta rasa hawaye, tana ta rokon Allah ya yafe mata yana gani ba laifinta bane, an fi awa biyu kan taji gidan yayi tsit, a wurin tayi bacci Washegari ma seda ta kai wuraren sha biyu kan ta farka sbd buga mata kofa da ake tayi kaman za'a ɓalla.

Dafe kanta dake sarawa tayi ko Sallar asuba bata yi ba, hawaye ya gangaro mata ta sanya hannu ta share kan ta motsa a hankali ta miƙe dafe da gini ta miƙa hannu ta buɗe kofan jin bugun ba na ƙare bane, woman Police ce tsaye tana kallonta
"Madam ko zaki iya ara mana mintuna biyu a cikin lokacin ki?"
Kaman bazata yi magana ba tace cikin dasashiyar muryarta
"Lafiya?".
"Shin kina cikin gidan nan gabaÉ—aya yinin jiya zuwa dare?"
Kai ta gyaÉ—a ba tare da ta amsa ba
"ko kin shedi hatsaniyar da ya faru a jiyan?"
Nan ma ta girgiza kai tana kallon matar da take ta karantarta..

"Ba zaki samu ko wani sheda daga gareni ba, ko ma menene kike so pls ki samu waenda suka asassa abun, ina da uzuri se anjima"
Ta ƙarasa a sanyaye kan ta tura kofan ta rufe ta juya zuwa bayi, seda tayi wanka ta zo tayi sallah tana rokon yafiyar Allah kan ta fita ta nemi abinda zata ci ta sake dawowa ta rufe ɗakin ruff ko bi ta kan wargajejjen parlorn bata yi ba, idan tace yanzu bata soma developing wani irin tsana na Mukhtar ba to wlh tayi ƙarya, a ƙasan ranta tayi ta ja mishi Allah ya isa kuma tana fata ya saka mata, ashe a chan kam case sossai aka yi sbd karfe da karfi ne suka haɗu sai da shudin Goshi case din ya mutu, nan Alhjnsu yayi ta mishi faɗa akan hakan ze iya ɓata mishi siyasa kar ya sake, ya dae ji ne ko da ya dawo ya tarar parlorn haka buga mata kofa yayi ta buɗe ba tare da ta kalleshi ba sai shima ya ji shakkan kallonta don fuskanta ba digon walwala ko farin ciki.

"Ki je ki gyara parlorn nan"
Yana kai nan ya juya ya fice, ta jima sossai kaman bazata yi ba se ta fito ta soma tattare parlorn incident ɗin jiya na dawo mata lokaci lokaci tana share hawayen baƙin ciki.

BAYAN WATA ÆŠAYA

Yammaci ne sakaliya tun safe bata fita daga ɗakin ba, bata jin karfin jikinta sam ganin yunwa ze iya mata illa don daga kwance ma jiri take ji yasa ta miƙe ta fito sanye da dogon hijab as usual ta shiga kitchen.

Rabin taliya ta dafa da kwai dafaffe guda biyu ta zuba a plate, ta juya frigde don ɗauko ruwa se ga Rita ta shigo kai tsaye plate ɗin ta ɗauka zata fice, shan gabanta Alaya tayi tana jin ranta na ɓaci

"Baiwar Allah lafiya?"
Da mamakin tsaurin idanun yarinyar Alaya tace
"ba lafiya ba kam, taya zan dafa abinci don na ci ki zo kawai ki É—auka ba magana ba komai kaman zamanki nake?"
Idanu Rita ta ɗan fitar cikin mamakin yau Alayar tayi magana haka ita bata taɓa ma jin dogon magana daga bakinta ba.
"Karfi ya ci daru ya danne, bani hanya in wuce hai village girl kawai"
Ranta ta sake ji ya zo mata wuya yarinya fitsararriya ta shigo har cikin gidanta tana zaune duk kauda kan da tayi be isa ba sai ta haɗa da zagi da cin zarafin ta ko da shi ke ba laifinta bane, cikin ɓacin rai tace

"Ai kuwa gwara da ni sau dubu saba'in in ma na amsa ni village girl din kenan, ko ba komai village girl ta fi ashawo...."
Watsa mata abincin gabaÉ—aya Rita tayi jiki yayinda ita kuma Alayah ta dauketa da zazzafar mari.
   hango Mukhtar bayan Alayar yasa ta dafa kumatu ta saki razananniyar ihu, cikin kuka tace
"Wallahi yau zan bar maka gidanka Mukhy, har ni matarka zata É—aga hannu ta mareni akan banza taliya? Ni dae?"

Da sauri Alayah ta juya zata yi magana ya kifa mata mari, yayi ball da ita bata san ta tafi kaman wacce iska ya ɗauka ba seda taji ta sauƙa a kafafun mutum, ɗagowa tayi bata gani daidai sai taga Maami ce da sauri ta miƙe ta faɗa jikinta ta soma kuka me cin rai, kan Maami tace tayi wani yunkurin kawai Alaya ta yanki jiki ta faɗi ƙasa...

"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Mukhtar ka kashe musu Æ´a ka huta, nace ka huta.."
Tana nufo shi ne take maganan
"wani irin zuciya ne da kai? Wani irin baƙin zuciya ne Allah ya halicceka da ita? Ashe baka da tausayi Mukhtar dubi yadda yar mutane ta koma"
Kwalan riganshi ta chakwamo
"Allah ya saka mata, wallahi Allah se ya bi mata hakkin ta, Allah ya mata sakayya tun a duniya, mugu azzalumi.."
Hawaye take yi bibbiyu, hannunta yake kokarin cirewa a wuyan shi tana sakin shi kuwa ta soma zuba mishi maruka hagu da dama tana kuka.

Ganin hakan baze mata ba ta soma neman abinda zata kwada mai ko zata huta bata yi taku biyu ba itama ta yanki jiki ta faɗi ƙasa. Se a lokacin ya gigice cikin hanzari y dago ta yana kiran Maami Maami, sede Maami tayi nisa, daukanta yayi da gudu zuwa motanta driver ze ja yace ya jira shi, da sauri ya koma ya ɗauko Alayah da banda haushinta babu abinda yake ji dama tsakanin shi da mahaifiyar yaya gashi tana kara ɓatawa, ta wannan ne kawai zasu iya samun matsala da Abbansu don yana son matarshi.

A motanshi ya saka ta yana gaba drivern Maami na bin su a baya har asibiti, cikin gaggawa aka Karɓe su emergency, likitoci suka rufu a kansu wasa wasa har aka yi Magrib kan suka samu kan Maami, Alayah kam se kusan bayan isha ma likita mace ta fito tana kallon Mukhtar
"kaine mijinta?"
Kai ya gyaÉ—a yana kallonta
"Toh Congratulations matarka tana É—auke da ciki na tsawon sati biyar sede akwai karancin nutrient a jikinta, and ciwon zuciyanta yana so ya tsananta kaman yadda jininta ke hawa duka wannan illah ne ga lafiyarta a gaskiya ya kamata ku kiyaye, a ka'idar aiki ma bayan an mata wanchan aikin zuciyar be kamata kuma ya sake hitting haka ba"

Shi duk sauran jawaban ma baze ce ya ji ba banda batun cikin nan da ya ji.
"Ciki???"
Ya maimaita kan ya sake cewa
"do you mean pregnency?"
Kai ta gyaÉ—a, ya ja wani dogon tsaki ga ta inda ya tsani auren ai, yarinya ta zo banda gidahumanci babu abinda take mishi kwata kwata ko shekara bata rufa ba ace wani ciki, shiyasa ya fi son hulda da wayayyun mata shi be shiryawa haihuwa yanzu ba...

"Look likita ina so ki zubar da shi ko nawa ne zan biya"
"wannan ba aikina bane, kuma bama haka a asibitin nan amma zaka iya zuwa gaba se ayi maka"
Har ta juya yace
"ko don lafiyanta? What if cikin ne yake triggaring ciwon zuciyar? I th....."

"MUKHTAR"
Maami ta kira sunan, se kawai ta sulale ta zauna a wurin tana hawaye a ranta tana istigfari bata san me zata yiwa Mukhtar ya shiryu ba, babu me fahimtar ciwon ranta babu me gane abinda take ji da takaici da haushin É—an da ta haifa a cikinta se wacce jarabawa irin wannan ya faÉ—arwa, muryarta a rarrabe tace
"ka fice daga asibitin Mukhtar wallahi na tsani ganinka"
Da sauri ya É—ago ya kalleta, ze yi magana ta daka mishi tsawa tana dafe kanta dake juyawa.

"I Said Get outttt!"
Chapter 18 · 0% Book details