Sashe 32
Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A chan ma cikin natsuwa yake shigar da kanshi gareta, har ya gama ci suka fito magana yake mata a hankali tana bashi amsa, anan ta yafa babban mayafinta ta É—auki jakanta tace
"Maami mun tafi"
Maami tace
"Allah ya tsare ya bada sa'a, sai kun dawo"
Suka fice a tare gwanin sha'awa, shi ya buɗe mata hadaddiyar motar tashi sport car ce BMW ta shiga shima ya zagaya ya shiga ya ja suka fice, kaman yadda ya faɗa campanin motocin shi suka tsaya suka shiga, ana ta miƙa gaisuwa cike da tsoro saboda sanin shi masifaffen marar haƙuri, kuskure kaɗan kashin ka ya bushe, ga mamakin su yau sai gashi sai murmushi yake saki ba wannan hayaniya da hargagin, har kyautar kuɗi ya musu suna ta mishi godiya cikin jin daaɗin sauyin da suka gani a tare dashi.
Wata coffee hyundai ta zaɓa ya mata kyau sossai, a take ya bada umarnin ayi wa motar duk wani checking kan yamma a kai mishi gida, daga nan school suka nufa duk yadda ta so ya barta daga haraba ya tafi zata yi duk abinda bata gane ba ya ƙi, a tare dashi suka yi ta yin komai, duk inda da bin layi zai nema mata seat ta zauna shi ya bi Layin sai an iso ya kirata ta zo su yi abinda zasu yi su kara gaba, kowa kallonsu yake gwanin sha'awa lallai haƙuri na da riba, duk masu yi mata kallon ta dace ta tsinci dami a akala basu san irin tsanin wutan da ta taka zuwa wannan wuri bane.
Karfe ɗaya suka gama komai, sai da suka tsaya masallacin makarantar ta shiga ɓangaren mata shi ya shiga cikin masallaci suka yi sallah kan suka fito, restuarant me kyau ya kaita suka ci abinci kan suka nufi asibiti, har yau ba'a bari an shiga wurin ummi ba, hanganta suka yi ta fara hawaye tuni ya jinginata da jikinshi yana lallashinta, sun ɗan jima kan suka fito a reception yace ta ɗan jira shi anan yana zuwa, wayanshi dake ta ringing tuntuni yana rejecting yanzu ma shi ya sake ɗaukar ringing wayan ta bi da kallo har ya ɗan yi nisa kan ta ga yayi picking ya ɓace mata.
"Rita i Said leave me alone! Ki kyale rayuwata na fita daga cikin sabgar rayuwarku daga ke har su Zee wacce ta sake kirana wallahi sai na mata rashin mutuncin da baku taɓa tunani ba, rubish"
Yana kai nan ya yanke wayan ba tare da ya jira amsar ta ba sim zai chanza bazasu dagula mai lissafi ba, yana kokarin zare sim ɗin saƙo ya shigo, kalma ɗaya da ya gani shi ya ja hankalinshi wurin dubawa, wani irin jiri ne ya kwashe shi da sauri ya dafe gini don ƙoƙarin zubewa ƙasa yake, a take zufa ta karyo mishi a kan lips ɗin shi ya furta
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun.."
*Kar ku sha'afa Al'ajabin So littafin kuÉ—i ne part 2 din zai zo muku akan naira 500 kachal har yanzu muna da gagarumin tafiya a gabanmu.
Zaki iya biya ta wannan asusun
0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763
Sai na ji ku*
🖤Gureenjoh🖤
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjo)
Adabi Writers Association
Book 1
*Page Twenty Three*
Zaune a gaban Dr Ahmad dake ta murmushin ganinshi da yanayi na daban yace
"Na zo ne ina bukatar a yi min tests ba zan iya haƙurin cire folder da sauransu ba please do the needful"
Sarai ya gane shi their rude patients husband Dukda yanzu Meddy specialist sun karɓe musu ita sbd finsu kwarewa a harkar zuciya sai dae ya san Maami ya kuma san Umar tunda ta hannunshi suka karɓi ummi.
"Wani iri kenan?"
Numfashi ya ja kan yace
"Komai da komai, precisely HIV/AIDS"
Da sauri Dr Ahmad ya kalleshi, jingina yayi ya lumshe idanu yace
"don't be suprise, it might be the product of my sins"
Ajiyar zuciya Dr Ahmad ya sauƙe kan ya danna kiran wata ma'aikaciyar jinya ya bata umarnin zuwa da kayan diban jini, tubes biyar ya buƙata.
Ko da ta kawo da kanshi ya tashi yayi sticking finger ɗin shi for the rapid antibody test na HIV kan ya saka syringe ya zuƙi jini sossai a tubes din nan, a na karshen ne ya ɗaga kwalban sama yana kallon jinin for seconds kan ya ajiye kan tray ɗin, rubutu yayi a kan plain sheet me ɗan tsawo da Mukhtar ba zai iya tantancewa ba sbd rubutun likitoci ba irin na normal mutane bane ya bata yace ta kai lab please.
"Sai zuwa yaushe duk results din zasu fita?"
Dr Ahmad yace
"zai iya kaiwa five hours kan a kamallah komai sbd suna dayawa"
Miƙewa Mukhtar yayi ya miƙa mishi hannu suka yi musabaha kan yace
"Zan dawo ko zuwa anjima, nd I will make the payments yanzu in na fita thank you very much"
Murmushi kwance a fuskan Dr. Ahmad shima ya bashi hannu kan ya juya ya fice, da kallo Dr. Ahmad ya bishi a fili ya furta
"Masha Allah, he's indeed a changed person"
Ko daga maganan shi ma ya fuskanci hakan.
Yana isa wurinta ya sakar mata murmushi tare da miƙa mata hannu ta kama ta miƙe yace
"Sorry madam na ajiye ki ko?"
Girgiza kai tayi tana murmushi, bata tambayeshi abin da yaje yi ba sai dae ta fahimci kaman akwai abinda yake damunshi, yanayinshi ya sake sanyi har suka isa gida babu wadda yayi magana, a tare suka shiga parlor Maami na musu maraba da dawowa, duk amsa mata suka yi suka mata sannu da gida kan kowa ya nufi É—akin shi don freshening, sai bayan la'asar ta fito ta zauna da Maami a parlor suna hira.
Chan shima ya shigo yayi joining É—in su Dukda ba wani magana yake ba, a kusa da Maami ya zauna ya É—aura kanshi akan shoulder É—inta, tsoro ne fal ranshi, hankalinshi rabi baya jikinshi rabuwa da Alayah shine fargabarshi a yanzu ba ciwo ba, Maami ta tambayeshi ko akwai wani damuwa ne yace babu, yana ji suna maganan Ummi akan yadda babu wani improvement saboda sun ce damuwa yayi mata over ta yadda jinin da ya tashi hitting yayi sama ba na wasa ba kuma laluranta ma na rashin ji da magana kaman musababbin BP É—inta ne.
Adu'ar samun lafiya duk suka mata, dab Magrib ya miƙe yace
"Maami zan É—an fita zan tsaya wani wuri ina ga daga chan zan wuce wurin baba kawai"
Suka mishi Adu'ar dawowa lafiya ya fita.
"Maami baki lura kaman yana cikin damuwa ba?"
Alayah ta faÉ—a tana kallon Maami
"Kwarai kuwa na kula, sai dae kila tunanin rayuwa ne with time zai sake in sha Allah"
Zaune a gaban Dr. Ahmad bayan sun gaisa yace
"ya ake ciki? Sun fito results din?
"Yeah sun fito, for now babu HIV but ka san test na HIV yana É—aukar 90 days ne kan ya zama successful, zaka dawo after 30days a sake yi haka after another 30 days again, sannan duk wasu STIs(Sexual transmitted infections) cututtuka da ake iya samunsu ta hanyar saduwa kaman su
Syphilis da gonorrhoea da sauransu duk babu"
Ajiyar zuciya ya sauƙe kan ya miƙa hannu ya ɗauki wani paper daban ya miƙa mai...
Tsawon mintuna talatin ya É—auka cikin office É—in kan ya fito, a cikin asibitin yayi isha kan ya isa wurin Baba suka yi karatu, Dukda baba ya lura kwazonshi ba kaman na jiya ba sai dae ya maida hankali sossai da sossai, daga nan ya tsaya ya saya masu gasashen kifi yayi gida.
****
Wasa wasa haka rayuwa ta zo ta sabar mishi da wani yanayi na daban, duk yadda yake karfafa zuciyarshi damuwarshi ba wani boyayye bane, yana iyakacin kokarin shi wurin bautar ubangijinshi kaman yadda yake matukar kula da Alayah da kuma Maami, bashi da wani buri illah ya shigo ya tarar dasu su biyu suna hira da raha hakan na kautar mishi da duk wani matsaltsalu na duniya, har ya sabar musu duk dare baya dawowa daga gidan baba hannu banza, ita kanta Alayah ta riga da ta saba bata cin komai sai ya dawo ya kawo ko balangu, tsire, kifi ko kaza gashi daban daban, yana riritata yana bata duk wani kulawa tsabar yadda hankalinta ke kwance Dukda yadda karatu yayi nisa wani irin kyau take narkawa tayi fresh abin ta.
Ta fannin mu'amalar aure bai taɓa nemanta ba wata huɗu ake nema kenan bata damu ba kasancewar ita wahalar abin kawai ta sani, ya kan rage zafi idan ta ciyoshi da gaske Dukda yana yawan shan tea me lemon tsami da gishiri, bata da wani matsala banda ciwon ummi da har yanzu babu wani cigaba, jiya e yau, duk ta tashi makaranta shi yake zuwa ya ɗaukota daga nan wucewa suke yi koyon tuƙi tun bata iyawa har ta soma kwarewa wani lokacin ma ita ke dawo dasu gida, in tace a watannin nan basu yi wani irin shakuwa na ban mamaki ba tayi ƙarya, yana bata duk wani kulawa da mace take fata ko buri, cikinta ya shiga wata na bakwai kenan duk zuwanta awo a tare suke zuwa, har yau babu wadda ya mishi maganan su koma gidansu ko ya ɗauke ta su tafi saboda daga Maami har Abba basa so su takura shi, kila ya fi so su zauna nan ɗin don duk wani shakuwa da be samu ba da Maami a yanzu ya same shi Dukda ya san ba kaman na umar da ita ba, amma kwarai zuwa yanzu sun shaku matuka.
Wani abu da yake yi yake ƙara burgesu shine yawan sadaka da taimako, har an san shi sai dae idan be ji taimako ba zai yi, abinci duk Litinin da juma'a yana ciyar da akallah mutane ɗari biyu zuwa uku, kuma lafiyayyen girki ba laga laga ba don a babban restuarant yake da contract, wani lokaci ma har ya ɗauketa su kai ziyara su orphanage, asibiti da sauransu a yanzu in ya ga rayuwarshi sai ya tsinci kanshi cikin zub da hawaye, lallai Allahnshi yana son shi.
***