← Book details Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 36

Sashe 23

Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan tsawon lokaci hira tsakanin en uwan na tashi Aisha ta dubi Maami tace
"Adda Bintu yanayin ki kaman kina cikin damuwa, Mukhtar ne?"
Girgiza kai tayi sai yanzu ma ta tuna da Mukhtar din tun jiya bata ganshi a nan ba, ta san ba zai taɓa chanzawa ba ai.
"Aisha wato dukda abubuwan Mukhtar na damuna sai dae abinda ke damuna a yanzu ya shallake wanchan, na rasa wani hanya zan bi wurin shirya tsakanin Umar da mahaifinsu da basa jituwa sam sam, Dukda ban taɓa ganin laifin umar ba duk na Abban nasu ne sai de abin na ci min rai sossai wallahi"

Ruqayya tace
"har yanzu ne rashin jituwar nasu? Na zata bayan doguwar nasiha da faÉ—an baba komai ya wuce?"
Maami tace
"kusan an samu sauƙin hakan amma daga sadda umar ya kama masa wani kaya ya kirashi ya cicci mishi mutunci shi kuma umar yayi rantsuwar har Abada idan har zai yi wani hulɗa da ya shafe lalata rayuwar al'umma ba zai taɓa bari ba, daga shi har Mukhtar ko inuwa basa haɗawa dashi saboda kowa da abinda ya fassara irin kariyarshi, yana nuna jarumta akan lamarin sai dae na lura abin na damun shi shiyasa sam baya son zaman ƙasar nan"

"Ya cigaba da haƙuri wata rana duk zasu fahimce shi in shaa Allah, yanzu ki duba irin taimakon da yayi a kan baiwar Allahn nan, kina tunanin ko Abbansu Mukhtar ya isa fidda matar chan daga gidan Hassan a yadda ya kafa tarko yake kuma da gogewa da duniya? In ba irin umar ba bana tunanin zata tsira cikin sauƙi haka"
Cewar ruqayya a hankali.

Aisha tace
"Allah ubangiji ya kyauta amma tabbas akwai wata rana da duk zasu yi nadamar hakan"

Lumshe idanu Alayah tayi ta sake maimaita sunan Umar a ranta, ya taimaketa ita kam bata da abin da zata saka mishi anan duniya sai dae da Adu'a, lallai zuciyarshi a wanke take ko bata ganshi ba tunda zai iya saka hannu ya É—auki umminta cikin najasa ya sakata a motar shi har ya kawo ta asibiti bayan ya fuskanci barazana daga Abban Jameelah.

A haka bacci ya sure ta, bata farka ba sai dab Magrib, a hankali take motsi ta É—an shaki numfashi tana jin kamshin turaren da taji rannan a sashen Maami me daaÉ—i, waigowa tayi don ganin me wannan kamshi sai suka haÉ—a idanu da Mukhtar, wani kakkauran miyau ta haÉ—iye cikin kokarin danne fargaba da tsoron da ya bijiro mata musamman idan ta tuna abinda ya mata kwanaki a asibitin chan da aka mata aiki.

Da idanu yake bin ta har ta miƙe zaune, muryanta ta ɗan gyara ta ce
"Ina yini?"
Albarkacin ya girme mata kuma É—a ga Maami.
Be amsa ba sai kallon da ya cigaba da bin ta dashi, chan ƙasa ta ja tsaki tana kokarin sauƙowa taji ya ce cikin buɗaɗɗiyar muryarshi
"Ke! Ni kika ja wa tsaki???"

*Kar ku sha'afa Al'ajabin So book 2 is not free, a kan naira 500 kachal zaki same shi immediately after an kamallah book 1, zaki iya yin payment ta nan
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai ki tura shaidar biya ta wannan layi
09039206763*

#Vote
#comment

                     🖤Gureenjoh🖤

AL'AJABIN SO
(heart touching story)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*

*BOOK 1*
*Page Sixteen*

*Na riga na yi alkawari in ba haka ba ina zan iya typing karfe 12🥲 sorry guys class nayi da ba zan iya dodging ba*

Bakinta ta tura gaba ba tare da tayi magana ba Dukda tsallen da ƙirjinta ke yi kaman ana dakan sakwara, sai dai abu ɗaya da ta lura dashi da ya bata lasisin hakan shine ba'a chake yake ba kuma idan hakan ne ta san zafin ran nashi da sauƙi, ba zata taɓa gigin yi mishi hakan ba idan yana buge don zai iya ƙas da ita a wurin ba tare ma da ya san ya aikata hakan ba, ƙarasa sauƙa tayi tare da sanya silifas ɗin ta
"Ke! Ina miki magana kin mai da ni banza?"
Nan ma bata ce komai ba taku biyu tayi ya sanya hannu ya fusgo ta tayi baya luuu ya mata masauki a kan kafafunshi hannunshi ya sa ya zagaye ta yana me kurawa fuskanta idanu for the First time a rayuwarsu irin kallon nan na kurilla yace chan ƙasa
"ba da ke nake ba Fatee?"
Ba tare da ta kalleshi ba ta zumɓura baki tace
"to ai ni sunana ba ke bane, ba gashi da ka kira sunan na amsa ka ba??"
Ta karashe tana ɗagowa ta kalli idanunshi da suke nan launin jaja kuma a lumshe, runtse su yayi yana jin yadda wani abu ke fusgar shi zuwa gareta, ji yake zuciyarsa na tsukewa wuri guda ga dukkan alamu ginin da babu shakka na so ne yake ginuwa daki daki cikin zuciyar shi, ɗauke kai yayi daga kallonta tare da ɗan tureta, ta kuwa sake taɓe baki alamun kai ka jiyo dama ba ni na ajiye kai na ba, toilet ta shige ko da ta fito ma bata same shi ba.

Da yammacin ranar aka bata sallama, gida suka dawo Dukda ta so tsayawa asibitin sbd ummin ta amma kuma ba hali don har yanzu tana ICU ne ba'a yarda ba ma da isa kanta bare a fara jinyar ta, likitoci da nurses ne kaÉ—ai ke zuwa kan ta, ko da suka koma gida ma bata bar zazzabin laulayi ba, kuma ta fahimci har lokacin babu shiri tsakanin Maami da Abba kai tsaye zata iya cewa sune sanadi, iya kokari Maami na yi wurin nuna mata komai lafiya ai dae bata san ta riga ta fahimta ba.

Kwance take kan kujera hannunta yalo ne take ci Dukda wani irin zazzabi da ya rufeta tana dukunkune sai rawan sanyi take kuma ta ƙi kashe Ac ko rage wa, Maami ta fita sai mama lami ne ke zuwa jin ko akwai wani abin da take buƙata ta kawo mata, bacci ne ya fara fusgar ta sam bata san Shigowar mutum ba ashe har ya kashe Acn bayan taɓa fuskanta da yayi ya ji jikinta raurau, baya baya yayi ya zauna kan kujera Red eyes ɗin shi ya zuba mata a ranshi yana ayyana dama haka mata suke fama ne ko ita ce kaɗai?

Tun da aka ce tana da cikin nan ba zai ce ga sadda ya risketa lafiya ƙalau cikin ƙarfi da kuzari ba, ko yaushe gata nan dai ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali yake jin duk wani rayuwarshi na baya ya fita kanshi fit, iya kokari yayi na daina shaye-shaye haka matan ma rabon shi da mace zai iya cewa ya manta, bashi da wani aiki sai na tunanin wannan yarinyar, wani sa'in ma yana son zuwa ɗin ya kalleta sai kuma wani sashe na zuciyarshi ya mishi nauyi, kunyar Maami ya lalaɓo ya rufe shi ruff ta yadda baya so ko haɗa idanu su yi.

Shisha Pen da smart ya bashi ya fitar yana ɗan jujjuyawa sun ce zai rage mishi wannan damuwan da ya shiga a kwanakin sai dai yana shakka don ya san zasu iya sa wani abu na bugarwa ciki, bakinshi ya kai kaman ya sha sai ya ja tsaki yana ƙoƙarin sauƙewa suka haɗa idanu, girgiza kai tayi tare da Miƙewa bata ce mishi ci kanka ba ta zo zata wuce yayi saurin riƙe hannunta kula da yayi kaman ranta ya ɓaci kuma hakan ya nuna har a fuskanta, fisgewa taso yi ta mance ma riƙon maza ba irin na mata bane...wani zafi ne ya ratsa ta mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin shanu a take ta fashe mishi da kuka sossai har sai da ya tsorata.

"Ni ka sakar min hannu..."
Da sauri ya miƙe yana kokarin duba hannun ko ta ji ciwo ne sam be san masu ciki da wannan mood swings ɗin ba ya haɗu kuma da wani tunani da tayi kanshi, ganin ya sake ta yasa ta nufi sama, taku biyu yayi ya tare ta
"Menene? Kin ji ciwo ne a hannun?"
"Ina ruwan ka da ni? Menene damuwarka? Ba tunani aka ce in yi akan auren mu ba? To na gama ba zan iya cigaba da zama da kai ba wallahi, tuban muzuru ne kayi ba na Allah da annabi ba..."
Shesheka ta ja tana matsawa baya ganin ya matso ta sossai yana kokarin taɓa ta don sam be fahimci inda matsalar ta taso ba tace
"kar ka taɓa ni, burin kowacce mace a rayuwa shine ta samu miji nagartacce, mai gaskiya da tausayi, wanda zata iya ƙarasa rayuwarta a tare dashi, sannan bayan aure su samu New wonderful family, burin kowace macece ta samu abokin rayuwa wadda zai agaza mata wurin cika duk burikan ta na rayuwa, ya taimaka mata a sadda take neman taimakonshi, ya so ta ya kasance mai kishin ta, sannan wadda zasu fuskanci duk wani matsalolin su a tare, ayi nishadi wasa da dariya, a yi salloli cikakku guda biyar a rana nd inspire one another to increase their deen, ayi respecting juna nd live peacefully in this nd the life hereafter, ka gayamin wanne kayi daga ciki? Ko kuma wanne kake shirin yi? Ya Mukhtar ɗan ka ne ke shirin zuwa duniya amma gaban idanunshi Shisha ne kake shirin sha wadda babu tantama na san flavor din ba zai rasa surkin abin bugarwa ba? Idan ba zaka ji kunyata ba ni karamar dangar ka da ka saba shawowa ka juye min shi be chanchanci kunyar ka ba? Maami bata chanchanci ka mata kawaici ba a cikin parlorn ta zaka yi shaye-shaye? Ka matsa min na wuce ka sha kayanka amma ka sani wallahi ni dae na gama zama da kai.."
Hawayenta ta share kan ta zagaye shi tayi sama da gudu tana kuka.
Chapter 23 · 0% Book details