Sashe 16
Al'ajabin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Fatima tun da nayi sallama da ƙasata na shigo wannan na san nayi sallama da farin cikin rayuwa, na fuskanci kalubale iri iri da damuwa kala daban daban kan Allah ya haɗa ni da mahaifinki ya maida ni tamkar sarauniya ya bani duk wani farin ciki da na rasa a baya amma shima Allah be bar min shi ba, tafiyar shi ga rabbissamawati ya sarar dani, na ɗauka nima zan bishi a kowani lokaci amma tunda na tsallake baƙar wahalar da na sha daga rasuwarshi zuwa haihuwar ki na sa a raina cewa komai ze zo ya zama tarihi, iko na rabbi ne kawai dawwamamme, na sa a raina zan raineki kila sirrin farin cikina na gareki, sai kuma gashi yadda kema Allah yayi dake.
Dukda haka ban sare ba, kema ina me karfafamiki gwiwa da kwantar miki da hankali a kan cewa in shaa Allahu zaki wayi gari kiga duk wannan sun wuce, imani da yaƙini akan ubangiji yana riskar da bayi zuwa ga magantuwar matsalolinsu, wallahil azeem ubangijinmu na sane da lamuranmu kuma ina da tabbacin wata rana ze fidda mu daga cikin wannan jarabawa, ko ban riski lokacin ba in shaa Allahu wata rana zaki yi farin ciki, zaki yi murna zaki tuna kuma da cewa na faɗa miki hakan"
Hawayenta ta share ta zurawa muktar ido, kila watarana shine ze zama farin cikinta, kila kuma karshen zaman su na iya zuwa ko kusa ko nesa, amma ka fin nan tayi alkawarin yunkuri wurin chanza shi, zata kasance me yi mishi Adu'a a ko wani motsinta zata taya mahaifiyarshi yakin mai dashi mutumin kirki da yardar Allah ko da kuwa ita baza ta samu ribar komai ba.
Anan kan sallayan tayi bacci da asuba ma jin mutum kawai tayi ya É—auke ta zuwa gado, bata mishi tirjiya ba ta hakura saide fuskanta be huta da ruwan hawaye ba don ba daaÉ—in abun take ji ba banda azabar ciwo, seda ta sake wanka na ruwan zafi sossai tayi na tsarki ta fito tayi sallah, yana kwance yana bacci, a hankali ta matsa kusa dashi ta sa hannu ta na É—an bubbuga kafafunshi
"ya Mukhtar! Ya muktar ka tashi kayi sallah don Allah, lokacin sallah na wucewa"
Ko motsi be yi ba, da ta matsa mishi ya ja dogon tsaki tare da kaiwa hannunta harbi da kafa da sauri ta ja baya ya samu iska, tagumi ta zuba tana kallonshi har bata san sadda bacci ya kwashe ta a wurin ba.
Sai misalin karfe goma ta tashi, yunwa ne ke dawainiya da ita kuma har lokacin bacci muktar ke yi, idanu ta zuba mishi tana aikin kallo, da zai shiryu muktar ba karamin kyau yake dashi ba, tana nan tana kallonshi tana sake-sake, ya buÉ—e idanu.
"Wani maitar ne kike yi da zaki tasani a gaba kina kallo haka?"
"Ba komai, ina jin yunwa ne"
"Ni zaki cinye kenan sai ki koshi?"
Da sauri ta girgiza kai, tsaki ya ja kan ya sauka seda ya tsaya wurin landline yayi call kan ya shige bayin, tana nan zaune har ya fito yayi wanka sede ya maida kayanshi ne don shima babu komai nashi anan É—in, tsayawa yayi da niyyar sallah kaman kar tace komai sbd tsoron shi sai kuma tace
"Ya Mukhtar namiji fa daga cibiyar shi zuwa guiwowinshine al'auranshi, Kaga zaka yi sallah kuma wandon be kai guiwa ba be kamata ba"
Ta faÉ—a a tsorace
"karki karɓa in nayi" ya faɗa yana jan tsaki tare da tada Sallar shi ita dae ta san sallahn nan kam se a hankali karfe sha ɗaya sallahn asuba sannan da gajeren wando.
Knocking aka yi ta miƙe ta buɗe, tray ne me ɗauke da abinci kala uku da ruwa da wani energy drink, karɓa tayi ta zo ta ajiye ta zauna jiranshi har ya idar ya juyo.
"ÆŠauki abin da zaki iya ci"
Ya faÉ—a ba tare da ya kalleta ba.
Shinkafa jollof ta ɗauka da ruwa, ya ja sauran, tana ci tana satan kallonshi ga mamakin ta ya cinye duka abincin trayn nan bata ma yi rabin nata ba, energy drink dinshi yake sha sai wayanshi ya fara ringing don yanzu ya kunnata, dubawa yayi ganin Maami yasa ya ƙi dagawa kiran duniya ta mishi ya ƙi ɗauka, chan kiran Alhajinsu ya shigo mishi kaman kar ya ɗauka ba sai ya ɗaga.
"Muktar ina ka kai Æ´ar mutane Maaminka ta kasa natsuwa? Kana so sai ka tayar mata da hawan jini ko?"
"Dad naga dae matata ce, me nata?"
"Ka amsa mini kuna ina? Taje gidan ku bakwa nan"
"Hotel"
Ya faÉ—a yana haÉ—e rai.
Ita dae tausayin Maami ne ya rufe ta ta san duk don ita ne hankalin Maamin yake a tashe, a hankali tace
"ya Mukhtar ka bani Maamin zan yi magana da ita don Allah"
Harara ya zabga mata kan yacewa mahaifinshi da ya gama ce mishi su dawo yanzu
"gaskiya ba zan dawo ta rabani da matata ba, ni ban rabata da mijinta ba haka kawai"
"Don Allah yaya Mukhtar"
Wayan ya jefa mata har yana dukan kirjinta ta dauka tana gaida Alhajin cikin girmamawa ya amsa yana tambayar lafiyanta tace da sauƙi Maamin na kusa?
muryar Maamin ta ji tana cewa
"Fatima? Kina lafiya kam?"
"Lafiya ta ƙalau Maami, eyaa Maami ki mana alfarma ki kwantar da hankalinki kinji don Allah, in sha Allah babu abunda zai faru"
Ta faÉ—a a karye cikin son karfafawa Maamin gwiwa, Maamin da taji hawaye na son zuba mata ne tace
"Fatima ki yafe mana mun kuntata miki rayuwa"
Girgiza kai tayi tana share hawayen da ya zuba mata
"ko É—aya Maami idan da ba don auren ba ai da ban sanki ba, amma yanzu na sameki bayan Ummina babu abin da ya kai hakan farin ciki a gare ni"
"Ki bashi wayan"
Maami ta faɗa, miƙa mishi ta yi.
Karɓa yayi yana kau da kai daga kallonta yana taɓe baki
"Ina kwana?"
"Baka damu da kwana na ba ai muktar da ka damu da ba haka ba, ka É—auki yarinyar nan ka maida ta gidanta ka bar Hotel da ita, sannan ka tabbatar ta cigaba da zuwa makarantar ta ranar Litinin"
Tana kai nan ta kashe wayan, hawayenta ta share Alhj dake tsaye yace
"menene kuma ne Maamin su? Ina dae yarinyar nan tace miki babu komai ki rabu da ita da mijinta mana"
Cikin takaici ta kalle shi tace
"Zurfin tunani da tarin tarbiyar da yarinyar nan take dashi she's too good for muktar wallahi"
Tana kai nan ta miƙe ta bar mishi ɗakin.
Su kuwa bayan ya ajiye wayan ya taɓe baki yace
"Maami matsala"
"Subhallah"
Ta ambata chan ƙasa, ba don tana tsoron yin magana ya zama laifi ba da tace yayi saurin tuba da wannan kalma da ya je fi mahaifiyarshi dashi in har yana son rabauta duniya da lahira iyaye ba abin wasa bane amma inaa.
"Ke! Tashi mu tafi"
Da sauri ta miƙe tabi bayanshi, a cikin harabar gidansu yayi parking, ajiyar zuciya me karfi ta sauke ko ba komai zata je ta samu tayi magana da Mahaifiyarta, bata jirashi ba tayi ciki zuwa ɗakinta ta ɗauko wayanta ta fara turawa ummi text message.
"Alaya ina kika shiga kwana biyu nayi sako shiru babu amsa? Kina lafiya dae ko? Ko ciwonki ne ya tashi? Ina ma ina da bakin kiranki in ji muryarki don tabbatar da lafiyanki... Don Allah kar ki min karya baki da lafiya ko?"
Kuka ta fashe dashi a fili tace
"Ummi bani da lafiya, ummi bana son wannan aure bana son shi, mugu ne, ummi marar tsoron Allah ne, bashi da ibada be san menene addininshi ba, ummi abubuwan da nake son faÉ—a miki kenan amma ba zan iya ba..."
Typing tayi
"na É—an yi rashin lafiya amma da sauki Maami ta kula da komai yadda ya kamata"
"Subhallah ya jikin? Allah ya sakawa Maami da alkhairi"
"Alhamdulillah ummi babu komai yanzu, Ameen thumma Ameen kefa ummi? Babu wani damuwa? Su Hajiya Zeenat basa takuraki? Aiki be miki yawa ba ummi?"
"Babu wani matsala Alayah, Allah ya baki lafiya"
Tattaunawa kaÉ—an suka kara taji an turo kofan, da sauri ta É—aga kai ta kalleshi..
"Ina da baƙi da dare ki shiga kitchen ki shirya musu abinci"
A hankali tace
"Toh"
Har ya juya ya ce
"Ki tabbatar mutane akallah ashirin zasu ci su koshi"
Yana kai nan ya fice, bata kawo komai ba bayan tayi la'asar ta shiga kitchen dinta Allah ya sa tana jin karfin jikin nata sossai Alhamdulillah, sossai ta zage tayi girkin har kala biyu jollof nd fried Rice pepper chicken sai ta ɗan yi snacks ta haɗa fruit drinks masu daaɗi, dab Magrib ta fito daga kitchen din wanka ta sake da alwala ta zo tayi sallah, ta jima tana karatun alqur'ani da rokar wa kanta mafita a wurin rabbisamawati har aka yi isha ta tashi ta gabatar kaman wasa tana zaune nan ta soma jin hayaniya a ranta take ayyana baƙin sun zo kenan.
Bata gama nazari ba ya shigo
"Tashi ki shirya jarrey baƙi na na jira a yi serving ɗin su"
A hankali tace
"Amma Ya muktar abincin ai yana dining naga be kamata sai na fita na sassa......"
"Kina so in wanka miki mari?"
Shiru tayi ta miƙe shine ya shiga drawer ɗinta ya duba ya zaɓo wani pencil gown ya wulla mata, seda ta gama kallon kayan kan ta saka a hankali babu shape na jikinta da be nuna ba.
Hijab ta fara dubawa yayinda shi kuma yake sake da baki yana kallonta don ba karamin gigita shi tayi ba sai gani yayi ta saka hijab
"ke ina zaki je da wannan abin?"
"Wurin baƙin naka ba?"
Tsaki me karfi ya ja yarinyar nan an yi bagidajiya
"ke kin san me sunana kuwa? PIYA-PIYA nake maganin kwari shine matata zata fita cikin abokaina da wannan abun a samu abun nuna ni? Kin cire ko kuwa?"
Ya daka mata tsawa daga karshe